YANTAR DA KANKA DAGA BAUTAR GUMAKA DA IYAYEN GIJI (MUTANE)

Started by Idris, February 27, 2006, 07:49:59 PM

Previous topic - Next topic

0 Members and 1 Guest are viewing this topic.

Idris

YANTAR DA KANKA DAGA BAUTAR GUMAKA DA IYAYEN GIJI (MUTANE)

Akwai bautatarwa ta jiki da kuma ta zuciya, bautatarwa ta jiki shine ? tursasa mutum ya zama bawa wato yake yin hidima ga waninsa ba da zabin kansa ba, da karfi.

Ita kuwa bauta ta zuciya (wato cikin tunani) shine a karkatar da zuciyar mutum  maimakon jikinsa ta hanyar hilatarwa da gurbata tunaninsa ya auka cikin hidima (bauta) alhalin shi yana zaton yantacce ne shi; mai yanci.

Mutumin da aka karkatar da tunaninsa aka gurbata  masa tunani ya zam bawa to babu shakka bawa ne har a zahirin sa. Wannan shine mafi munin abin da ke faruwa ga mutum; mutuwa ta kan fi alheri gareshi.

Shi kuma Gunki shine duk wani abu da ake amfani da shi don bautatarwa ga tunanin mutum, duk abin da ake iya gabato da shi a shashantar da zuciyar bawan da ke mika wuya, ya dimauta. Ya auka cikin hidima (bauta) shine Gunki.

YANCI
Dan-Adam yana da jiki da kuma ruhi; a yayin da ya zamanto hikimar rayuwa itace kowanne mutum ya inganta tunaninsa ya kyautata shi don ya daga martabar ruhin nasa da kansa a kebe, shi kuwa gangar jiki shine gundarin abu na zahiri wanda ta hanyar sa ne mutane suke cudanya da juna, suke kuma bayyanar da bukatunsu da aniyarsu. Hakika mutane muna da sabani a jikkunan mu da kuma halin mu, amma ba a ruhin mu ba. a ruhi kam dai-dai muke.

Dukkanin mutane an halicce su yantattu ne (ba bayi ba). Dukkanin mutane daya suke a ruhi, babu banbanci ko da tsakanin jinsin mace da namiji.

Banbanci da muke dashi a jiki an halittashi ne don a gyara lamuran mu ya zamanto mun sami saukin gudanar da harkokin mu na zahiri cikin duniyar nan da muke tarayya a cikin ta.

Abu ne da ya zama tilas mu kasafta ayyukan mu a tsaknin mu; amman wannan bai maida wanin mu ya zama yafi sauran ba. Mafi alheri cikin mu shine wanda yafi imani, wayewa da hali na gari, mallakar abin duniya ko matsayi ba abin lura bane kwata-kwata. Dukkanin sabanin mu na zahiri sun kasance ne don mu fayyace mu gane junan mu, dan samun saukin gabatar da zarafin mu na rayuwa. Allah mabuwayi da ya halicce mu baya duban jikkunan mu da abin da muka mallaka, sai dai abin da zukatan mu suka kudurce.

Shugaban kasa ko Gwamna babu ta inda ya dara sauran mutanen gari, Liman ko Fasto bai zama yafi sauran mabiya ba, mutum dan asalin kasar Hausa bai dara mutum da asalin kasar Yarabawa ba, haka mutumin dake zaune a Enugu bai fi mutumin da ke Okene ba. Ko wanne mutum ya kan kasance yaro ne shi ko kuma babba (mai Hankali). Dukkan babban mutum yana da cikakken yanci.

Ko wane mutum mai hankali yana raye ne ko tana raye ne don amfanin zuciyar ta/sa. Duk wani mai hankali ba zai tinkari aikata wani abu ba face ya fahimci fa?idar abun ga zuciyar sa/ta  matsawar ba haka bane to wannan ya zama bautar (da bata da lada ba faida ke nan) kamar yadda ya haramta ga mutum ya zama mai girman kai, jijji da kai, fankama da alfahari, hakanan haramun ne mutum ya wulakantar da kansa, ya zama mai jin nakasu a tare da shi. Dukkanin mu ayarin mu guda ne.

