Nema na aka yi na dawo PDP-in ji Atiku

Started by bamalli, June 02, 2010, 03:07:16 PM

Previous topic - Next topic

0 Members and 1 Guest are viewing this topic.

bamalli

Nema na aka yi na dawo PDP-in ji Atiku
 
 
Atiku ya dade yana sansana jam'iyyar PDP
A Najeriya Tsohon mataimakin shugaban Najeria Alhaji Atiku Abubakar, ya ce neman da wasu manyar jam'iyyar PDP suka yi masa ne yasa shi dawowa jam'iyyar, ba wai kawai neman takara kamar yadda wasu ke cewa ba.
A wani taron manema labarai da ya kira a Abuja, ya bayyana cewa a yanzu shi dan jamiyyar PDP mai mulkin kasar ne, domin an yi masa rajista daga mazabarsa ta jihar Adamawa.

Atiku Abubakar ya nunawa manema labaru da sauran mutanen da suka halarci taron katin rajistar ta sa.

Shi dai tsohon mataimakin shugaban Nijeriar, ya fice daga jamiyyar PDPn ne a shekara ta 2007, sakamakon takun saka a tsakaninsa da tsohon shugaban kasar Cif Olusegun Obasanjo.

Komawarsa jam'iyyar ya gamu da tirjiya daga wasu 'yan jamiyyar a mazabarsa, inda suka ce ba sa maraba da shigarsa jam'iyyar.