Mu Kyautata Rubutunmu

Started by jaybee, January 10, 2007, 02:22:42 PM

Previous topic - Next topic

0 Members and 1 Guest are viewing this topic.

Wai yaushe za mu kyautata rubutunmu na Hausa?

Mu Kyautata Ru...
0 (0%)
Mu Kyautata Ru...
0 (0%)

Total Members Voted: 0

jaybee

Assalam Alikum 'Yan uwa. Bayan gaisuwa mai yawa da fatan an yi sallah lafiya, kuma ina fatan an shiga sabuwar shekara lafiya.
Ina so in yi amfani da wannan dama domin in yi kira ga marubuta litttattafan soyayya na zamani mai suna ( Adabin kasuwar Kano/ Kano Market Literature) da su daure su rika karanata littattafansu sosai kafin a kai ga bugawa, wato (proof reading). domin akasari idan kana karatu za ka rika karo da kurakurai da dama, wani lokacin za ka ga an hada kalmar da ya kamata a raba ko kuma a raba kalmar da ya kamata a hada, da dai makamantansu.
Marubuta don Allah a kula, mu kara kyautata rubuntunmu na Hausa.
Daga Jibril Shu'aibu Adamu

gogannaka

Wannan gaskiya ne.Ina ganin abin da ya sa haka ke faruwa shine gaggawa da su marubutan suke domin su ga cewa sun buga littafai da yawa a tsakanin lokaci kadan.Wannan kuma kan rage ingancin rubutun nasu.
Madallah da wannan shawara taka jaybee.
Surely after suffering comes enjoyment