Yandaba!

Started by Firdausi, December 28, 2001, 12:56:57 AM

Previous topic - Next topic

0 Members and 1 Guest are viewing this topic.

Firdausi

Salama Alaikum!
Yaya shaanin yandaba a Kano?
Nakeji a BBC chewa da sallar nan sunshiga gidaje sunyi kashe kashe a unguwar kufar mazugal, koki, etc. ?to haryanzu akwai wadannan mugayen mutane a kano? kuma mai hukuma ta tanada akansu? > ? ? :(
Dafatan Allah yakawo zaman lafiya a kano da duniya
baki daya.

Anonymous

Assalamu Alaikum Warahmatullahi wa Barakatuhu

Malama Asmau

Bayan gaisuwa irin ta Musulunchi inai miki barka da Sallah Allah ya maimaita mana Ameen.
Bayan haka matsalar Yandaba matsalche mai bantakaichi wache take nuna rashin chigaban Al'ummah kuma bazata kareba sai an hada kai baki daya Hukuma da mutanan Gari baki daya Hukuma kadai ba zata iya ba haka kuma mutanan Gari ba zasu iyaba su kadai sabo da haka muna bukatar bawa wannan matsala muhimmanchi baki dayanmu dan mu tsira da mutunchin mu da Rayukan mu da lafiyar mu baki daya kihuta lafiya

Dan uwanki a Musulunchi
Amin S. Khalid

Anonymous

? ?Assalamu alaikum, da fatan munyi bikin Sallah lafiya ameen, lallai matsalar YAN DABA wata babbar matsala ce da ya kamata abata kulawa ta musamman daga bangaren hukuma haka daga bangaren jama,a baki daya, domin bai kamata ace lokacin da wasu al,umman duniya suke tunanin harba tauraron dan adam ace har izuwa wannan lokaci jama,ar Kano sun sake wannan lamari yana ci masu tuwo a kwarya ba, ?ya kamata hukuma ta dauki babban mataki wajen magance wannan lamari domin an taba samun lokacinda hatta su yan daba suna tsoron anunasu cewa yan daba ne, ballantana ace wai gasu sun bayyana awata unguwa suna zubar da jini, kuma wai alokacinda hukuma ta sanya hannu akan tabbatar da shari,ar muslumci a Kano, to lallai abin da ban mamaki, shin wai shari,ar da gaske akeyi kuwa? Wassalamu alaikum, dan uwanku , Abubakar M.Abdullahi.

Anonymous

Salamu alaikum,

Shin, su wanene waennan mutane? ?su kamar area boys ne? ?Me yasa suka zama haka? ?Yakamata ayi wata forum, dasu da mutane da gwamnati, a sam meyasa sukeyi abubuwanda sukeye, ko rashin aiki, ko rashin ilmi etc.

wassalam
a bukar
Quote
Salama Alaikum!
Yaya shaanin yandaba a Kano?
Nakeji a BBC chewa da sallar nan sunshiga gidaje sunyi kashe kashe a unguwar kufar mazugal, koki, etc. ?to haryanzu akwai wadannan mugayen mutane a kano? kuma mai hukuma ta tanada akansu? > ? ? :(
Dafatan Allah yakawo zaman lafiya a kano da duniya
baki daya.


Anonymous

Game da 'Yan-daba.

Assalam Alaikum 'yan'uwa.

Da farko dai godiya ga wad'anda suka k'ik'oro wannan fili mai ban sha'awa da amfani. Allah ya saka maku, amin. :-[

A gaskiya b'ullowar 'yan daba da ire-irensu, babbar matsala ce ta al'umma. Amma nauyin ya fi ga shugabanni, musammam ma masu tafiyar da gwamnati.

Idan ka d'au kowanne titi a cikin birnin Kani, misali, za ka ga kafin ka ci rabin kilomita, ka yi kacib'is da yara -daga 'yan shekaru 5 zuwa 25- suna wasan banza a kan titi, ko suna bara, ko suna karta, ko suna k'wado. Wannan kuwa, ko da a ranakun aiki ne. Watau dai, ba sa zuwa makaranta, kuma ba wanda yake zancensu, ballanatana k'ok'arin yin wani abu a kai.

A wannan gari mai tarihi da arziki a da, muna da Sarki, muna da Gwamna, muna da manyan masu kud'i da sauran masu ilmi. Amma, kaico! Kowa ya zuba ido, sai sha'aninsa yake yi.

Irin wad'annan yara, wad'anda wasu ba su damu da su ba, domin ba 'ya'yansu ba ne, su ne suke zama 'yan daba, domin ba su da aikin yi; yawanci kuma ba su da yadda za su yi. A k'asa wadda yanzu talauci ya fara kaka-gida, me kuke zato?

