SHIN INA MA'ANAR MATSAYIN KANO NA CIBIYAR CINIKI?

Started by Babangoro, January 19, 2004, 09:47:46 PM

Previous topic - Next topic

0 Members and 2 Guests are viewing this topic.

Babangoro

:'(
Mutumin Kano yana alfaharin wannan matsayi na birninsa, wato Centre of Commerce, ko kuma Cibiyar Ciniki. Sai dai kash! Har yanzu mun kasa tsayawa mu duba alfanun wannan matsayi na Kano ga al'ummar Kanon.
A hankali a hankali dai wadansu sai tsallakowa suke yi daga wadansu wurare suna mamaye wannan sana'a ta kasuwanci, (musammman ma cinikin), su kuma 'yan Kanon ana turesu gefe. Kai ba ma saye da sayarwa na kasuwanni ba, hatta sana'a ta fara sullubewa daga hannunmu. (Ka je mayankar kano ka ga abin mamaki!). Ina mafita?

Anonymous

A gaskiya akwai bukatar duba wannan matsayi na Kano na Cibiyar Ciniki. Babu makawa, Kano tana nan da matsayinta na Cibiyar Ciniki, saidai kash! Akasarin mutanen Kano basa cin moriyar wannan matsayi, domin bakin haure duk sun mamaye maikon. Misali, idan kaje kanti Kwari, zaka ga mutum a zaune a gaban kanti yana muzurai, amma duk barazana ce kawai, idan ka bincika sai kaga jarin na wani ne wanda ya tsallako kogin kuwara, saboda haka ribar wani wuri zata tafi. Me yake hana manyan 'yan kasuwarmu tallafawa na kasansu domin a gudu tare a tsira tare? Allah ya kyauta.

Anonymous

aikin ke nen mu `yan arewa! mai ya hana mu tsalake kogin da ke kwara? daman chen ai larabawa ne masu shagunonin da kuke misali da su! ba ma `yan nijiriya banne.  Sha`a nin abubuwa yanda suke yanzu a kano da yawancin sawran arewa komai baya a komawa wato sha`anin adini ya kori masu hali duk sun koma abuja da sawran wuraren da za su iya chinikin su babu damuwan adini domin sunfe riba a wajajen nan.  Kano a da kafin sha`anin adini ta shiga zaman jama`a wato lokacin da kano taye sunar ta kenan! Yanzu samari da `yan mata da su ka sami illimi duk barin kano sukeyi suje wasu wuraren kamar lagos da abuja. Mayan campononi da masu kudi ba su zuwa arewa kuma balle kano! Ba wanda zai sa kudin sa inda babu kwanchiyar hankali don adini