A lokacin da aka yanke wa sabon jariri cibiya, to igiyar farko cikin igiyoyi uku da suka maida shi mai dogaro da wani an katse ta. Daga nan fa jaririn ya zamo ba wani yanki ne shi na jikin mahaifiyar sa ba, ya sami kwarya-kwaryan yanci  yaron zai ke cin abincin sa ta baki, ya kuma shaki iska kai tsaye ta hancin sa daga iskar gari. Akwai sauran igiyoyi biyu da za a katse su nan gaba a rayuwa. Yaron zai girma ya kosa ya sami  cikar hankalin sa don fuskantar kalubalen rayuwa. Mutum mai hankali yantacce ne shi dangane da zuciyarsa, a yayin da hankalin mutum ya cika don tunkarar rayuwarsa da kansa, Allah Madaukaki zai yanke igiyar ta biyu, to daga wannan lokaci ne fa wannan sabon mutum yakan dauki dawainiyar samawa kansa dukkanin bukatunsa na ruyuwa, da kare mutuncin kansa (a wannan lokaci ne ake fara kiran mutum mukallifi ko baligi) idan rayuwar sa zata yi kyau ko zata yi muni zai danganta ne da yadda ya kyautata cin moriyar kyautar da Allah yayi masa ta hankali da zuciyarsa. Daga wannan bigire ne fa mutum ya zama baligi koda yake ba duka baligi ne yake mutum ba ai wasu baligan sun fi dabba munin hali, da lalecewa.

Igiya ta farko da ta maida mutum mai dogaro ( wato cibiya) mutum ne yake yanke ta, ta biyu kuma (wato cikar balaga) Allah ne da kansa yake yanke ta a lokacin da ya raya shi ya balaga, yayi hankali. Igiya ta karshe wadda da ita ne ake tantance ingancin rayuwa, mutum ne yake yanke ta da kansa. Ko wane mutum shi ke da ikon ya daukar wa kansa zabi ko dai ya zama cikakken mutum mai hankali (mumini) ko kuma ya kangare. Dukkanin mu muna da dama iri guda ne dangane da daukar waccan shawara. Makasudin rayuwa shine zama cikakken mutum na gari. Babu wani abu da ya banbanta mutum da sauran halittun Allah  face dai hankali da kwakwalwa, ta hanyar kwakwalwar mu ne muka sami ikon sarrafawa da jujjuya sauran halittu.

A zahiri Zakoki sun fi karfin mu amma ta hanyar kwakwalwar mu mun kame su a cikin gidajen zu. Giwaye sun dara mu girma nesa ba kusa ba amman a yau muna iya tsare su a gidajen zu. Muna iya rugurguza manyan duwatsu mu gina dogayen gidaje. Madalla, da wannan kwakwalwa. Ka zaci kanka karami amman a cikin ta duniyar take.

A lokacin cikar hankali da balaga kowanne mutum yana fuskantar zabi ne guda biyu a rayuwar sa, ko dai ya shelanta kwato yancin sa daga dukkanin bautar wasu mutane ya zabi rayuwa kyakkyawa ta hankali ko kuma ya tabbata bawan son zuciyar wani ya halaka, ya tabe, ko wanne mutum; imma dai sarki ne shi ko sarauniya ce ita, don haka ya cancanci a martaba shi.

