KanoOnline Online Forum
May 22, 2012, 11:58:43 PM
1 Hour
1 Day
1 Week
1 Month
Forever
Login with username, password and session length
News
: Please check your user profile to make sure you have the correct e-mail address. Thanks...
Home
Help
Search
Calendar
Articles
Downloads
Gallery
Login
Register
KanoOnline Online Forum
>
Forum
>
General
>
General Board
>
Goodluck ya amince da Jega a matsayin shugaban INEC
Pages: [
1
]
Go Down
« previous
next »
Print
Author
Topic: Goodluck ya amince da Jega a matsayin shugaban INEC (Read 726 times)
0 Members and 2 Guests are viewing this topic.
bamalli
Super Member
Offline
Gender:
Location: Port Harcourt,Rivers State
Posts: 1300
“and do not throw yourselves into destruction” .
Goodluck ya amince da Jega a matsayin shugaban INEC
«
on:
June 09, 2010, 12:38:17 PM »
Goodluck ya amince da Jega a matsayin shugaban INEC
Attahiru Jega ya dade yana gwagwar maya a fannoni da dama a Najeriya
Majalisar kasa a Najeriya ta amince da bukatar shugaban kasa Goodluck Jonathan na nadin Farfesa Attahiru Jega a matsayin sabon shugaban Hukumar Zaben kasar.
Hakan dai zai baiwa shugaban damar nada Farfesa Jega a matsayin sabon shugaban hukumar zabe ta kasar.
Majalisar wacce ta hada da tsaffin shugabannin kasar da gwamnoni masu ci da shugabannin majalisar dokoki ta kasa, sun amince da nadin nasa ne bayan wani taro da suka gudanar a fadar gwamnatin kasar da ke Abuja.
Duka tsaffin shugabannin kasar ne dai suka halacci taron majalisar.
Wakilin BBC Ibrahim Isa, yace mai yiwuwa wannan nadin ya kwantarwa da 'yan kasar hankali, ganin irin kyawun zaton da ake yiwa Attahiru Jega, wajen aiwatar da gaskiya.
Sai dai acewar Janar Muhammadu Buhari na jam'iyyar CPC, har yanzu akwai sauran aiki a gaban 'yan kasar, wajen fitowa domin yin rijista da kuma kare kuri'unsu.
A yanzu dai ya ragewa majalisar dattawan kasar ta amince da nadin nasa, sannan a rantsar da shi domin fara aiki.
Dama dai anta rade-radin cewa za a baiwa Malam Jega wannan matsayi a kafafen yada labarai na kasar.
Farfesa Jega
Farfesa Jega dai shi ne shugaban Jami'ar Bayero da ke Kano, wanda kuma masu sharhi ke kallon ya taka rawa sosai wajen farfado da jami'ar.
Ya kuma taba zamowa shugaban kungiyar malaman jami'o'in kasar wato ASUU.
Yana daya daga cikin 'yan kwamitin mai shari'a Lawal Uwaisu, wanda ya gabatar da gyra-gyaren da za a yiwa tsarin mulkin kasar.
Ya yi karatu a jami'ar Ahamadu Bello University, sannan yaje Amurka, inda ya samu digiri na biyu da na uku.
Ya kuma shugabanci sashin kimiyyar siyasa na jami'ar Bayero da ke Kano.
A watan Oktoba mai zuwa new ake saran wa'adin sa zai kare kan shugabancin jami'ar ta Bayero.
Kalubale
A kwai dai babban kalubale a gaban sabon shugaban hukumar da ake saran nadawa.
Ganin irin matsalolin da suke tattare da harkar zabe a kasar.
Abaya dai anzargi jami'an hukumar zaben kasar, da gazawa wajen shirya zabuka masu inganci a kasar.
A shekara ta 2007, kasashen duniya sun yi Allah wadai da kasar, bayan da ta gudanar da zaben bayyana a matsayin mafi muni a tarihi tun da kasar ta samu 'yan cin kai.
A yanzu ya rage kasa da shekara guda ne kawai kafin 'yan kasar su koma rumfunan kada kuri'a domin zaben kasa baki daya.
Kuma alamu na nuna cewa zaben zai zamo daya daga cikin mafiya mahimmanci a tarihin kasar.
Wasu na ganin damace a gareshi ta aiwatar da shawarwarin da suka gabatar a kwamitin mai shari'a Lawal Uwaisu.
Logged
Pages: [
1
]
Go Up
Print
« previous
next »
Jump to:
Please select a destination:
-----------------------------
Forum Stuff
-----------------------------
=> Welcome to the Online Forum
=> Guestbook & Feedback
-----------------------------
General
-----------------------------
=> General Board
=> From News Sources
=> Islam
=> Business and Commerce
=> Health Matters
=> Security Matters
=> Science and Technology
=> Hausa Music and Poetry (Kade-Kade da Wake-Wake)
=> Announcements
=> Education
=> Sports
=> History
=> Culture
-----------------------------
Member Showcase
-----------------------------
=> Literature
=> PHOTO GALLERY
=> Member Poetry
=> Cooking Forum
=> AUTOMOTIVE
=> chit-chat
Subject
Started by
Replies
Views
Last post
Nigeria 1988 population was false.. He is data to prove it.
«
1
2
...
7
8
»
Anonymous
105
38211
May 03, 2005, 04:24:56 PM
by
mrguest
OF OIL SUBSIDY REMOVAL, JONATHAN, LAMIDO AND THE COLLAPSE OF NIG. ECONOMY(2)
Nuruddeen
0
412
January 10, 2012, 07:02:47 AM
by
Nuruddeen
TMC PRESS RELEASE/The Muslim Congress (TMC)
bamalli
0
387
July 22, 2011, 06:54:53 PM
by
bamalli
AREWA A IDON KASA DA DUNIYA - Arewa in National and World Perspectives
«
1
2
»
Tukurtukur
24
7253
September 28, 2010, 10:36:11 PM
by
Tukurtukur
The Fulani boy who became President
bamalli
0
467
May 07, 2010, 05:30:32 PM
by
bamalli
Powered by
EzPortal
Loading...