News:

Ramadan Mubarak!

I pray that we get the full blessings of Ramadan and may Allah (SWT) grant us more blessings in the year to come.
Amin Summa Amin.

Ramadan Kareem,

Main Menu

Tatsuniya Online (GIZO DA GOGI)

Started by IBB, March 27, 2003, 10:28:08 AM

Previous topic - Next topic

0 Members and 19 Guests are viewing this topic.

IBB

;)keep it up Ihsan.

Ummi karki hada fada bada shi nake ba

here no be beef
IHS

IBB

cont from Gizo da shan yaji

BAYAN GIZO YA GAMA SHAN YAJI, SAI 'AKA KAISHI WAJEN

SARKI. KOKI MATAR GIZO TANA TA MURNA. SARKI YA

KALLI  :o GIZO YANA TAKAICI SABODA YACI GASAR KUMA

RABIN GARIN YA ZAMA NA SHI (GIZO). SAI SARKI YA

TAMBAYI DOGARI KO GIZO YAYI SHEII LOKACIN DA YAKE

SHAN YAJIN, DOGARI YACE 'A'A. SHI KENAN SARKI YABAWA

GIZO RABIN GARI. BASHI KE DA WUYA SAI GA KURCIYA TAZO

TACE AI GIZO YAYI SHEII LOKACIN SHAN YAJI. TA FADI

WAYON DA GIZO YAYI, YANA TAMBAYAR DOGARI KO YACE

SHEII. SHIKE NAN SARKI YA KARBE GARIN SHI YA KASHE

GIZO.  ???

KURUNKUS KAN DAN BERA
IHS

IBB

BA DAN KARYA, KARYA CE, IN FADA RIJIYAR ZUMA A CIRO NI DA GUGAR NAKIYA DA ALKAKI

IN TUNTUBE DA TUWON SHINKAFA IN DAUJE BAKI DA TSOKAR NAMA ;D
IHS

Ihsan

Allah ya kara dawo dani filin tatsuniya...:) Tatsuniyar mu a yau ita ce...

GIZO YAYI AMARYA

Gata nan gata nan ku...

Gizo ne dai suna zaman lafiyar su shi da koki garin kalle kallen shi (irin na wasu...ban fadi suna ba!) ya gano 'yar gidan tururuwai (ants).

Gizo da debowa ya kai yace ay shi yana sonta zai kuma aureta!!!... su Gizo har da sakin koki!

Aka daura auren gizo and the ant aka sha biki aka gama aka kai amarya gidan gizo. Da farko kamar abun arziki ana zaman lafiya komai gizo yake so ana yi mashi.

After few month sai tsiya ta fara...tururuwa ta daina yiwa gizo abunda yake so! Ana haka sai rannan gizo ya hadu da koki a hanya

koki: ashe gizo an yame (rame), ashe gizo an yame?

Gizo: in bayi (bari) dai koki! nayi karambani da na auyo (auro) 'yar gidan tururuwai. Baki na ta maujeje (big), baki na ta kwalele (big), cikin ta kamar kwarya, kafar (leg) ta kamar tsinke (stick).

Koki tace ato that's ur own wahala... coz ita (koki) tayi kyau ( ::)) babu abunda ya dameta. Shi kuwa gizo wahala ta ramar dashi.

Nan dai gizo ya tsaya wai shi dai gaskiya koki ta dawo...he's tried of the ant! Koki sai da ta wahalar dashi sannan ta dawo! ita kuma 'yar tururuwa ya sake ta.

Gizo da koki suka koma kamar da tare da 'ya 'yansu. Gizo yayi kyau (ewww)...

Kurunkus kan dan bera da ba dan gizo ba dana yi karya...

greetings from Ihsaneey

al_hamza

where do you come up with these stories from.
man this gizo na shan wahala a tatsuniyoyin hausa  ;D
ABILUNAH? SABILUNAH? AL-JIHAD! AL-JIHAD!

Ihsan

lol Ali...wallahi I all remember it from my childhood...:) insha Allah sai kuma gobe za'a kara saka wata...
greetings from Ihsaneey