BAUTA
Mutane suna da soye-soyen zukatan su, sannan kuma an basu karfin hankali don ya dai-daita wannan son zuciya. Dukkanin mu muna zaune ne a duniyar mu ta zahiri guda daya ne, don haka babu makawa sai mun kasafta duniyar a tsaakanin mu bisa adalci. Allah Mai rahama da ya halicce mu bai yi mana kwauron ababen bukatar mu ba; akwai wadata kusan ma sama da iyakacin abinda zamu nema, wasu mutanen saboda sakaci da muguwar aniya sai suka ki yarda su kauwame son zuciyar su sai suka zama tamkar dabbobin daji wajen neman biyan bukatar su na son zuciya sun zabi su rufe idanun su suyi watsi da yanci da mutuncin sauran mutane. Lokacin da Allah ya turo mu nan duniya, ya turo mu ne a daidaikun mu kuma zai tashe mu ne a wannan banbar rana ta tashin kiyama don mu fuskanci hisabin mu daban-daban. Babu wani rai da zai dauki aikin wani ran. Allah bashi da dangi, don haki babu wanda ke da kusanci da Allah, saboda halittarsa. Annabi Isa da Annabi Muhammad (amincin Allah a gare su) mutane ne kamarmu ba wata halittar Allah ta musamman, bane su, hakika Allah adali ne shi. Allah ya aiko littatafansa don ya gana kai tsaye da bayin sa. Makasudin ganawar shine fahimtarwa da wayar da kai. Allah ba zai rikita zancen sa a kasa fahimta ba, shi kuma mutum ba sakarai bane shi da zai kasa fahimtar sassaukan zancen Allah mai hikima .

Lokacin da Allah ya saukar da Al-Kur?ani mai girma ga Muhammad (SAW) an umace shi da ya kiyaye ya bar kalaman Allah hakanan yadda aka isar da su a gare shi ta yadda zai zama ga mai karanta shi a yau tamkar yadda annabin ya karbe shi daga Allah. Babu wani wanda ke shiga tsakanin wani da Allah a dangane da abinda ya shafi ibada.

Al-Kur?ani shine kadai ingantaccen littafi da mutum zai dogara da shi. Ilimin kimiyya na iya ci gaba amman Al-Kur?ani shine tabbatacciyar gaskiya. Al-Kur?ani yana dai-dai da gaskiyar rayuwa, kuma yana magana ne da hankulan mutane.

Shi Al-Kur?ani ya gabatarwa da mutane cewar kada su karbi abinda baza su fahimce shi da hankulan su ba.Imani ta hanyar yakini yake zuwa kuma babu wani wanda za a azabtar dashi akan abinda bai fahimce shi bisa yakini ba. Annabi Muhammad (SAW) ya kalubanci masu adawa da shi akan cewa su zo da wata gaskiya da tafi wadda yake kai zai karba.

Don haka duk wanda yaki yarda yayi aiki da hankalin sa ya zama wawa, wanda kuma ya zauna ya bar wani yana wasa da hankalin sa, yana juya akalarsa yadda ya so to ya zama sakaren bawa. Mutum fa sarki ne da yake alaka da wasu sarakunan ko wata sarauniyar bisa cikakken yanci da iko iri daya. Kyakkyawan umarni daga Allah:- ?KADA KAYI ZALUNCI KUMA KADA KA BARI A ZALUNCE KA?.

Shelanta cewar babu wani mai hukunci sai Allah, adali shi kadai shine ya maida mutum cikakken mutum.

Babu shakka dukannin gwagwarmayar rayuwa ana yin ta ne don a kubuta a sami kwanciyar hankali da farin ciki ne. dukkanin mutum yana yunkurin samun farin ciki ne. Ga mai hankali rayuwa shine cimma ainihin farin ciki tabbatacce.

Shaidanun yan siyasa wadanda suka ki amincewa su kyautata zukatansu, sune suke riyawa tamkar sun san don me Allah ya halicci sammai da kassai.

Sune suka kaga sabbin Gumaka na zamani don su bautar da sauran mutane, alhali an halicce mu yantattu daga bautar wasu mutane. Kangarewa Allah shine matsalarda ta dade tana gudana kuma dukkanin annabawa suka zo don su kawar. Annabi Muhammad (SAW) ya kasancce shine na karshe a jerin annabawa. Duk annabawa an aiko su ne don su gargadi mutane su fahimtar da su yi aiki da hankulan su da basirar su domin su tsira daga bautatarwa cikin tunani.

