Shawara ga gwamnan Kano

Started by Sas, November 20, 2004, 08:32:14 AM

Previous topic - Next topic

0 Members and 2 Guests are viewing this topic.

Sas

Salamu Alaikum,

A ko yaushe ban taba tunanin menene dalilin da yasa Gwamnatin tarayya ce zata bawa Jiha jiha kudin da zasu tafiyar da alamuran jahohin ba. Sau da dama sai naji ance ai Gwamnatin tarayya ce bata aiko da kudi ba saboda haka Gwamnatin jiha basu da halin gudanar da wani abu. Gaskiya a tunanin na wannan ba dai dai bane.

Kama tayayi a ce jiha kamar dai Kano yadda allah ya bamu saar cinikayya da amfanin gona mu muke daukar nauyin yawancin aiyukan cikin jihar mu ba Obasanjo ba. Dalili na anan shine, kasancear samu Mai da akai a wasu sassan kasar tamu yasa duk jikin mu yayi sanyi akan mu mu tashi muyi aiki da baiwar da Allah ya bamu mu tashi kudade daga jihar mu. Kafin a samu mai, shin akan wa muka dogara? Ji nake da kanmu muka dogara?

Ina ganin ya kamata daya daga cikin abubuwan da Shekarau ya kamata ya fara dubawa shine yayi zai samu ya tada tattalin arzikin jihar kano ya zamana bamu dogara akan Gwamnatin tarayya ba. In yaso in Man da muke ji dashi ya kare, a kalla muna da abin da zamu ci gaba da amfani da.

Bissalam,
ny good thing I said is from Allah and any bad thing I said is from me...So I ask for Allah's forgiveness for my errors both conscious and unconscious ones...Ameen!!!

gogannaka

Hakika wannan shawara ce mai kyau SAS....Problem din shine abun da za'a iya tarawa a matsayin haraji ba zai taba yin kusa da abun da ake samu daga federal govt ba. Amma dai duk da haka an ce dogaro da kai yafi dogaro da wani.
Surely after suffering comes enjoyment

Sas

Salam,

Wani abu da zamu duba muga shine:

Ina duban Nigeria ne kamar tsintsiya. Danko ne yake rike da zaborin. Mutum yana iya ciran guda da kanshi, ko dakansu suna iya faduwa kuma da zarar an warware dankon nan ko tsintsiya ta rabu kenan.

Zamu iya kallon Nigeria a halin yanzu kamar haka. Kwnakin baya ina magana da wani dan kudu yake ce min ai shi a nashi raayin shine a raba Nigeria gunduwa gunduwa shine zai kawo zaman lafiya a ssassr mu. Wannan kalamai nashi sunsa nayi tunanin ashe akwai mutane da dama da suke tunanin haka kuma bamu sani ba cewa nan gaba ko wannan raayi nasu zai yi tasiri. Yanzu idan Nigeria ta rabu (yaya gari kamar Kano zai tafiyar da alamurran sa?-- A gaskiya banga yadda zaai ba, jira muke sai hakan ta faru sannan mu yi hankali).

Manufa ta anan shine bamu san abun da zai faru ba a nan gaba ba kuma hakika akwai damar da cewa Nigeria zata iya rabuwa da babu abun da zai hana in hakan ya taso da karfi. Kuma me kano zatai in hakan ya faru?

Bissalam



ny good thing I said is from Allah and any bad thing I said is from me...So I ask for Allah's forgiveness for my errors both conscious and unconscious ones...Ameen!!!

_Waziri_

Sas,

This is a very beautiful thought process. However it shouldn't be meant for Kano State only. When Nigeria break up, the discussion will not be about Kano only but Northern Nigeria or atleast, North West.

We really have to learn to think of how we can start taking our destiny into our hands before another group of coupist like ORKAR group will come and excise a larger portion of us out of the present Nigeria. Please Sas why not write in English that you may increase your odience?

mlbash


this is a very nice post, mr. sas. i really appreciate your foresight and IN SHA ALLAH, i'll soon make a breathtaking contribution about the retrogression of our beloved state.
t is my intention to make the neglected aspect of our societies viable

SAAHIB 92

sas.

wannan magana taka akan hanya take,amma ALLAH yasa wadanda suke da hakki kan lamarin su fahimta. kuma su aiwatar. musamman ace shawarar ta karbu ga dukkan jahohin arewa.

bayan haka, rubutunka cikin harshen hausa abin birgewa ne,domin turanci ba yarenku ba ne. :idea:  kowa ya bar gida....... kuma kayan aro abin banza ne.

maassalam
Radina billahi Rabban,
Wa bil Islami Dinan,
Wa bi Muhammadin Nabiyya!"

