KanoOnline Online Forum

General => Culture => Topic started by: MaAMaa_LagOS on March 20, 2003, 02:20:37 PM

Title: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: MaAMaa_LagOS on March 20, 2003, 02:20:37 PM
What's ur fave karin magana? Here are a few of mine.

 :PMuga ta fadi................kwarkwata ta dane kwabo

 :-[Na biyu kuma?..............Ance 'Kare ya sunanka?'

 8)  Baji.............................Ance da nigga uwarshi ta mutu.

 :'(Alhamdulillahi.................Muslim Braza (brother) ya fadi jarabawa.

sai naji naku. ;D
Title: Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: ummita on March 20, 2003, 05:35:36 PM
  :-X but I wont mynd learnin from others
Title: Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: adamuadamu on March 20, 2003, 06:34:51 PM
me i know dey intrested in proverbs(as of hausa)
but check this out
    WUTSIYAN RAKUMI TAYI NESA DA KASA.
Title: Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: Gimbiya on March 20, 2003, 08:13:39 PM
--- Garin dadi na nesa ungulu ta leka masai ---
--- komin nesan jifa kasa zai dawo ---
--- Ba'a kin ta mutane, barawo ya je sata ---
oh yah my favorite, my mom saying all the time
--- Abin da babba ya gani, yaro ko sama ya hau ba zai gani ba---

more to come
Title: Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: sdanyaro on March 20, 2003, 11:01:49 PM
Assalamu alaikum;
 
Check out www.Dandali.com for more... at the Proverbs (Karin Magana) Section of that web site
http://www.dandali.com/cgi-bin/proverbs/proverbs.php.  
 
You can post your Proverbs directly at
http://www.dandali.com/cgi-bin/ugb/ugb.cgi?action=addentry
 
You can also add your comments to Proverbs at
http://www.dandali.com/cgi-bin/proverbs1/guestbook.cgi?action=view&start=1
Title: Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: Rose on March 21, 2003, 12:47:47 AM
Ummita yaya Ba Hausa ne? :)
Kuwa yabar gida, gida ya barshi.
Title: Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: Hausa Error on March 21, 2003, 01:15:24 AM
eer!!! aha ni na tuno wani  amma its almost same as that of maman lagos

  Baji.............................Ance da nigga uwarshi ta mutu.

 akwai  Ji........................bagwariya na karin magana ;)
Title: Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: MaAMaa_LagOS on March 21, 2003, 11:57:06 AM
Here some more!

sai kayi......sababbe........karuwa ta ga mai wa'azi

Da ba asan asalin kuli-kuli ba sai tace da flawa akayi ta.

Mu dai muna nan anan............Iyamiri ya fada rijiya

Kan ku ake ji ........................mahaukaci ya fada rijiya "ni dai wanka na nake yi"

Allah na mutane.....................jaba ta ga bakin mijinta.

Allah sarkin dadi ...................inji barawon takanda.
Title: Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: Blaqueen on March 21, 2003, 04:45:07 PM
LoL!!!!!! ;D
Title: Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: ummita on March 21, 2003, 05:26:46 PM
Quote
Ummita yaya Ba Hausa ne? :)

Ummita (tilts her head 2 d left) .....Ke, Ice zo mu fiter waje...need 2 speak 2 u in private.......;). Awaki hausa diyawer ma sef!! Well d whole point iz err........well I no get bigmanism when it cumz down 2 learnin from others.....ammen Ice u hit me bad!!! ::) ;)
Title: Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: Rose on March 21, 2003, 08:12:27 PM
Did I?
well i was just kiddin cos me too no sabi this twist hausa
May be a little :-/
Title: Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: Hausa Error on March 22, 2003, 12:01:41 AM
sannu da zuwa kayan dadi   - bebe yaga ya ga mata
Title: Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: Rose on March 24, 2003, 02:02:01 AM
Quote
sannu da zuwa kayan dadi ? - bebe yaga ya ga mata
Thats really funny! hehehe  :D
Dama dai ba beben bane ko?
Title: Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: ummita on March 24, 2003, 12:07:01 PM
Quote
Here some more!

 she laffs......ew mother Lagos....tsaya lets assimilate d new onces..let us learn first b/4 u loads up sum more...