A yayin da sauran annabawa aka aiko su ga wasu al?ummatai a kebe, shi kuma Annabi Muhammad (SAW) ga dukkanin jinsin bani-adama aka aiko shi don haka ne ma ya zo da littafin duk duniya, littafin da zai tabbata har karshen zamani.

Sakon dukkanin annabawa a fayyace yake cewa ku kangarewa dukkanin Gumaka, ku mika wuya ga hukunci na Allah mabuwayi shi kadai. Duk wani kubutaccen mutum yantaccen musulmi ne shi. Mutumin da yake hakikanin yantacce daga bautar wasu mutane sa?annan kuma ba bawan tasa son ziciyar bane shi babu shakka Musulmi ne shi, ba tare da la?akari da sunan da ya kira kansa ba. Wannan shine sunan da ake tantance masu yancin tunani na gaskiya, kace ?ya ku mutanen littafi! Ku taho zuwa ga kalma mai daidaitawa a tsakanin mu da ku; kada mu banta wa kowa face Allah. Kuma kada mu gwamaita komai da shi, kuma kada sashen mu ya riki sashe ubangiji , baicin Allah? to idan sun juya baya  sai kuce ? kuyi shaida cewa lalle ne masu sallamawa ne? (Imran aya ta 64).

.Ba wani abu ne Musulmi ba face dai mai sallamawa yana neman gaskiya ne , ya kuma tsayu a gareta. Musulmi shine duk wani cikakken mai aiki da hankali, hikima da basira wajen gudanar da dukkanin shafukan rayuwarsa guda biyu. Musulmi shine mutumin da ya amince ya kuma mika wuya ga hukuncin Allah shi kadai. Suna da Allah ya baiwa irin wadannan mutane shine Musulmi ita kuwa hanyar rayuwar tasu sunan ta Musulunci (Al-Islam).

Shafin farko na rayuwa shine neman fahimtar ma?ana, hikima da kuma dalilin ita kanta rayuwar (menene ya dace a so shi, me ya dace a ki shi), shi kuma daya shafin shine na biyan bukatar abinda ya dace  rai ya so (wato biyan bukata).

Kama yadda ya kasance musulmi ba shi da ikon ya tursasa wani ya bi tsarin rayuwar sa (musulunci), haka ma babu wani mahaluki da ke da ikon ya tursasa musulmi yabi tsarin rayuwar sa.

Musulmi ba Bahaushe bane shi, ba Bayarabe bane kuma ba Inyamuri bane koda kuwa yana magana da wadannan harsuna kuma iyayensa yan asalin wadannan yankuna ne.

Musulmi ba dan Nijeriya bane shi ko dan Amurka ko dan Japan bane, ko da kuwa yana zaune a wadannan kasashe.

Musulmi ba dan Shi?a bane shi, ko dan Sunni ko Kirista ko Yahudu ko Baindiye bane. Wadannan sunaye ne da aka kirkira don a kawar da mutane daga Allah.

Shaidanun yan siyasa ne suke hura wutar kabilanci da kishin kasa don cimma muguwar anniyar su.

Miyagun yan siyasa ne a ko da yaushe suke haddasa fitina tsakanin Bahaushe da Inyamuri ko Bayarabe. Wadannan ibilisan mutanen su ke gwara musulmi da kiristoci. Irin wadannan shaidanun sune suka kago tsarin siyasar da suka kira shi tsarin nuna wariyar launin fata (Apartheid) a kasar Afirika ta Kudu, su wadannan ibilisan sune a yanzu suke cikin kasar Iraki don dora son zuciyar su akan wasu mutane.

Suna mulki ne ta hanyar rarraba kawukan mutane; fifita wasu akan wasu da kago wasu  ababen bauta (Gumaka).

