Birnin Iko Kano

Started by Sas, November 20, 2004, 08:23:36 AM

Previous topic - Next topic

0 Members and 1 Guest are viewing this topic.

Sas

Salamu Alaikum,

haba mutanen Kano? Me yake damun mu? Zuwa na birnin iko yan kwanaki da suka wuce nayi mamakin yadda da wuya ka samu mutum mai karfi a jikinsa yana yin bara. Kwata kwata basu yarda da wannan ba. A takaice, abun da ya bani mamaki shine maimakon matasa kamar mu su rinka yin bara sai kaga suna sayar da abu buwa da dama dan dai su samu abun da zasu ci. Amma a kano fa? Inaa ai gwara na yi bara ko tumasanci na samu naci da dai na samu ina sayar da wani abu. A kan hanya a iko zaka samu abubuwa da dama kamar su kayan moto, taya, tip, kayan keke, abun sha, abun ci, tumatur, allayahu, dankali, kaset na bidiyo da CD. A takaice dai komai.

Wannan yana nufin cewa muma yan kano mu fito kan titi mu sayar da Tubani ko masa? AA!!! Amma dai ya kamata mu lura muga cewa bara ma kanta baa yarda mutum yayi ta a addinin mu ba kuma ace mutum da karfinsa yana bara? Allah ya kiyaye. Gwamnati bata aikinta a wannan fannin yadda ya kamata.

Bissalam
ny good thing I said is from Allah and any bad thing I said is from me...So I ask for Allah's forgiveness for my errors both conscious and unconscious ones...Ameen!!!