IBB

IHS

IBB

KATA NAN KATAN KU

GIZO DA BASAMUDE


AKWAI WANI BASAMUDE A BIRNIN KUDUS. BASHI DA KOWA

SAI KATON SAN SA (HIS BULL) WANDA YAKE SAWA A GASAR

TABA KANSHI. SABODA YANA DA SAWO BABU WANDA ZAI IYA

TABA KANSA (HEAD) IDAN MUTUN  BAI TABA BA SAI YA CINYE

SHI. HAKA YAKE YI DUK SHEKARA WANNAN SHEKARAR SAI GA

SHI A GARIN SU GIZO YA NEMI WANDA ZAI TABA KANSHI YA

BASHI SA (BULL) DUK GARIN KOWA YAKI. GIZO NA JIN LABARI

SAI YAZO YACE AI SHI ZAIYI SHIKE NAN BASAMUDE YACE TO

AKA SA RANAR GASA, DA RANAR TAZO GIZO SAI YAKI

FITOWA DAGA DAKIN SHI, BASAMUDE YAZO BAKIN KOFA

YACE GIZO YA FITO GIZO YACE YANA ZUWA BASAMUDE YAI

TA JIRA DA YA GAJI YA KARA CEWA GIZO YA FITO SAI GIZO

YA CE YANA AIKI NE YA KUSA GAMAWA BASAMUDE YACE

WANI IRIN AIKI NE WANNAN SAI GIZO YACE AI YANA DINKE

BANGO BASAMUDE YACE DINKE BANGO? GIZO YACE E SAI

GIZO YACE MASA YA LEKO DAKIN YA GANI YADDA AKE DINKE

BANGO BASAMUDE CIKIN MAMAKI YA LEKA YANA ZURA

KANSHI CIKIN DAKI SAI GIZO YA TABA. GIZO YA FARA TSALLE

NA CABA (TABA) NA CABA JAMA'A SUKA SHEDA AI GIZO YA

TABA SHIKENAN GIZO YACI KATON SA

KURUNKUS KAN DAN BERE
IHS

Rose

Another bunch Ihsan :)
Sannunki da aikin rubutu.

Kai su mallam gizo anzo duniya da kafar baya :D
aNo Ta DaBo ChiGaRii, GaRi Ba KaNo Ba DaJin ALLaH.

IBB

DARE DUBU DA DAYA
IF U WANT ME TO READ THIS BOOK 4 U HERE POST UR REPLY AS 'YES' NUMBER OF RESPONDS DETERMINE.............
IHS

Ihsan

Tatsuniya shiru kwana biyu  :) karatu yayi yawa shi yasa... but insha Allah idan na samu lokaci zan zagayo na rubuta ko daya ce....till then...take care all buh-buy
greetings from Ihsaneey

gogannaka

ga tanan ga tananku
gizo ne dai ya yiwo ciyawa ya kasa dauka sai ya dado wata ;D ;D ;D
Surely after suffering comes enjoyment

baby_gal_84

wai sannu ihsan da kukari but plz tell us more ........gaskiya i miss childwood ayya my nanny i called her inna shes always the person tellin me tstsuniya and she died just a month ago ....ayya i miss her coz she never belive im old now shes alway pitin me like a baby tellin me stories and so on........ ihsan plz keep them comin me i cant remember all them in full ihsan do yu know the tstsuniya of i think yara ne da yawa daya tayi sata sai aka kaisu wajen wani kogi to find out or so i cant remeber all........plz if yu do tell us.
ond of love fills the life with sweet promises.

baby_gal_84

wai sannu ihsan da kukari but plz tell us more ........gaskiya i miss childwood ayya my nanny i called her inna shes always the person tellin me tstsuniya and she died just a month ago ....ayya i miss her  :'( :'(coz she never belive im old now shes alway pitin me like a baby tellin me stories and so on........ ihsan plz keep them comin me i cant remember all them in full ihsan do yu know the tstsuniya of i think yara ne da yawa daya tayi sata sai aka kaisu wajen wani kogi to find out or so i cant remeber all........plz if yu do tell us.
ond of love fills the life with sweet promises.

MaAMaa_LagOS

Ga wani tsohon labari amma na manta da sunan sa..........


Gata nan gata nanku..............
Wata rana wani miciji ya shiga fada ya sari dan sarki bai sani ba ashe fadawa suna ganin shi. Suka bishi yayi ta gudu yayi ta gudu yana haki har ya kai wurin wani Bawan Allah ya gaya masa abin da ya faru. Bawa Allahnan sai ya tausaya masa ya ce "kasan mai zai faru?" ya ce "a'a". "Zan bude bakina ka shiga ciki na ka buya idan sun tafi sai ka fito". Maciji ya ce na gode ya shiga cikin bawan Allah. Fadawa su ka nemi maciji suka rasa. Bayan fadawa sun gaji sun koma fada, sai mutumin nan ya ce da maciji ya fito. Maciji yace ba zai fito ba wai shi ya samu wurin zama. Mutumin nan yayi yayi da macijinan ya fito ya ki.
   Ana nan anan mutumin nan ya rame sosai. Wata rana Allah ya hada shi da wani tsuntsu ya gaya ma tsuntsun abin da ya ke damun sa. Tsun tsun yayi dogon tunani ya ce ya san yadda za'a yi. Idan rana ta fito mutumin nan ya kwanta a rigingine a kan titi, idan macijin ya ji zafi zai fito shi kuma sai ya cin ye shi. Haka kuwa akayii maciji na leko kansa tsuntsun ya hadiye shi.                                                                
    Sai tsuntsun ya ci gaba da ba mutumin nan shawara ya ce "yadda ka rame haka ya kamata ka sami kaji biyu ka ba matar ka ta dafa ma ko ka ji karfi"
Mutumin nan sai yayi wuf ya kama tsuntsun nan ya ce "saura daya".
    Ya tafi da tsuntsun nan ya sa shi a keji ...........to be continued.
aSY DoES iT