Goga mai bakin taba romo! Kai ashe dai akwai masu kwadayi da yawa nan. Goga, ko ka taba cin burodi da kwakwa? Wayyo dadi! Ai kana taunawa wallahi sai ka ji wani dan mai mai na fita kana hadiya ba ko shan ruwa! Dan Allah ka gwada ka bani labari.....
Husna, da alaman kina san yaji sosai. To, sai ki sami dan yajin ki hada da mangyada da dan gishiri daidai. Sai ki sami kosai, ko takalallabi, ki dinga dangwala kina ci! Har kunnenki sai ya motsa ba baki kawai ba!....