INGARMA GIDAN TALAKA........

Started by SAAHIB 92, August 17, 2004, 06:54:24 PM

Previous topic - Next topic

0 Members and 1 Guest are viewing this topic.

SAAHIB 92

Kasancewar taron 14/8/04 na mahalarta dandalin kanoonline abin farin ciki a tare da ni, sai na ga ya zama tilas a gareni da na bayar da budaddiyar shawara ga dukkan jama'ar da suka halarci wannan zauren gami kuma da godiya ga shugabanin wannan shiri.

Shugaban taro Dr kumo gani na da shi na farko ke nan amma na sanshi farin sani a rubuce,mun ji dadin jawabinsa mai harshen damo,kuma mun tsinci abubuwa da dama,amma akwai sharhi zai biyo baya in allah ya so.

Malam ado kurawa mun gode da sanyayan kalamanka masu ma'ana.amma maganar shirin gwamnati wadda ta shafi almajirai tana bukatar kowa da kowa ya shigo cikin shirin,har iyayen da suke turo 'ya'yayansu su ma sai an hankaltar da su.

Iyayen tafiya farfesa abdallah da malam salisu danyaro zan yi abin da bana son yi( MORE GREASE TO YOUR ELBOW)allah ya saka da alheri.

amma a ganina kamar lokaci yayi,ko ya zama kamar wajibi a kara wayar da kan jama'a a kan mahimmancin a gazawa wannan tasha ta dandalin kanoonline,ba wai don kun gaza ba, a'a sai don mu kara fahimtar mahimmancin wannan dandali da kuma daukar cewa; nawa ne,na kane,na mune mu taru mu rufa masa bargon sutura ko don su waziri ma,kar su ce mun dauko kayan da ya gagaresu dauka amma muna neman a sauke mana.

Dr yusuf muna godiya da takaitaccen sharhi, gami da matukar godiya da karamin goro wanda aka ce yafi babban dutse.


Ga abokaina sababbi irin su Dr wailari,gogannaka,sadik,darma,hashim,da sauransu muna yi muku fatan komawa gida lafiya, har masu GUZURIN GIREBA DA BAKILAWA,gami da masu DAURE FUSKA, KUMA LOKACI GUDA SUNA MURMUSHI DON SUN GA BENE............zaria wiz luv.[/b]
Radina billahi Rabban,
Wa bil Islami Dinan,
Wa bi Muhammadin Nabiyya!"

 ABBAS A YAKASAI