Duk mutane suna da son kai, duk wanda ya sami dama  zai so ya zama mai bada doka (Ubagiji) in banda wadanda suka yi imani da Allah da ranar kiyama, imani na gaskiya.

Akwai wasu gungun mutane da suka shelanta a bayyane cewa su kam sun kangare wa Allah babu ruwansu da shi, don haka suna gudanar da harkokin su babu la?akari da Allah kan duk shawarwarin su sun kira wannan tsari nasu da suna ?Secular System? wato tsarin sekular. Wadannan fa sun bayyana kangarewar su ga Allah.

Daya gungun mutanen sun fi ga munafunci. Sun yi da?awar cewa Allah suke bautawa amma a zahiri sun kafa kawunansu ne a matsayin jakadun Alah. Su ake bautawa maimakon Allah. Sun zo da sunan addini kuma masanan badini.

Sunnanci, Shianci, Kiristanci da addinin Hindu basu banbanta da tsarin Sekulanci ba (tsarin da babu Allah a cikin sa) duk wadannan tarkon shaidan ne don ya rudar da mutane ga barin musulunci.

Shin mutum nawa ne suka yi imani da annabin Allah Musa (AS) a lokacin da yake a raye duk da irin gwagwarmayar da ya sha kan yayan Israila? Amma a yau sai ga makiya sun kago ?Talmud? (liitafin dokokin rayuwa na Yahudawa) don su kawar da mutane daga koyarwar Musa (AS). Annabi Isa (AS) bai sami sama da mutum fiye da sha biyu musulmi a tare da shi ba. Kaico! Shaidanu a yau sun maida shi abin bauta, bayan sun gurbata At-Taura, dubi yadda littafin (gurbatacce) ya gaza daidaito da ci gaban kimiyyar zamani sa?annan ya sanya mutane da yawa suna shakku da kyamar addini.

Wadanda suka kagi Sunnanci da Shianci sun yi yunkurin gurbata Al-Kur?ani, amma da suka kasa sai suka kagi tasu Talmud din (HADISI) don maye gurbin Al-kurani. Sun maida annabi Muhammad (SAW) abin bauta, alhali ya dace ne ya zama kyakkayawan abin koyi ga mutane (musulmi na gari) sai gashi ana kallonsa tamkar abokin tarayya ne ga Allah, daga lokacin da suka maida shi  abin halitta na musamman sa ya zama ba abin koyi ba, alhali wanan dalili ne ya sa Allah bai aiko wani Mala?ika ba amma ya aiko mutum irin kowa. Ba abin mamaki bane da ya kasance  Sunna da Shi?a suna daukar hukunce-hukuncen su ne daga Hadisi maimakon Al-Kur?ani. Hukunce-hukuncensu nawa ne suka saba da Al-Kur?ani? Ba kuma don shaidanun basu san cewa littafin Allah ya cika da gaskiya da adalci ba ne kuma babu abin da ya rage Allah bai fade shi ba. Shin Musulmi nawa aka bautatar a  cikin wadannan kagaggun addinai?

Kamar yadda karl Max ya lura addini (irin waccan) ba shakka maye ne ga talaka. Ta hanyar Hadisi ne Sunna da Shi?a suka sami dama suke jefe mutane su kashe su, sa?annan suka hana wa mutane barin kukumin da suka jefa mutane a ciki ta hanyar irin wancan Hadisin ne suka tauye mutane suka mai da su tamkar mutum-mutumi.

Sun hana wadanda ba musulmi ba karanta Al-Kur?ani (alhali Allah ya aiko da shi ya zama shiriya ga duk mutane), su ka kago doka sukace wanda ba musulmi ba ba shi da tsarki (najasa ne shi), suka kuma kange musulmi daga nazarin Al-Kur-ani domin a fadinsu musulmi sakarkaru ne baza su iya fahimta da kwakwalwarsu ba. Suna bukatar taimakon wasu Sufaye da ke riya cewar suna da wata ganawa ta musamman da Allah ? hakika wannan  bautatarwa ne.

