Murnar cika shakaru shida (6) da zuwan GSM: Me muka amfana?

Started by Dan-Borno, August 24, 2007, 11:55:45 AM

Previous topic - Next topic

0 Members and 1 Guest are viewing this topic.

Dan-Borno

Wannan wata ta Agusta da muke ciki, ita ce watar da
aka shigo da wayar sadarwa ta hannu zuwa wannan
kasarmu mai albarka - Nigeria.  Abin mamaki, yau kimanin
shekaru shida (6) kenan da zuwan wannan na'ura, kowane
birni da kauyuka in kaje, baza ka rasa wata kamfani
ta sadarwa ba.

Kamar yadda komai yake tattare da nasa alkhairi ko
sharri, haka shima wannan na'ura ta sadarwa ke da ita.
A watan Agusta 2001, Nigeria tana da layuka ta sadarwa
kimanin 450,000, amma a yanzu muna da layuka ta
sadarwa kusan kimanin 38 million.

Har ila yau, a shekara ta 2001, kamfanunka na sadarwa
suna da kimanin kudi da dukiya wuri na gugan wuri dalar
Amurka miliyan hamsin $50m amma a yanzu ta bunkasa
ta hayayyafa ta kuma samu karin kudi da jari kimanin
biliyan tara da digo biyar dalar amurka $9.5 billion.  Wannan
tashin gwabron zabin ya nuna cewa a duk fadin Afrika
Najeriya ita ce ja gaba wajen kasuwan GSM, kuma hatta
a cikin kasashe masu tasowa ta chilla bisa kowa.

A gaskiya, idan muka duba baya kafin zuwan wannan
na'urar GSM, zamu fahimci cewa mun samu biyan bukatu
kwarai da gaske, duk da cewa duniya ta shaida cewa
kamfonin sadarwa da ke najeriya sune mafiya ci baya
wajen bada kyakkyawar hanyar sadarwa.

Har ila yau, idan muka duba dimbin samaruka da yan'mata
masu tasowa suka samu aikin yi, imma ta hanyar samun
aiki a kamfanoni sadarwa ko kuma ta hanyar sayar da kati
ko kuma "tele center".  Hakika zamu rungumi zuwan GSM
zuwa najeriya, domin ta tallafa kwarai da gaske.  Har ila yau
munga karin yunkurowan kananan kamfanoni wadanda suke
matsayin "dillalai" wa kamfanin GSM din, kwarai da gaske
zuwan GSM ta kawo alkhairai da dama.

Shin zuwan GSM najeriya ko rashin zuwan ta, wacce ce tafi
amfano ga jama'an najeriya, tare da la'akari da mummunar
service da kuma tsadar kudi?

To jama'a, ina fatan zaku yi hakuri da irin hausar D-B.
"My mama always used to tell me: 'If you can't find somethin' to live for, you best find somethin' to die for" - Tupak

HUSNAA

DB this is sooooooooooooo booooooooooooooooooooooooooring.........yawn...
Ghafurallahi lana wa lakum

Muhsin

Well DB, I think I will choose zuwan nata yafi alheri duk da yake ta taho da sharrori inculculable. Yet, alheran za su iya outnumbering the latter.

There is no much time to talk tall, but perhaps when back.....
Get to know [and remember] Allah in prosperity & He will know  [and remember] you in adversity.

Bajoga

To! kamar yadda Muhsin ya fadi, nima hakan ne zuwanta din yafi hamfani. Amma wani abun bakin ciki shine, as DB said above, mune the highest customer na GSM wa nahiyar Africa da wasu kasashe masu tasowa kuma at the same time mune masu poor service. Always (especially in the evening/night) in kana aiki da wayar salula sai kana yawan samun network problem, ga fadin abinda ba dai-dai ba, kana tare da mutum amma in ka kirashi ta GSM sai kaji ance "is not responding"

Gaskiya in akwai wanda yake da access da masu wayar GSM to yakamata ya sanar dasu irin matsalolin da muke fama dashi musammamma CELTEL (Sorry, na kawo celtel ne saboda shina ke amfani dashi na kuma san problems nasa, sauran sai dai inji masu shi suna fadi)

Da fatan zamu samu progress akan wannan harka.

HASBUNALLAHI............

Muhsin

Get to know [and remember] Allah in prosperity & He will know  [and remember] you in adversity.