KanoOnline.com Forum

General => General Board => Topic started by: admin on October 25, 2007, 10:48:29 AM

Title: Ta'aziya -- Prof. Abdalla Uba Adamu Has Lost His Mother
Post by: admin on October 25, 2007, 10:48:29 AM
Assalamu alaikum,

I am sorry to announce to all Kano Online members, the death of the mother of Prof. Abdalla Uba Adamu, one of the cofounders of Kano Online. She passed away on Wednesday 24th October, 2007 in Kano, Nigeria.

Allah Ya jikanta. Ya kuma rahamsheta. Amin summa Amin.
Title: Re: Ta'aziya -- Prof. Abdalla Uba Adamu Has Lost His Mother
Post by: zezezee on October 25, 2007, 11:35:36 AM
Allah Ya jikanta, Ya gafarta mata. Mu kuma, Allah Ya kyauta namu zuwan, ameen ameen.

Title: Re: Ta'aziya -- Prof. Abdalla Uba Adamu Has Lost His Mother
Post by: dfynest on October 25, 2007, 11:40:16 AM
I heard the news over the radio this morning. My heart felt condolence to the Prof. and the entire members of his family. May her gentle soul rest in perfect peace, Ameen.
Title: Re: Ta'aziya -- Prof. Abdalla Uba Adamu Has Lost His Mother
Post by: MUNTAKA on October 25, 2007, 11:53:58 AM
may allah forgive her, grant her the eternal rest and let her gentle soul rest in perfect peace. may He also give the family the fortitude to bear the great loss.
Title: Re: Ta'aziya -- Prof. Abdalla Uba Adamu Has Lost His Mother
Post by: Dan-Borno on October 25, 2007, 11:56:51 AM
Inna Lillahi Wa Inna Ilaihir Rajiuna

Bismillahir Rahmanir Raheem
Kullu nafsin za ikatul mauta

Allah ya gafarta mata da RahamarSa
Yan'uwa da suka rigamu gidan gaskiya kuma,
suma Allah ya gafarta musu
Sa'annan mu da muke da rai, Allah yasa mu
cika da imani

Prof. sai hakuri da addu'a
Title: Re: Ta'aziya -- Prof. Abdalla Uba Adamu Has Lost His Mother
Post by: gogannaka on October 25, 2007, 12:35:00 PM
Allah ya Jikanta ya gafarta mata.Allah ya albarkachi zuriyar ta.
Haka dukkan musulman da suka mutu Allah ya  yi musu rahama daga rahamar shi wadda bata misaltuwa.
Mu kuma Allah ya bamu kyakkyawan karshe.
Title: Re: Ta'aziya -- Prof. Abdalla Uba Adamu Has Lost His Mother
Post by: Muhsin on October 25, 2007, 12:44:13 PM
Salam,
Inna Lillahi Wa Inna Ilaihir Raji'uuna

Allah subhanahu wa ta'aala ya jikan ta ya kuma gafarta mata dukkanin zunubanta ya albarkaci bayanta ya kuma basu hakurin jure rashinta.

Though I don't know where the sitting of condelence is taking place yet I'll find that out and soon and be there in person by Allah's grace.

Prof. Abdallah, Allah ya kara hakurin rashi. Muma, in tamu ta zo, Allah ya sa mu cika da imani.
Title: Re: Ta'aziya -- Prof. Abdalla Uba Adamu Has Lost His Mother
Post by: admin on October 25, 2007, 02:21:06 PM
Quote from: Muhsin on October 25, 2007, 12:44:13 PM
Though I don't know where the sitting of condelence is taking place yet I'll find that out and soon and be there in person by Allah's grace.
Muhsin, It is in Daneji Quaters in Kano city... Go on Sabon-Titi to Mandawari and make a turn towards Marmara, You should see the place on the right hand side.