Wallahi,kad'an kenan, idan ba a tashi tsaye an yi wani abu wanda zai ja hankulansu ga makaranta ko wata sana'a ba.

Ban san dukkanin amsoshin ba. Amma na san idan aka had'a tunani, za a iya samo maslaha.

Don haka, nake kiran shugabannin, musammam ma Sarkin kano da Sarakunan Jigawa da Gwamnoni, su had'u a wani guri su tattauna wannan matsala cikin gaggawa, su san ta yi.

Wassalam.

baby

salamu alaykum

gaskiya nima naji wannan labarin game da yandaba
ya kamata asan abun da za'ayi game da yandaba
sabboda kullum hankalin mu a tashe yake saboda anytime gari ya rikice,to sun samu damar pashi da makami
na gode se anjima.
mashallhu
ee jee

Ibro2g

Assalamu Alaikum...
    Kamar yadda Mallam Khalid yace; Maganar tafi karfin humuma ita kadai kuma haka tafi karfin mutane kadan su. Dole duka a taru a hada kai, da hukuma da mutanen. Idan aka diba, ta haka ne kadai za a iya gyaran wannan Al-amari da sauran Al-amura na Kasar mu gabaki daya. Allah ya taimaka mana, kuma Allah ya taimaka ma federal republic of Nigeria, Ameen.
Safety and Peace

Guduma

Assalam, 'yan uwa.
Na dade ina nazari kan taaddar da 'yan daba ke tafkawa kan jamaa a can kano. Kuma abin takaici shine, wai basa huce hushinsu sai akan 'yan uwansu musulmi. Kash! Allah wadai! Ni dai wallahi a ganina, ya kamata dattawa da masu hannu da shuni su yi zama na musammam dan a tatafka muhawar sosai akan wannan matsala, kuma a dauki mataki kwakwkwara akanshi. Abin kunya ne ace wai musulmi da suke ,yanuwan juna suna farwa juna da kisa, Allah SWT ya sa mu gane. Kowa na gani ga can wassu wajaje ana ta yi wa musulmi kisan gilla, ba mai taimakawa, to mai yasa su 'yandaba baza su je can su taimaki 'yanuwa ba? Sai kawai su baje karfinsu akan wadanda basu ci ba, basu sha ba?

Garba_serkik

whats da fuckin point i thought this is meant to be an overall site ..i mean i love this site cos i just came acrosss it and i thought it for everyone i DONT UNDERSTAND WHY A GROUP OF U THINK U CAN EXPRESS URSELF FULLY WHEN U TYPE IN UR LANGUAGE I MEAN DONT GET ME WRONG BUT I AM HALF HAUSA BUT I DIDNT UNDERSTAND THE LANGUAGE WHEN I WAS IN KANO OR EVEN NOW SO...EVERY SINGLE WORD U SAID IN THIS TOPIC I HAVE NO BLOODY IDEA OF :P

yo malla salisu i know u are very responsible sort this people out and tell them TO FIX UP LOOK SHARP!!! ;D 8)
t nice to be important but more important to be nice ;)

Garba_serkik

whats da fuckin point i thought this is meant to be an overall site ..i mean i love this site cos i just came acrosss it and i thought it for everyone i DONT UNDERSTAND WHY A GROUP OF U THINK U CAN EXPRESS URSELF FULLY WHEN U TYPE IN UR LANGUAGE I MEAN DONT GET ME WRONG BUT I AM HALF HAUSA BUT I DIDNT UNDERSTAND THE LANGUAGE WHEN I WAS IN KANO OR EVEN NOW SO...EVERY SINGLE WORD U SAID IN THIS TOPIC I HAVE NO BLOODY IDEA OF :P

yo malla salisu i know u are very responsible sort this people out and tell them TO FIX UP LOOK SHARP!!! ;D 8)
t nice to be important but more important to be nice ;)

ajingi

Haba Baturen London,

;D ;D ;D ;D ;D ;D, . On posting anything in hausa language does n't mean that we are betraying your confidence on this site. We are just menifesting the majesty, decorum and daring of our language and culture. Okay!! take care................
I object to violence because when it appears to do good, the good is only temporary; the evil it does is permanent.

isyus

Ai Asma'u yan'daba kadarar hukuma ne.
ne day one young cantact me in my office in order to ask me something about the last lecture i deliver in hall,. what are you expected/

Muhsin

Quote from: "isyus"Ai Asma'u yan'daba kadarar hukuma ne.
How did the become so my dear?
I'm a bit confused
Get to know [and remember] Allah in prosperity & He will know  [and remember] you in adversity.