by d way I did get it. Infactly, I not grab any of them karin talks. A lil explanation will du ma self & ma sista Ice, errr let me call my grandmother, so that I can get alot...nxt tym I will blast this place with karin talks, Ice saboda ke zanyi haka...anyways I no go even boda    ..Mother lagos come 4ward....when is our nxt lessons due in? ;).
Title: Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: Ihsan on March 24, 2003, 09:54:07 PM
kwana nawa ne .... maye yayi amarya zai cinye ta

Ana raba ka da ciwon kyalle .... kana kyalle ta haihu

abun nema ya samu ..... matar dan sanda ta haifi barawo

a dade ana yi ..... wataran sai gaskiya

zani ce ta tadda muje mu

A rina .... an saci zanen mahaukaciya

A bari ya huce .... shi ke kawo rabon wani

Abun mamaki .... kare da tallan tsire

Ba'a ba kura ajiyar nama

Abu mai sauki .... fidda wando taka

Aikin banza .... kiba a kunne

Albarkacin kaza .... kadangare kan sha ruwan kasko

Ba'a hada gudu da tsusar duwawu
Title: Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: Hausa Error on March 30, 2003, 10:00:58 PM
ALLAH sa banyi laifi ba dai da nai postin wannan,

-kai baka iya c*n matar aboki ba sai ka mata ciki
Title: Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: Ihsan on March 30, 2003, 10:52:48 PM
::) ::)
Title: Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: Aydee Fella on March 31, 2003, 02:33:17 AM
Quote
ALLAH sa banyi laifi ba dai da nai postin wannan,

-kai baka iya c*n matar aboki ba sai ka mata ciki
Amma mallam wallahi kai tsami ne.
Title: Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: Hausa Error on March 31, 2003, 12:39:03 PM
Quote
Amma mallam wallahi kai tsami ne.

Amma goodfella kai fatiyaiye ne 'amma mallam kai tsami ne' ai ba karin magana bane, amma bari na koya maka daya

-wai kura ce zata ce da kare maye

 in kana da hankali zaka gane
Title: Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: ummita on March 31, 2003, 12:48:43 PM
Yo! Fella......kai Fella baka jine?(she hisses) dama it aint nefink, juss wanted 2 tell ya......he stole ur avator. 2 bugs bunnies.....whuz r real owner?[/b]
Title: Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: Ihsan on March 31, 2003, 08:25:42 PM
Ummita, ay haka nan suka yi!!! maybe dai idan sun wuce JJC stage su dan gyaru... >:([/b]
Title: Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: IBB on April 02, 2003, 02:41:30 PM
KAMAR DA KASA.......INJI MAI CIWON IDO

AIKIN BANZA............HARARA 'A DUHU

NA SHIGA BAN DAUKA BA......BAYA FIDDA BARAWO

SAU NAWA KUMA...........ANCE DA TSUNTSU YA SUNAN KA

YA ZAMA DOLE............CIN KASUWA DA MAKIYI

AI SAI KAYI.........KARUWA TAJI MAI WA'AZI

KAMAR GASKE.........NOMAN DAN-KOLI

BONONO...............RUFIN DAKI DA BARAWO

TASHIN HANKALI..........FADA DA MAI-GARI RANAR SALLAH

TASHIN HANKALI..........GOBARAR GEMU

'DOKI..........KAMAR SABON ANGO
Title: Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: IBB on April 03, 2003, 08:50:02 PM
ZANCEN KAKE SO...........ANCE DA GAURO YA IYALI

RASHIN HAKURI KAMAR ZAWO

YA ZAMA DOLE............ACE DA MIJIN IYA BABA

YAU DA GOBE TAFI WASAN YARO

SHEGE NA KAUYE.........ARZIKIN MATSIYACI

KOWA DA ARZIKIN SA..........MAI DOKI NA ADUA A KUTURI

RAKIYA MUKAYI DUNIYA.........MATSIYACI YAGA MAI JAKAI

TURURUWA MA A RANAR BANZA TAI JIDO BALLANTANA RANAR GARAR YAR TA
Title: Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: IBB on April 08, 2003, 05:41:34 PM
MAAMA LAGOS A MULMULO KAKIN MAGANA ;D
Title: Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: Blaqueen on April 13, 2003, 02:09:50 PM
there's one used when a person is such a good lair and hypocrite...