 ABBAS A YAKASAI

Sas

Salaam,

Na gode. Ai dalilin da yasa nake rubutu da Hausa shine ni ban ga dalilin da zaisa ace wai lallai sai nayi magana da turanci sannan mutane(Hausawa) zasu fahimta. Dalili kuwa shine in kuka lura da illar da turanci yakeyi mana a kasarmu, to Wallahi kafin mu ankara sai 'ya'yanmu sun tashi ko Hausar ma basaji.

Ku lura kuga shekara kamar talatin baya ai Hausa tafi karfi akan yanzu. In na duba naga yadda 'yan Chana ko Japan, ko "Turawa" kai har ma larabawa, abun yana bani sha'awa yadda suke karantar kusan komai da harshensu. Sai kaga mutum yazo daga Chana ko turanci baya ji amma in fannin math ne ko physics ko ma aikin likita ne, wanda yake jin turancin bai yaga masa ba.

Inaga wani abu ma da Gwamnan ya kamata yayi shine ya samo hanyar da zamu karfafa Harshen mu ya zama cewa bai bata ba nan ba da dadewa ba.

Wani abun dariya shine rannan ina magana da dan uwana a "MSN Messenger" saiyace ai wai lalle sai nayi mashi rubutu da turanci. Naso ace a gabana ya fada da na...

Bissalam
ny good thing I said is from Allah and any bad thing I said is from me...So I ask for Allah's forgiveness for my errors both conscious and unconscious ones...Ameen!!!

SAAHIB 92

Sas,

assalam.

kasan an ce wai ...jiya ba yau ba.... jawabanka sun zamo kukan kurciya wanda abin takaici acikin wannan zauren namu ma ba kowa ne zai gane ba. abin da nake nufi daga mazan har matan da manya da kanana kowa wai shi bature ne, kuma turanci abin sha'awane da birgewa idan ma baka iya ba sai ka zamanto abin kwatance. wannan takaici da yawa yake.

yanzu lura da tsarin rubutun mutanen zauren ma kawai ya isheka misali, har gwanence rubutun turanci  ake yi, wasu dan gwanencewa su turancinma na bakaken amurka ake kwaikwayo, abin nasu dai agurinsu wasar da su.

abin takaici a halinn yanzu yara kanana yan makarantar nursery ba za su iya rubutawa ko karanta hausa ba,har sai an kai ruwa rana, amma wajen karanta (ali and the angel) wayyo ba'a magana. kaga  a hankali-a hankali sai a wayi gari turawa sun yaki tunaninmu da dabi'un mu kuma sun cinye yarenmu da yaki .mu kuma mun zamanto bayinsu. tir !! da wannan al'amari.

A GANINA- kamata yayi dukkanin makarantun kano da makamantan jihar kano su yaki wannan al'amari ta fuskar jawo hankalin gwamnati, da shugabanin jama'a, da su shigo cikin wani sabon shiri da ya kamata su gabatar ga dukkanin al'umma na kara farfadowa da tayar da  komadar yaren hausa. ta hanyar sanya yaren hausa ya zamanto wajibi a dukkan darussa na dalibai.
kuma a yawaita gabatar da alamuran jan hankali ga yara ta kafofin labarai da makamantansu.

kuma a dakusar,ko a sanya tsaro da sharudda akan fina-finai wadanda suke karyar cewa al'adun hausa suke wakilta ko bunkasawa. (abin bakin ciki!!) domin abin da suke nunawa ya sha banbam da tsari irin na hausawa. wannan ya kara kashe hausa ta fuskar yare ,tarbiyya gami da al'ada. don haka sai a koma aron kalmomi da dabi'u  irin na turawa da sunan wayewa......hmmm!!!  KOWA YA BAR GIDA....GIDA YA BARSHI!!!!
Radina billahi Rabban,
Wa bil Islami Dinan,
Wa bi Muhammadin Nabiyya!"

 ABBAS A YAKASAI

_Waziri_

Well, I really am the one who thought that this discourse should go in English since going by the nature of the subject of discourse more people from the other part of Nigeria or even the world will need to know that the people of Northern Nigeria are not parasites as they are being represented in most media outfits.

There is also the need for us to make others see that we too understand the probable attribute of the image shown by the future of the country called Nigeria, in which now, it seems, we are its only stauch advocates, perhaps we are the ones who get more from it. Others need to know we can hold an alternative view about Nigeria.

I only think the above make more reasons why we should discuss this in English. It is not that we hate Hausa, our lanuguage, No. I wrote my second book in Hausa some 4 years back and I am proud of the fact that Hausa is my first speaking tool, but I also believe that our objective is what should determine what we want to achieve. Mine was only a thought not a suggestion. If any writer deems it better to write in English, I certainly will have no objection whatsoever. Let people do what they like doing best. Let them be what they like being best.

