Nigeria at 42, mu gode Allah!!!

Started by Bakatsine, October 01, 2002, 02:34:39 AM

Previous topic - Next topic

0 Members and 3 Guests are viewing this topic.

Bakatsine

Assalamu alaikum, A gaskia ya kamata mu gode Allah akan irin rahamomin sa da cigaban da Nigeria ta samu acikin waddan nan yan shekaru (42). Shekara 42 ba wani dogon lokaci bani acikin rayuwar kasa. Na samu damar ziyartar kasashen Africa da Asia da dama, sai naga cewa lallai muma baa baya ba, mun samu bunkasar arziki,  ilmi, kiwon lafia, hanyoyi, masanaantu, kasuwanci dadai sauran su. Zani iya tunawa da lokacin da nake tasowa farkon 1970-80, a kauyenmu (Tama KTS) ba hanyar mota, ba ruwan sha, ba wutar lantarki, ba asibiti, kurkunu yakan kayar da mutane da dama aduk shekara, mafi yawan gidajen kauyenmu na hakki ( kara) ne, ga talauci da jahilci sun dabaibaye jama'a. Amma yanzu idan na dibi kauyen mu ya chanza, mun samu wadatar ruwan sha, ansanya wutar lantarki, anyi kwalta, mafi yawan gidajen yanzu bugun kwano gare su, ga kasuwa, ga asibiti, ga sababbin ajujuwan makaranta angina, yanzu muna da mutane dama masu digiri, diploma, NCE, da dai sauransu, yanzu akwai mutanen da   suke da motocin kansu da na haya, babura da kekuna sun wadata, kai hatta injinan nika za su kai biyar. I dan na tuna da irin halin dana tashi naga kauyen mu, na dubi irin halin da yake ciki yansu, sai inyi salati in gode Allah domin rayuwar mu ta inganta a cikin wannan lokaci. Na sani Nigeria nada nata matsalolin, to wace kasa ce bata da su? ni a gani na muna kara kururuta halin da kasar take ciki, amma idan muka duba to lallai wannan shekaru 42 baa banza suka shude ba.Allah shi taimakemu ya tabbatar mana da alherin sa amin.
Sanusi Jari
Moscow Russia

sdanyaro

Malam Sanusi Jari,  
Assalamu alaikum;

Da farko muna yi maka barka da zuwa wannan zauren na Kano Online Forum.
Kuma wannan abunda ka fad'a gaskiyane. Kuma yakamata duk halin da mutum yake ciki sai ya gode wa Allah Mad'aikakin Sarki. Domin idan ka duba K'asashe da waya ba su samu cigaban da muka samuba. To sai muce Alhamdulilla - ala kullu halin.  

Godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin Sarki...

awwal

Assalamu Alaikum

Malamai lalle kan na yarda da ku kan cewa dole ne mu gode wa Allah a duk inda muke kamar ma yadda wasu suke cewa godewa Allah ya zama wajibi ko da kuwa mutum yana bakin kura ne. Kuma lalle an samu ci gaba cikin wadannan shekaru musamman idan aka yi la'akari da yadda Nigerian take a wancan lokacin kamar yadda Mal. Sunusin ya ce, to amma abin ya kamata kada mu mance da shi shi ne cewa ci gaban da muka samu cikin wadannan shekaru da za su fi haka nesa ba kusa idan da a ce shuwagabanninmu ba su ci amananmu ba suka sace mana kudade suka fita da su kasashen waje suka tara wa turawa.

Abin da ya sa nace haka shi ne kuwa, idan muka duba wasu kasashe na duniya, musamman ma ga 'yan uwa wadanda suke kasashen waje, musamman ma kasashen da ake kira kasashe masu tasowa, zai ka ga irin ci gaban da aka samu a wadannan kasashe nesa ba kusa ba ya fi na Nigeria.

A matsayin misali, a nan Iran inda nake, duk wanda ya zo ya ga yadda yanayin rayuwan al'umma yake a nan da yadda yan Nigeria suke to lalle zai tausaya mana. Nigeria mu na da arzikin da za mu iya kyautata rayuwarmu, amma saboda hadama da rashin kishin kasa na wasu shuwagabanni ya sa mutane suna cikin halin kaka ni kayi na rayuwa da dai sauransu.

Don haka ni a ra'ayi na ina ganin akwai bukatan shuwagabanni su ji tsoron Allah su kiyaye wannan amana da Allah da kuma al'umma suka ba su, idan suka yi haka lalle kan ci gabanmu zai bunkasa

Maassalam

Awwal

Nuruddeen

Bakatsine mai kan kwarya, Nigeria at 42 is still a fool. Abi?
Nuruddeen a.k.a Jibo Nura :)  :)  :)
o try and fail is atleast to learn. That will save one the inestimable loss of what might have been (positive or negative).