"idan ta riga ki zuwa courti, sai dai ku taradda da igiya"...

meaning if the person first u reach court, they go hang u.. cuz the person is good at lying, the court already pronounced u executed...
Title: Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: IBB on April 15, 2003, 06:18:04 PM
Quote
there's one used when a person is such a good lair and hypocrite...

"idan ta riga ki zuwa courti, sai dai ku taradda da igiya"...

meaning if the person first u reach court, they go hang u.. cuz the person is good at lying, the court already pronounced u executed...

LOL ;D NICE 1
Title: Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: Guduma on August 06, 2003, 02:28:59 PM
Nima ga 'yan kadan da na sani.......

Jeji bai gama cin wuta ba, fara bata isa barka ba
Bakin ciki ba bakon Uwar barawo bane
Wanda zaa yanke,  ai ba sai an mai wanka ba.......
Manyan abu,  wai karuwa ta ga jaki tsirara!
Ba girin girin ba dai tayi mai, wai kura ta dauki gurmi
Kunama, mai horo da gindi!
Ka tambayi kunne zakin miya? Tambayi baki kasha labari!
Title: Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: kilishi on August 06, 2003, 03:43:50 PM
Ba kullum ake kwana a gado ba
ba girin girin ba tayi mai
inda ba kasa ake gardamar kokawa
abinda ka shuka shi zaka girba
iya ruwa fidda kai
aiki yaro in da yake so kaga sauri

meet you next time
Title: Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: nicer_007 on March 12, 2004, 11:59:29 PM
GANE MINI HANYA...... MAKAHO YA SO TSIGUMI
TAYA NI FIGA.... UWAR MIJI TA ZAMA KAZA
ABU MAI SAUKI... DOKAR UWAR MIJI
LAIFI TUDU NE .... TAKA NAKA.... KA HANGI NA WANI
Title: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: Shiekh on June 09, 2004, 04:11:06 PM
Kare da kudinshi sai ya sha "LAHAULA..."
Title: Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: jewel(abdulgee22) on August 01, 2004, 09:16:06 AM
Quote from: "MaAMaa_LagOS"
What's ur fave karin magana? Here are a few of mine.

 :PMuga ta fadi................kwarkwata ta dane kwabo

 :-[Na biyu kuma?..............Ance 'Kare ya sunanka?'

 8)  Baji.............................Ance da nigga uwarshi ta mutu.

 :'(Alhamdulillahi.................Muslim Braza (brother) ya fadi jarabawa.

sai naji naku. ;D

ALLAH YA WADAN NAKA YA LALACE...............RAKUMIN DAWA YAGA NA GIDA.
 THIS HAS BEEN MY FAV , BECUS JUST IMAGINE THE LOOKS THE
NA DAWA IS GIVEN NA GIDA WITH ALL THOSE LOADS .

KARSHEN TIKA TIKA TIK...................

IN ALLAH YASO.................KO A TUKUNYA ZAKARA SAI YAYI CHARA

CORRECT MOI FOR ANY MISS KATE
Title: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: Anonymous on May 12, 2005, 10:00:26 PM
Shiekh I definitely agree with your words.
Title: Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: mlbash on June 06, 2005, 06:43:43 PM
Quote from: "UmmAyman"
kwana nawa ne .... maye yayi amarya zai cinye ta

Ana raba ka da ciwon kyalle .... kana kyalle ta haihu

abun nema ya samu ..... matar dan sanda ta haifi barawo

a dade ana yi ..... wataran sai gaskiya

zani ce ta tadda muje mu

A rina .... an saci zanen mahaukaciya

A bari ya huce .... shi ke kawo rabon wani

Abun mamaki .... kare da tallan tsire

Ba'a ba kura ajiyar nama

Abu mai sauki .... fidda wando taka

Aikin banza .... kiba a kunne

Albarkacin kaza .... kadangare kan sha ruwan kasko

Ba'a hada gudu da tsusar duwawu
 GREAT! IM REALLY TRIPPED!
Title: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: neozizo on August 08, 2005, 08:53:29 PM
kallo ya koma sama.....
shaho ya dauki dan giwa.   :o

