Hasashen sakamakon zaben gobe da abinda zai biyo bayansa:

Started by Abu-Fatima, April 15, 2011, 03:18:33 PM

Previous topic - Next topic

0 Members and 1 Guest are viewing this topic.

Abu-Fatima

(a) Gobe PDP zata lika jam'iyyar CPC, ACN da duk sauran jam'iyyun adawa da kasa, saboda taurin kai, sonrai da rashin kishin talakawa yahanasu hada kai. (b) Faduwar CPC a gobe zai hana jama'a fitowa zaben 26 ga wata, saboda kusan duk 'yan CPC suna CPC ne saboda Buhari, don haka bazasu fito zabeba bayan gwaninsu yasha kaye. (c) Kin fitowar jama'a zaben 26 ga wata, zaisa 'yan takarar CPC susha kasa, PDP tayi galaba. Gwamnoni irin su Ibrahim Shema zasu tsallake! (e) Bayan an kafa gwamnati, tsirarun 'yan CPC da suka ci zaben majalisun tarayya a makon jiya, zasu sake sheka su koma PDP: dama akasarinsu tsoffin 'yan PDP ne. (f) 2015 in Allah Yakaimu, lokaci Buhari yabar siyasa sai kuma muga abinda Allah zaiyi.

bakangizo


admin

Allah ya banu zama lafiya.
To Amma a halin yanzu Kano ta kama da wuta ko ina sai kone kone, har da kashe kashe....

Mun samu labarin rashin zaman lafiya a Zariya, Kaduna, Gombe, Minna da kuma wasu ruraren...
Kaini Kano ko a buhun barkono!!!

Abu-Fatima

Hakane. Abinda hasashenmu bai hangoba shine cewa samari da matasa zasuyi bore bayan sun fara jin sakamakon zaben. Abin takaici kuma shine hasashena na biyu dana uku sun kama hanyar tabbata, domin labari ya ishemu cewa a wurare da dama wasu 'yan uwa sun fara bankawa katin zabensu wuta saboda wauta. Wanda ya kone katin zabensa ai tamkar ya burmawa cikinsa wukane kana ya daga hannu sama yana kirari.