Tada Ganuwar Birnin Kano

Started by Anonymous, September 14, 2001, 02:53:01 PM

Previous topic - Next topic

0 Members and 2 Guests are viewing this topic.

Anonymous

Ina ganin lokaci ya yi da mutanen Kano za su lura da cewa wani muhimmim bangare na tarihinsu da kuma diyaucinsu na rugujewa a hankali.

Ganuwar birnin Kano na daya daga cikin manyan abeban tarihi na wayewar kan Bahaushe, amma ga alama mun yi watsi da ita muna ganin a idanuwan mu tana rugujewa.

Shin ba abin kunya ba ne a ce Turawa da suka ci Kano ba su rusheta ba, amma gata tana faduwa a gaban mu.

Kanawa lokaci ya yi da za ku sake yin sabon tunani akan makomar ganuwar birnin Kano.

In aneman ra'ayin jma'a!

Daga
Yusuf Adamu a Birmingham, Alabama.

sdanyaro

It seems to me that people have not taken the importance of what the Kano Ganuwa had offered to the actual survival of Kano city - state as we know it now seriously. How else could you explain the way that this important monument is being treated now? Yusuf, you are right, we should start a drive for Ganuwar Kano to be restored.

Anonymous

Hakika ashe ba ni ka dai bane ,Wallahi duk lokacin da na je kano idan nabi hanyar B.U.K SAI in ji hawaye yana zubar min.
Domin ba faduwa ganuwa take ba kawai mugayen mutane maras sa ci gaban kano sun fara rushe ganuwa suna gina gidaje, tare da collaboration din marasa kishin dake basu filayen HAKIKA YA KAMATA MUYI WANI ABU.
Shin meya dace muyi?.

Anonymous

?Assalamu alaikum , hakika batun ganuwar Kano wata babbar magana ce da ya kamata al,umma su bata kulawa ta musamman , musamman gnin yadda wasu shafaffu da mai suka mayarda Ganuwar Kano filayen gini, shin wai babu wata hukuma mai alhakin kula da ita wannan babbar cibiyar tarihin Kanawa? ? Wassalamu alaikum.

Anonymous

Lallai muna da dan dama,  na dade abin nan yana sosa min rai ta kai ga har na taba zuwa na gana da skataren History and culture na jihar Kano tun kimanin shekaru goma sha biyar da suka wuce akan maganar rushe ganuwa.  Ya kama mu dauki wani mataki ta hanyar nuna damuwarmu ga hukuma da wayar da kan mutane akan muhimmacin wuraren tarihi irin ganuwa da sauransu.

Fadala itace kawai wani abu na tarihi da ya rage wannda kowa ke iya gani zahiri ya kaddara irin ci gaban da mutan Kano suka yi a da can baya a tarihi.  

Isma'eel Na'iya