Duk wanda ya hau motar Kodayi
.....zai sauka a tashar wulakanci!   :oops:

abun nema ya samu.......
matar falke ta haifi jaki   :D

Dokin mai baki.........
yafi gudu   :wink:

Banza a banza........
Kare a PDP!
Title: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: Nabulsi on October 19, 2005, 04:00:40 PM
Kai IBB! Ice dai kai jikan barbushe ne ko? Irin wannan karin magana haka sai kace Waziri aku.
Title: Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: jaybee on February 07, 2007, 12:21:45 PM
wata sabuwa kuma... in ji 'yan caca
Title: Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: amira on July 17, 2007, 09:14:37 PM
wai ma.......maganar banza.
Title: Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: HUSNAA on July 18, 2007, 11:45:05 AM
Abin nema ya samu, wai matar direba ta haifi mota

Hmm.. jiya ba yau ba, tsoho ya tauna kashi

Kaya kaya budan kan karya.

Mugani a kasa, an ce da kare ana biki a gidan su.

Faduwa ta zo dai dai da zama.

Da tsohuwar zuma ake magani.

Sannu sannu bata hana zuwa.. sai dai a dade ba a je ba
Title: Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: amira on July 18, 2007, 05:24:51 PM
sususu da shashasha in kunga sakarai ku taho tare.

tsiya zata tada tsohon bashi

duniya kamar rawar yan mata ce, na gaba ya koma baya
Title: Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: amira on July 20, 2007, 03:35:52 PM
hausawa kan ce nan gani nan bari
Title: Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: Dan-Borno on July 20, 2007, 05:24:31 PM
Ba a kin ta mutane: ance da barawo ya gudu

Shure Shure baya hana mutuwa

Barin kashi a cike, baya maganin yunwa

 ???
Title: Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: amira on July 31, 2007, 12:54:32 AM
Mai nama ya kan nemi wuta

Samu yafi iyawa

Kama da wane ba wane ba
Title: Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: IBB on July 31, 2007, 11:24:14 AM

Kama da wane ba wane ba

This reminds me of Cafenol advert when i was young.

In tayi ruwa rijiya in bata yiba masai
Title: Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: amira on July 31, 2007, 06:46:48 PM
aikin banza makaho da waiwaye.

gani yafi ji

da taka muguwar rawa gwama kin tashi

Giwa a garin wani zomo
Title: Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: IBB on August 09, 2007, 08:41:21 PM
Ina ruwan ungulu da kitso

Kafin 'a kirga mutane an kirga mutun

Wanda baiji bari zai ji hoho

Karshen alawa kasa

Anci gaba, wanda zaije sama ya taka leda

Arziki yaci uban nada an sai da gida an sai bulo

Da na sani kyeya ce
Title: Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: Bayya on August 27, 2007, 06:23:02 AM
You guys have said almost all, amma ga kari.

Wai kunkurune zai yi wa bushiya kafa

Shagwaba......tarwada da kukan kishirwa

Ai sai kayi ta yi.....karuwa ta ji mai tafsiri
Title: Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: Dan-Borno on June 11, 2008, 10:52:15 AM
hey guys please help me shade more lights on the
meaning and usage of this proverb.

Ba a gudu da susan duwawu
Title: Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: IBB on June 24, 2008, 11:19:50 PM
Let me see if I can help

Dont speed when your tank is empty. (U may not get far)
Title: Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: IBB on June 24, 2008, 11:28:40 PM
Barin kashi a ciki baya maganin yunwa
Title: Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: gogannaka on June 25, 2008, 01:09:45 AM
Barin kashi a ciki baya maganin yunwa

Anya wannan abun gaskiya ne.
Gaskiya fa yana magani.
Title: Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: gogannaka on June 25, 2008, 01:14:54 AM
Sanabe----hanci da rawar dari(cold)
Title: Re: Favourite Hausa Karin magana/proverbs
Post by: Ahmed.WANG on December 23, 2008, 10:47:43 AM

In ka ga gemun 'dan uwanka ya kama wuta shafa wa naka ruwa.

Gwanin ruwa shi ruwa ke ci.