Thanks.
Title: Re: Ta'aziya -- Prof. Abdalla Uba Adamu Has Lost His Mother
Post by: Bajoga on October 25, 2007, 02:33:15 PM
Quote from: Dan-Borno on October 25, 2007, 11:56:51 AM
Inna Lillahi Wa Inna Ilaihir Rajiuna

Bismillahir Rahmanir Raheem
Kullu nafsin za ikatul mauta

Lallai wannan "aya" gaskiya ce, kuma ba abinda zamu iya fadi sai dai kawai fatan Allah madaukakin sarki ya gafarta mata, Allah kuma ya ba dukkan families dinsu hakurin juriya da wannan rashin.

Mu kuma da muke da rai, sai muyi fatan Allah yasa idan tamu tazu mu cika da imani, haka zalika, magabata wadanda suka rigamu gidan gaskiya, suma Allah ya gafarta musu.

Prof. Allah ya bada hakuri, ameen.
Title: Re: Ta'aziya -- Prof. Abdalla Uba Adamu Has Lost His Mother
Post by: Mufi on October 25, 2007, 03:16:01 PM
Allah Ubangiji ya jikanta da Rahamarsa, Yasa Aljanna Firdausi makomanta. Iyali data bari Allah ya basu juriyan wannan rashin. Mu kuma idan tamu tazo Allah ya bamu sa'an cikawa da imani, Amin.
Title: Re: Ta'aziya -- Prof. Abdalla Uba Adamu Has Lost His Mother
Post by: Nuruddeen on October 25, 2007, 03:49:10 PM
Allah ya ji kanta da rahama. Ya kuma ba 'yan uwanta hakurin jurewa. May Allah give Prof Abdallah fortitude to bear this irreparable loss. Alla ya bada hakuri. Ma'asslam.
Title: Re: Ta'aziya -- Prof. Abdalla Uba Adamu Has Lost His Mother
Post by: sadiq on October 25, 2007, 04:31:17 PM
Allah ya ji kanta, yayi mata rahama, ya kuma sa ta huta. Ameen. May Allah(SWA) give our Prof the fortitude to bear the loss. idan kuma namu yazo, Allah ya sa mu cika da kyau da kuma Imani, Ameen.
Title: Re: Ta'aziya -- Prof. Abdalla Uba Adamu Has Lost His Mother
Post by: amira on October 25, 2007, 04:37:21 PM
Allah ubangiji ya jikanta yasa ta huta. Allah ya ba yanuwa da abokan arziki hakuri
na rashi, mukuma Allah yasa mucika da imani Ameen.
Title: Re: Ta'aziya -- Prof. Abdalla Uba Adamu Has Lost His Mother
Post by: Lawwali on October 25, 2007, 05:02:30 PM
Hakika Ta rayu rayuwa ta gari. tunda ta kawo mutum kamar Prof. Abdallah Duniya Kuma ta bashi Tarbiyyar da yake da ita a halin yanzu. wannan itace babbar gudummawar da Mace za ta bawa al'umar da take ciki. Godiyarmu Gareta Shine muce ALLAH ya jikanta ya sa Ta huta. Ameen
Title: Re: Ta'aziya -- Prof. Abdalla Uba Adamu Has Lost His Mother
Post by: MySeLf on October 25, 2007, 05:12:07 PM
GAFUR RAHIM ALLAH YA GAFARTA MATA, YASA MUTUWA HUTUCE.....
YA KUMA JIKAN IYAYENMU DA SAURAN MUSULMI.
Title: Re: Ta'aziya -- Prof. Abdalla Uba Adamu Has Lost His Mother
Post by: jewel(abdulgee22) on October 25, 2007, 09:59:24 PM
Allah ya jikanta, kuma Allah ya gafarta mata........amin. Zuriyar ta, Allah ya basu hakuri juriya da kuma jimata addua. amin
Title: Re: Ta'aziya -- Prof. Abdalla Uba Adamu Has Lost His Mother
Post by: mustidoc on October 26, 2007, 01:01:21 AM

