Makomar Niqabi a kasashen Turai

Started by bamalli, June 02, 2010, 02:18:08 PM

Previous topic - Next topic

0 Members and 1 Guest are viewing this topic.

bamalli

Makomar Niqabi a kasashen Turai

Irin wannan Niqabi na ci gaba da jawo cece kuce a kasashen Turai

Kasashen Turai da dama sun dade suna nuna adawa

da Niqabin da mata musulmai suke sakawa domin kare fuskokin su.

Kama daga Niqabi, wanda ke rufe fuska da Hijabi mai rataya, wanda ke rufe jiki baki daya.

Abinda ake tattaunawa akai shi ne na 'yancin mata da addini dama tsoran ta'addanci.

Sai dai al'umar musulmai sun koka game da makomar hakkin su na bil'adama da 'yancin rayuwa.

Faransa ta yi kaurin suna
Kasar Farnsa na cigaba da matsa kaimi kan shirinta na haramtawa mata musulmai sanya Niqabi a bainar jama'a.

Shugaba Nicolas Sarkozy, yace zai mika kudurin dokar ga majalisar dokokin kasar a watan Mayu, domin hana sanya hijabin "a bainar jama'a".

Wani kwamitin majalisar dokokin Faransa ya bada sahwarar haramta mayafin, yana mai cewa ya sabawa al'adun kasar.

Sai dai majalisar koli ta kasar-ta yi gargadin cewa dokar za ta iya sabawa tsarin mulkin kasar, dama kundin kare hakkin dan adam na tarayyar Turai.

A shekara ta 2004 ne aka fara bullo da haramta amfani da hijabi mai rufe jiki, kuma dokar ta samu karbuwa tsakanin jama'a, a kasar da ake kokarin raba addini da al'amuran kasa.

Sai dai za a takewa musulman kasar hakkin su, wadanda adadin su yakai miliyan hudu zuwa biyar.