Sura ta 56 aya ta 79, Allah Mai Hikima yayi bayanin cewa mutumin da ke da tsarkin zuciya shi ke iya fahimtar sa. Amma sai suka yi wa ayar tawili na son zuciyar su.

Shin wai idan wadanda ba musulmi ba an hana su karanta Al-Kur-ani sa?annan su kuma musulmi ba za su iya fahimtar sa ba, shin waye Al-Kur?ani zai yi wa amfani? Shin akwai wata rana da wadannan mutane  za su riki Al-Kur?ani su nazarce shi da kyau? Ya zama abokin tafiya mai shiryawa a rayuwar su, maimakon karanta shi don neman lada kawai? Eeh addinan da mutane suka kago, kishin kasa da mutum-mutumin da akn sassaka su ne GUMAKAN YAU. Gumakan da Annabi Ibrahim (AS) ya kakkarya, irin su ne kuma Annabi Muhammad (SAW) ya fitar da ga Makka. Annabi Muhammad ba da wadannan duwatsun ko iccen da aka sassaka yake yaki ba! Dukkanin annabawa ?Ibrahim da Muhammad (SAW) suna yaki ne da bautatarwa ta tunani (wato a kadandane tunanin ka a hana ka fahimtar gaskiya) suna yaki ne da wadannan iyayen gijin da suka rabe da gumaka ?yan siyasar yau.

Shin mecece Najeriya da har mutum zai yi mata alkawarin zai kare ta da dukkanin karfinsa, zai kuma mutu saboda ita? Shin wannan kasa da ake kira Nijeriya ta san yadda aka halicci mutum? Shin ina mutum ya bar Allah har da zai zauna yana hidimar rudin wasu mutane?

Ka sani cewa wadannan mutane ne da suka yi tawaye ga Allah da ya halicce su ya raya su, yan tawaye ne da suka kangarewa tsarin dabiar da aka gina su akan ta (imani da Allah). Sune suke da alhakin duk fasadin da ke faruwa a doron kasa babu abin da zai hana su su bautatar da kai. Ba sa kimanta martabar ka ta Dan-Adam. Shin wanene yake a shirye ya zama musulmi? Wannan shine Danuwana ko Yaruwata; wadannan sune kadai masoyana a doron kasa. Lallai ne wadanda suka ce ?ubangijin mu Allah ne? sa?annan suka daidaita, to, babu wani tsoro akansu, kuma baza suyi bakin ciki ba? 46 aya ta 13.

A zaman mujtama?a na musulmi ba karfi ke iko ba sai dai gaskiya, mujtama?a ta musulmi muamalace tsakanin sarki da sarauniya (wato mu?amalace mai yanci cikakke). Allah shine makoman mu, makiyan Allah basu da makoma kuma basu da manufa ta gari don haka baza su iya shiryar da kai ba.

Kuzo mu hada karfi mu binciki inda gaskiya take, muyi aiki da ita, zukatanmu na da yabanya kyakkyawa, ko dai mu dasa alheri a cikinta ko kuma shaidanun yan siyasa suyi mana mugun dashe.

Don neman Karin bayani ko bukatar kwafin littafin nan mai suna THIS IS AL-ISLAM kyauta ta hanyar sadarwa ta e-mail (yanar gizo-gizo) dina, ko kuma idan kana bukatar mallakar ainihin littafin sai ka name ni.

Nine IDRIS ALI, kana iya nema na ta hanyar e-mail:idrisomeiza@yahoo.com ko ta hanyar waya 0805-3140923.

Mai fassara Turanci zuwa Hausa: UMAR ADAM AHMAD, e-mail:dattijo100@yahoo.com, 0802-3606521.
Do not oppress and do not allow yourself to be oppressed