Innah Lillah Wa Innah Ilaihi Rajiun. Allah Ya ji Kan ta, Ya rahamshe ta, Ya yafe mata, Ya kuma sa ta a Aljannah Fiddausi, Ameen summa Ameen. Allah kuma Ya ji kan iyayuen mu da ka kannin mu baki daya, ameen. In tamu ta zo, Allah Ya sa mu chika da Imani, Ameen.
Title: Re: Ta'aziya -- Prof. Abdalla Uba Adamu Has Lost His Mother
Post by: bakangizo on October 26, 2007, 09:09:16 AM
Allah ya jikanta da JinkanShi, ya gafarta mata da GafararSa kuma ya rahamsheta da RahamarSa, amin.
Title: Re: Ta'aziya -- Prof. Abdalla Uba Adamu Has Lost His Mother
Post by: Bee on October 26, 2007, 09:35:34 AM
Allah ya ji kan ta Ya kuma sa ta huta.
Title: Re: Ta'aziya -- Prof. Abdalla Uba Adamu Has Lost His Mother
Post by: Muhsin on October 26, 2007, 10:29:59 AM
Quote from: admin on October 25, 2007, 02:21:06 PM
Quote from: Muhsin on October 25, 2007, 12:44:13 PM
Though I don't know where the sitting of condelence is taking place yet I'll find that out and soon and be there in person by Allah's grace.
Muhsin, It is in Daneji Quaters in Kano city... Go on Sabon-Titi to Mandawari and make a turn towards Marmara, You should see the place on the right hand side.

Thanks.
Am today, after school hours, going to be there by Allah's grace.
Thanks.
Title: Re: Ta'aziya -- Prof. Abdalla Uba Adamu Has Lost His Mother
Post by: *~MuDa~* on October 26, 2007, 12:30:44 PM
Loosing a mother is like loosing one sense of being, i only oray that you will be strong enough to carry on, it pains me so deeply to have learnt this, but all the same, Allah knows best and we are suppose to be grateful for his actions, may Allah grant her Aljanna Firddaus, it will be alright insha Allah. Allah ya gafarta mana duka. Amin!
Title: Re: Ta'aziya -- Prof. Abdalla Uba Adamu Has Lost His Mother
Post by: dan kauye on October 26, 2007, 05:04:59 PM
Allah ya ji kanta,ya kuma rahamta mata..

Those last couple of weeks have been really crazy.A good friend of mine lost his mum,and week later his 19 year old sister,both to diabetes.Allah ya ji kansu..
Title: Re: Ta'aziya -- Prof. Abdalla Uba Adamu Has Lost His Mother
Post by: HUSNAA on October 26, 2007, 06:46:21 PM
Inna Lillahi wa Inna Ilaihi rajiun.
Allah Ya jikan ta da RahamarSa. Ya sa karshen wahalar kenan. Allah Ya Kyautata karshen duk musulmin da ya rasu da kuma wa'yanda za su biyo baya ameen.
Professor Allah Ya baka da iyalinka hakurin jure wannan babban rashi, ameen.
Title: Re: Ta'aziya -- Prof. Abdalla Uba Adamu Has Lost His Mother
Post by: Ibro2g on October 26, 2007, 11:28:54 PM
Innalilahi wan inna Ilayhir Raji'un

May Allah forgive her, save her a place in Firdaus. May he bless what she has done and all she has left behind. May Allah ease her mourners in his mercy, give them the heart to take the loss and the courage to continue our lives struggles. May Allah bless the muslim, guide us to the right path, forgive us our wrongdoings and grant us paradise. Ameen.

please recite Suratul Ahad 3 times for her and all the believers gone before us
Title: Re: Ta'aziya -- Prof. Abdalla Uba Adamu Has Lost His Mother
Post by: Bayya on October 27, 2007, 07:21:53 AM
Allah ya ji kanta ya gafarta mata.
Allah yasa ta huta, muku Allah
ya kyauta na mu zuwan, amin.
Title: Re: Ta'aziya -- Prof. Abdalla Uba Adamu Has Lost His Mother
Post by: yakasai on October 28, 2007, 12:19:37 PM
ALLAHU TA'ALA YA JIKANTA, YAYI MATA RAHAMA, YA KUMA KYAUTA NAMU ZUWAN, Amin summa Amin.
Title: Re: Ta'aziya -- Prof. Abdalla Uba Adamu Has Lost His Mother
Post by: mnzubair26 on October 29, 2007, 10:20:19 AM
Allahu Akbar, Allah ya jikan ta, Allah ya rahamshe ta, Allah yasa aljannah Firdausi makomar ta. Allah ya basu hakurin jure rashin ta. Mu kuma idan tamu tazo Allah yasa mu cika da imani. Ameeeeen S. Ameeeeeeeeeeen

