Assalamu alaikum yan-uwa da abokan Arziki na kano online,da wani dan karamin tunanine nayi naga kamar ya kamata mu dan wasa kwakwalwa,mu dan gwada kacici-kacici (hausa/english riddles)
Ga wasu nan dai kan na samo wasu,wanda ya sanni ya ba da ansa. in kana/kina da wani ku rubuto
- shanu na dubu amma madaurinsu daya.
-baba na daka, gemu na waje
-takanda ba kashi ba
-baba ya zaga iya ta zaga basu hadu ba
-yadda dillin yakanyi dillin haka ma dillin ya kanyi dillin
- tsimagiyar kan hanya make yaro make babba
Wanda ya san ansa ya bayar in kuma kun bada gari na fada maku ansar
QuoteAssalamu alaikum yan-uwa da abokan Arziki na kano online,da wani dan karamin tunanine nayi naga kamar ya kamata mu dan ?wasa kwakwalwa,mu dan gwada kacici-kacici (hausa/english riddles)
Ga wasu nan dai ?kan na samo wasu,wanda ya sanni ya ba da ansa. in kana/kina da wani ku rubuto
- shanu na dubu amma madaurinsu daya.
-baba na daka, gemu na waje
-takanda ba kashi ba
-baba ya zaga iya ta zaga basu hadu ba
-yadda dillin yakanyi dillin haka ma dillin ya kanyi dillin
- tsimagiyar kan hanya make yaro make babba
Wanda ya san ansa ya bayar in kuma kun bada gari na fada maku ansar
ANS TO UR RIDDLES
TSINTSIYA
WUTA DA HAYAKI
KANWA
KUNNE
KAZA DA KWAI
YUNWA
Thats very Impressive you two
I'll try and get some too
I shoulda used da blue.... :-/
Yadda dillin takan yi dillin haka ma dillin yakan yi dillin
'yan matan gidan mu masu fararen kunnuwa
kogi ya aki ya kawo a gefe nake wanka
yarda kaza ta kanyi kwan nan haka ma kwan nan ya kanyi kaza
tunkiya?
i dont know the last 1
Quoteyarda kaza ta kanyi kwan nan haka ma kwan nan ya kanyi kaza
tunkiya?
i dont know the last 1
FATE-FATE is for the zazzagawa's abincin su ne
wasa kwakwalwa da muhawara kuma fa? are they all this part of this room? like:
"wani mutum sun tafi fatauchi da abokinsa, sai suka samu dukiya. sai ya sai plot of land. shi kuma abokin sai ya gina daki daya a wannan filin.
sai suka nemi aure, kowannensu aka bashi.
to wanene zai tashi ya bar dakin between the friends?"
if none can afford to build another room
Shiekh I definitely think just like you.
the owner of the land? he owns the property in the 1st place
gaskiya kam IBB...tunda idan babu land din ay the other guy cannot build a room on air. dan haka sai ya tashi ya bashi plot din shi (idan ma rushe dakin zai yi sai yayi) amma dai wuri na mai plot ne.
Lets see if anyone can get the answers to theses riddles:
rawanin sarki ya faskari nadewa.....................
Uku Uku gama gari................
Dakin saurayi babu kofa.....................
kasuwa taci ta watse, ta bar kare kala.................
Na bada gari
Haba dai, well hia are the answers in order
Hanya
murfu
Kwai
Harshe
sum more pls i like the egg riddle (dakin saurayi ba kofa) lol
okay here goes..........
godiyata tana da ciki, bana hawan godiyar sai ciki na ke hawa.....................
Rigata guda, aljifunta dari......................
Hanya daya ta rabu biyu...............
Nwah woh I'm loosing my Hausa ne? I dont know these ones again. Ni dai na bada gari. Anybody wanna try before our Lady Amira drop the ans
hia are the answers in order
Daki da gado a ciki
Gidan gara
wando
IBB and other members, ku dan nemo mana other riddles cos am out of them.
Thanks ;)
Well here we go amira:-
Shanuna dubu ma daurin su daya....
Tsinstiya.
Iya ta zaga baba ya zaga basu hadu ba?
Kunne.
Dan baka a bayan shuri.....
Quote from: Bayya on November 09, 2007, 02:38:33 PM
Kunne.
Bayya kayi saurin amsawa.
Da ka yi irin ta wani bakatafe,da aka tambaye shi 'iya ta zaga baba ya zaga basu hadu ba'
His answer was 'Dan b*&^% uba, wata ta buya' ;D
Quote from: Bayya on November 09, 2007, 02:40:55 PM
Dan baka a bayan shuri.....
Farce..
Yan matan gidanmu masu farin kai
To yaya gogan,
In na amsa yanzu banyi sauri ba?
LOL...yes bayya ba ka yi sauri ba.
Carry on!
;D ;D i can answer this one
Tabarya?
Well done DB ;D ;D ;D
Ba wani kacici kacici ne?
Sai dai ka samo mana ;)
To, da ban sha'awa. Akwai saura...... Me ne?
Na sara ta ki saruwa, na bizne ta ki biznuwa.
Sarki ya sauko daga kan doki.
Kogina ya kai ya dawo. Babu mai iya ketarewa sai Bello mai dan warki.