SABUWAR JAMI'A A JIGAWA

Started by Anonymous, January 15, 2002, 10:37:44 PM

Previous topic - Next topic

0 Members and 1 Guest are viewing this topic.

Anonymous

Na karanta cewa Jihar Jigawa ta kafa kwamiti da zai duba yiwuwar kafa Jami'ar Fasahar Bayanai (University of Information Technology) Sai nake tunanin cewa anya kuwa wannan shi ne abin da ya kamata a yi a Jigawa? Don me ba za kafa Jami'ar Aikin Gona ba ko ta Lafiya? Ni dai a ganina kenan. Me kuka gani? ???

Anonymous

Salamu Alaikum!  
 E to, ila dai a kiyin komai.Amma ni a gani na rayuwa ba yar kaifi daya bace, saboda haka duk wandannan fannonin da kake zance ana da bukatar su.In yayi ta Information din ma laba' asa. Gaba kuma sai a yi ta Agric din ko kuma maka mancin haka ;D


Anonymous

[/color

    Hakika maganar usman daidaice domin kuwa ba wata jamia da bama bukata ajihar tamu, domin ni ina ganin har bangaren larabcima. :-/

Anonymous

Mutanen Jigawa ashe kuna nan! Ni kuwa a ganina ban ki a yi Jami'a a Jigawa ba, abu ne da muke bukata matuka, to amma kun san cewa kudaden da za kashe wurin tafiyar da irin Jami'ar da Turaki ke so a yi ai da yawa ku kuma lura da maganar ci-gaba da gudanar da ita bayn baya kan gadon mulki. Sannan kuma ku duba bukatun Jihar Jigawa, amma kuma in so ake yi ta zama wata cibiya ta Bayanai a Nijeriya to sai in ce ya yi dai-dai. Allah dai ya yi mana zabi mafi alheri.
Amma kafin a kafa Jami'a ku daure a sami waya da internet connection masu rai a Jigawa. Na san an sawo kayan aiki na miliyoyin naira, amma ba na jin cewa an aiwatar da wani a u da su. Kila suna can a jibge a ministry.
Bissalam ;D

Anonymous

? ? Assalamu alaikum.
? ?Batun kafa jami,a a karamar jiha kamar jigawa ina ganin ba shine abin da ya kamata a bashi muhimmanci ba a halin yanzu a cikin wannan matashiyar jiha, ya na da kyau ace an baiwa ilimin pri. da karama da babbar secondry matukar muhimmanci wajen ganin an ingantasu , ta fuskar wadatasu da muhimman kayan aiki da isassun malamai wadanda suka san makamar aiki.
? Gudanar da jami,a abune mai matukar jan kudi sannan gashi ita wannan jiha batada wasu gagaruman hanyoyin shigowar kudi baicin kason gwamnatin tarayya.
? Ina rokon Allah da ya daukaki al,ummar AREWA baki daya.
? ? ?Wassalamu alaikum,
? ? ?Abubakar ?Magaji Abdullahi. Riyadh.

Anonymous

 Haba ,yan uwa ina so ku runka tunani fa cewa shi kudin da gwamnati ke badawa ba tana bada shi ba domin wani yasasu a aljihu ya cinyaba, saidai ana bada sune don ayiwa jaha da alumma aiki, amma maganar ace ayi wani aiki abar wani aiki bai tasoba domin (abari ya huce shike kawo rabon wani).

  Naku Umar Shitu Babura L.G.A. Jigawa

Anonymous

Assalamu alaikum yan uwa:

Ilimin zamani, musamman irin wanda Gwamna Turaki yake ta surutu akai, abin bukata ne a Nigeria baki daya bama Jigawa kadai ba. Babbar matsalar itace su masu zancen bada irin wannan ilimi basu fahimce shi sosai ba kuma bana jin akwai gaskiya a cikin zancen nasu.

Idan Gwamnatin Jigawa ta inganta makarantun da take da su yanzu (a Kazaure, Gumel da Dutse) sukansu zasu iya ba wannan jiha irin ma'aikatan (technology, agriculture etc) da gwamnati da kamfanoni zasu bukata. A yanzu haka, gwamnatin Jigawa ta nemi jami'ar ATBU, Bauchi da ta taimaka mata wajen fara jami'a a jihar.

Allah yasa wannan "investment" din na gaskiya ne.

Anonymous

Mustapha na sanka da son rubuce rubuce to ga dama ta samu, ina fata zaka tofa albakacin bakinka
ka huta lafiya ameen.

Magaji.