M. N. Zubairu
Quote from: admin on October 25, 2007, 10:48:29 AM
Assalamu alaikum,

I am sorry to announce to all Kano Online members, the death of the mother of Prof. Abdalla Uba Adamu, one of the cofounders of Kano Online. She passed away on Wednesday 24th October, 2007 in Kano, Nigeria.

Allah Ya jikanta. Ya kuma rahamsheta. Amin summa Amin.

Title: Re: Ta'aziya -- Prof. Abdalla Uba Adamu Has Lost His Mother
Post by: salizone on October 30, 2007, 07:48:35 PM
Ina yiwa dukkan 'yan uwa ta'aziyya, Allah kuma ya bamu hakurin rashin wannan baiwar Allah, ita kuma Allah Ya gafarta mata ya kyautata bayanta.
Title: Re: Ta'aziya -- Prof. Abdalla Uba Adamu Has Lost His Mother
Post by: SAAHIB 92 on October 31, 2007, 11:44:29 AM
Allah ya kyautata kwanciyarta,kuma ya sata cikin cetattu.
Title: Re: Ta'aziya -- Prof. Abdalla Uba Adamu Has Lost His Mother
Post by: Diso on November 01, 2007, 11:34:05 AM
Inna Lillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un!

Allah ya jikan mai rasuwar wannan uwa tamu.
Allah ya gafarta mata ya yafe dukkan laifukanta.
Allah ya sanya aljannar Firdausi ce makomarta.
Allah ya amfana zuri'ar da ta bari bayanta.
Allah ya baiwa iyalanta hakurin rashinta.
Allah ya kyautata tamu bayan tata.
Title: Re: Ta'aziya -- Prof. Abdalla Uba Adamu Has Lost His Mother
Post by: _Waziri_ on November 01, 2007, 03:25:21 PM
Quote from: mustidoc on October 26, 2007, 01:01:21 AM

Innah Lillah Wa Innah Ilaihi Rajiun. Allah Ya ji Kan ta, Ya rahamshe ta, Ya yafe mata, Ya kuma sa ta a Aljannah Fiddausi, Ameen summa Ameen. Allah kuma Ya ji kan iyayuen mu da ka kannin mu baki daya, ameen. In tamu ta zo, Allah Ya sa mu chika da Imani, Ameen.

Amin Amin. Have been a way for too long it seems. Prof. my heart felt!

But am sure she is in God beneficence by now. If for anything, our culture, civilisation and faith has been blessed thru her in your person. You may not have an idea of how you shaped and still continue to shape minds in the mould of the truth towards appreciating God and his bouties in the 21st century using the Islamic, Hausa, West African spectacle. It gives us alot of pride as we remember to pray for her always as one blessed soul that outletted the adoring souvenir in you.

Allah Yayi mata rahama Yasa mu iya 'counting achievements' dinmu yadda tayi yanzu, 'at the point of our death too'.   
Title: Re: Ta'aziya -- Prof. Abdalla Uba Adamu Has Lost His Mother
Post by: manasmusa on November 01, 2007, 03:46:16 PM
KULLU NAFSIN ZAIKATIL MAUTI. Tabbas, dukkan mai rai sai ya dandani mutuwa. Allah ya jikanta ya gafarta mata, ya kuma sa aljanna ce makomarta Allah ya bada jimirin jure rashinta. mu kuma in tamu ta zo Allah ya sa mu cika da imani mu tashi da shi. ameeen.
Title: Re: Ta'aziya -- Prof. Abdalla Uba Adamu Has Lost His Mother
Post by: Abdalla on November 02, 2007, 07:20:17 AM
Lunar Horribilis - Godiya
Jama'a, Assalamu Alaykum,

A madadin iyali na da kuma ni kai na, ina mika dimbin godiya ga daukakin majalisa saboda sakonnin ta'aziyyar rasuwar mahaifiyar mu, Hajiya Rabia't Muhammad Lawan da aka dinga aiko mana ta majalisa, ta tarho, ta imail da kuma da yawa wadanda suka dinga zuwa har gida tare da iyalansu, da kuma wadanda suka dinga zuwa ofis.

