ALLAH KO SHINE ABIN GODIYA

Started by EMTL, January 13, 2004, 02:13:29 PM

Previous topic - Next topic

0 Members and 1 Guest are viewing this topic.

EMTL

ALLAH KO SHINE ABIN GODIYA

Wataran ina kilisa akan laulawa
Nai tsinkayi sai ga mutum mai kyawun yawa
Yayin da ya yunkura don tsayuwa
Nan ga kafa babu sai dogarawa
Gurgu yake amma ba alamar damuwa
Ashe mai kafafu lalle ko zai godiya

Sai nai gaba ina mai-yawan godiya
Sai nai kicibis da mai godiya
Sai nace “Sannuka Mallam Mai yawan godiya”
Sai yace “Niko ni nake kan godiya”
“Sani ni makaho nike ni ina godiya”
Sai nai tuni ni ko ga Jarin-Mujiya
Lalle ko Allah shine abin godiya

Nai gaba sai gani hanyar gida
Sai nai karo da yaro abin-sha’awa guda
Yai tsaye shiko a gefe guda
Mai-hamdala “Ya ka kebe gefe guda?”
Yai shiru-ashe kurma guda !
Nai salati (SAW), lalle ko Allah abin godiya

Ai gashi gurgu, makaho da bebe duk suma suna godiya
Mu Yan-Adam lalle ai ko sai godiya
Mu tuna fa Allah shine abin godiya
Ni mai kafafu lalle ko zan godiya
Ga kunnuwa lalle ko ni ko sai godiya
Ga kalami lalle ko sai godiya
Kaichonmu idan dai ba godiya

Shin an yarda Allah shine abin Godiya?
To lalle a dilla a wani ma ya zan godiya
Kada ai kasala lalle a maimaita yin godiya
Allahummma salli alan nabiyyin mai yawan godiya
Allahumma Allah mahalicci abin godiya
Lalle ko Allah shike abin godiya.


Fassarar EMTL,
7th Dhul Qidah 1424 AH
30th December 2003 CE
In the Affairs of People Fear Allah (SWT). In the Matters Relating to Allah (SWT) Do not be Afraid of Anybody. Ibn Katthab (RA).

Twinkle

Alhamdullilah, dat was really good,
Ai fa ya kamata mutum ya dinga godiya ga Allah no matter wat condition a person is in, even if a person hasn't eaten for 2 day.
color=red]I RULE IN A UNIQUE WAY!

[/color]
[/i]