SAAHIB 92

Sas,

Mu bukatar da muke da ita  kuma mu ke kira ga wadanda abin ya shafa,itace ta a kara inganta yaren na hausa ,gami da yanto shi a hannun bakaken turawa.

A NAWA HASASHEN-sai an kashe maka yare ya zamanto kai kanka kana jin kunyar yinsa ,sannan kuma sai ayi maka abin  da bakaken turawanmu suke kira wai (MORAL CONQUEST).Shin menene marabar halin da mu ke ciki a yau da jawabinnan.

shi ilmi dadi ne da shi tun bama an raba an sanwa wasu ba, ina ma (waziri) zai gutsuro mana kadan daga ckin littafin da ya rubuta da yaran HAUSA ko ma kara gasgata shi kuma mu karu, domin DA ABOKIN DAKA AKAN .....SHA GARI?
Radina billahi Rabban,
Wa bil Islami Dinan,
Wa bi Muhammadin Nabiyya!"

 ABBAS A YAKASAI

Yoruba Land

I love Hausa language and I understand it very well and would like to have it developed too.

Quoteshi ilmi dadi ne da shi tun bama an raba an sanwa wasu ba, ina ma (waziri) zai gutsuro mana kadan daga ckin littafin da ya rubuta da yaran HAUSA ko ma kara gasgata shi kuma mu karu, domin DA ABOKIN DAKA AKAN .....SHA GARI?

SAAHIB92,

Waziri is lying, he did not write any book in Hausa.

Sas

Salaam,

Da kyau ganin cewa wasu ma suna tunanin cewa lallai ya kamata ayi wani abu game da yadda yaren Hausa yake sulalewa daga bakin mutane. Manufarmu anan itace abun takaici ne duk da cewa wai ana kiran wannan zauren "KANOonline" amma ace wai yawancin mutane daga Kano bazasu iya fahimtar me ake tattaunawa ba.

Ina ganin cewa wani yana karya baiyi daidai ba sai dai in ka tabbata cewa hakkan karya yake yi, kuma duk da haka bai kamata ka karyata shi a fili ba.

Allah ya zaba mana abin da yafi alheri kuma ya daukaka harshen mu a duk fadin duniya.

Mu huta lafiya.
ny good thing I said is from Allah and any bad thing I said is from me...So I ask for Allah's forgiveness for my errors both conscious and unconscious ones...Ameen!!!

Yoruba Land

Sorry Sas please. I did not intend saying Waziri was lying. I wanted to bring out the meaning of what SAAHIB 92 was trying to say. I f he say Waziri should bring evidence of his writing in Hausa for him to be sure of what Waziri say then he meant to say Waziri was lying.

Actually I know Waziri very well and I know what he can or cannot do. But still I am sorry if anybody should find what I said harsh.

Indabawa

Quote from: "Sas"Salaam,

Da kyau ganin cewa wasu ma suna tunanin cewa lallai ya kamata ayi wani abu game da yadda yaren Hausa yake sulalewa daga bakin mutane. Manufarmu anan itace abun takaici ne duk da cewa wai ana kiran wannan zauren "KANOonline" amma ace wai yawancin mutane daga Kano bazasu iya fahimtar me ake tattaunawa ba.

Ina ganin cewa wani yana karya baiyi daidai ba sai dai in ka tabbata cewa hakkan karya yake yi, kuma duk da haka bai kamata ka karyata shi a fili ba.

Allah ya zaba mana abin da yafi alheri kuma ya daukaka harshen mu a duk fadin duniya.

Mu huta lafiya.

I think i should come in at this juncture, seeing that Waziri's aobservation is being misunderstood.I balieve the import of his suggestion was that the advice being offered by Sas and the attendant responses should not be localised.It is a well known fact that it is not only Hausa speakers that visited this site,and also to my belief, it is not the intention of the facilitators of the site to make the site exclusive.

Therefore,sharing our discussions with non Hausa speakers does not and cannot in any way dampen our profficiency in the language.Saboda haka Sas,Waziri da sauran mu,duk dai Allah ya sa kowa aniyar sa ta bishi.
e who kneels to Allah can stand up to anything.

Sas

Salaam,

Gyara anan daya da zanyi maka Indabawa shine bance lallai wai ya kamata a daina turanci kwata kwata a wannan "forum" dinba ballanta nace a rinka Hausa kawai. Manufata itace matsala ce da na gani a tare da Hausawa a yanzu da Hausar ma in ba ai sa'a ba sai ta bace daga bakin 'ya'yanmu ko jikokinmu. Wannan shine abun da Turawa suke nema kuma da alama suna kan hanyar samun nasara.

Kawai abun da nake nufi kenan. Da fatan ka fahimta! A huta lafiya.

JAK
ny good thing I said is from Allah and any bad thing I said is from me...So I ask for Allah's forgiveness for my errors both conscious and unconscious ones...Ameen!!!