Wasu tambayoyi daga dan kasar Poland

Started by Bartek, June 08, 2006, 03:21:24 PM

Previous topic - Next topic

0 Members and 1 Guest are viewing this topic.

Bartek

Salaam,
Ni dalibi ne daga kasar Poland. Ina sha'awar harshen da al'adar Hausa sosai. Na ziyarci Kano bara wallahi akwai mutane masu kirki masu hankali da yawa a can. Amma ina can mako biyar kawai saboda haka ban iya fahimci abubuwa da yawa ba. Hakika ina da tambayoyi da yawa. Amma da farko bari in tambaye ku wani abu:

Lokaci-lokaci idan kuna hira da wasu yan hausa ku kan ji turanci kuma ku sauya daga turanci zuwa hausa ko daga hausa zuwa turanci. Wannan abin mai sha'awa ne kwarai. Sai ku fada mini me ya sa ku kan yi wannan.
Yaushe ya kamata a yi wannan a ganinku?

Na gode sosai

Sai an juma!

Abdalla

Barka da rana, Aboki daga Polan

Lafazin da ka ji ana amfani da shi a Kano lokacin da ka zo shi a ke kira da ENGHAUSA - watau had'a yaren Ingilishi da na Hausa a cikin magana d'aya. Wannan d'abi'a ce ta 'yan boko - watau wad'anda su ka yi karatun zamani. Da ma ai wanda bai iya Ingilishi ba, ba zai yi ENGHAUSA ba.

Babu wani dalilin yin haka sai dai sabo da kuma sha'awa. Da yawa ba sa son yin haka, amma wannan ya fi ga wad'anda suka manyanta (watau wad'anda su ka d'an girma), domin samari (daga 10-35) sun fi sha'awar yin haka. Wad'an su kuma suna yi ne domin su nuna birgewa, domin a ce su 'yan birni ne.

Kada ka manta, yin ENGHAUSA ya danganta da mai yin maganar, da kuma wanda ake yi wa maganar. Idan wanda ake yi wa bai iya Ingilishi ba, to dole mai yin maganar ya tabbatar ya yi da tsabagiyar Hausa, ba tare da ya cakud'a da wani yare ba.

Sannan kuma wani k'arin bayani shi ne cewa wad'anda suka iya wani yaren (harshe) su kan yi haka. Misali, wad'anda su ka iya LARABCI  su ma suna gauraya harshen Hausa da na Larabcin. Haka ma wad'anda suka iya ko Yarbanci ko Fidinci (watau Pidgin English), su kan gauraya -- saboda haka ba wail sai lallai Hausanci ba.

Idan kuma akwai wani k'arin bayanin bayan wannan, to don Allah jama'a a dad'a fahimtar da mu gaba d'aya.

Abdalla

admin

Assalamu alaikum;

To Dalibi Bartek, mungode da wannan tambayar taka. Haka kuma muna godiya da amsar da Shehun Malami Abdalla ya bayar.

Madalla.
Kaini Kano ko a buhun barkono!!!

mlbash


Mr. Bartek you amaze me seriously for you write the hausa words most accurately! you are welcome and i hope you'll be patronising the forum to advance your learning.
t is my intention to make the neglected aspect of our societies viable