An haifi Malama Rabi'at, kamar yadda aka fi saninta, a garin Gwarzo, Kano, a shekarar 1942. Ta rasu ranar Laraba, 24 ga Oktoba 2007 da misalin 10.00 na dare a sakamakon arangamar ciwon asma da ke fama da shi da ya taso mata gadan-gadan lokaci guda.

Duk da cewa ba ta taba fitowa a wani dandalin da nake fitowa ba a wajen nazarce-nazarce na, amma ta yi wani babban fice a inda ba a zata. Masu karatu watakila za su tuna da wani ayarin haruffan Hausa ma su lankwashe-lakwashe  wanda a ke kira Rabiat (rabiat.ttf). To sunanta na sakawa wannan ayarin haruffan lokacin da na kirkiro gundarin haruffan rabiat.ttf ranar 2 ga Yuli, 1995. Na saka sunanta ne domin gode mata da irin gudunmowar da ta bayar wajen ilimintar da ni; saboda haka na sakata a cikin tunanin jama'a ko bayan ranta – sai kuwa ga shi duk da ta rasu, amma kusan dimbin jama'a da dama na tunawa da ita a duk lokacin da aka yi rubutun Hausa da ayarin haruffan Rabiat.

Mun gode mun gode mun gode bisa ta'aziyyar da aka dinga kawo mana har tsahon kwana bakwai-- kuma majalisa a wakilce ta ke sosai domin da yawa 'yan majlaisa suna tare da mu, tun da ga jana'izar har bayan share makoki. Wannan ya dada tabbatar min da muhimmancin wannan mattattar alheri domin zuwan su da kuma zaman su (wadansu ma har da iyalansu) ya taimaka kwarai wajen daurewa da wannan rashin da muka yi.

Mun gode da goyon baya, da kuma addu'o'in da a ka yi mana. Allah Ya karba. Allah Ya ba da lada. Allah Ya bar zumunci. Allah Ya jikan dukkanin Musulmai. Lallai rai dadi ne da shi; kuma rasuwa zafi ne da ita. Allah Ya sai mu cika da imani.

Abdalla, a madadin dukkanin iyalan Muhammad Uba Adamu Kantoma, Mazaunin Kano, Najeriya.

Title: Re: Ta'aziya -- Prof. Abdalla Uba Adamu Has Lost His Mother
Post by: bb1and2 on November 06, 2007, 12:49:34 AM
Allahu akbar!!! muna fatan Allah ya jikanta ya rahama mata kuma Allah yasa Aljanna makoma ita da dukkan musulmin da suka rigamu. Mu kuma Allah yasa mu chika da Imani idan tamu  ta zo. Ina kuma mika ta'aziyya ta ga kaninsa Ado Uba Adamu.
Title: Re: Ta'aziya -- Prof. Abdalla Uba Adamu Has Lost His Mother
Post by: ajingi on November 07, 2007, 08:28:31 AM
Inna Lillahi wa inna Ilaihirajiun! May her soul rest in peace and ours to come in the glamors of faith.

Allah (SWT) ya jikanta da rahamah, Ameen!!
Title: Re: Ta'aziya -- Prof. Abdalla Uba Adamu Has Lost His Mother
Post by: IBB on November 15, 2007, 10:30:17 AM
Inna lillahi wa inna illaihir rajiun. Allah yaji  kanta yasa ta huta Ameen Allah bata gidan Aljannatul Firdausi. Allah ya ji kan musulmai kaba daya ya kyautata namu zuwan Ameen