Author Topic: wakar janar buhari  (Read 27579 times)

0 Members and 1 Guest are viewing this topic.

Offline suleimanharuna

 • Member
 • *
 • Join Date: Jan 2007
 • Posts: 2
  • View Profile
wakar janar buhari
« on: January 08, 2007, 09:45:25 AM »
WAKAR JANAR MUHAMMADU BUHARI

Bismillahi rabbana Allah
Sai Janar Buhari
Nai niyya in wake zakina
Sai Janar Buhari
In sai dashi gun duka dangina
Sai Janar Buhari
In san da su babu kamar nawa
Sai Janar Buhari
Zaben badi kam ni nai zabi na
Sai Janar Buhari
Tabbas ni Buhari zan zaba
Sai Janar Buhari

Sai kumu tattaro mu zabeshi, don saboda ta baci sai janar ka gyarota, sai janar Buhari

Yai gwamna yayi minista fa
Sai Janar Buhari
Har yai shugaban kasa nawa
Sai Janar Buhari
Amma bai ci mana amana ba
Sai Janar Buhari
Yayi riko da gaskiya baba
Sai Janar Buhari
Duk jama’a sunata madalla
Sai Janar Buhari
Janar Buhari Allah maimaita
Sai Janar Buhari

Sai kumu tattaro mu zabeshi, don saboda ta baci sai janar ka gyarota, sai janar Buhari

Jama’a na a basu mai sonsu
Sai Janar Buhari
Buhari kam ya amsa kiransu
Sai Janar Buhari
Har yai takara fa dominsu
Sai Janar Buhari
Aka sace kuri’arsu jarinsu
Sai Janar Buhari
Aka baiwa wani can barensu
Sai Janar Buhari
Yana ta barna fa da sunansu
Sai Janar Buhari

Sai kumu tattaro mu zabeshi, don saboda ta baci sai janar ka gyarota, sai janar Buhari
Janar Buhari yai kukan zucci
Sai Janar Buhari
Yana ta begen so da aminci
Sai Janar Buhari
Da rashin ruwanmu har da abinci
Sai Janar Buhari
Balle manya babu suturci
Sai Janar Buhari
Wannan ya hana masa barci
Sai Janar Buhari
Har sai ya kwato mana ‘yanci
Sai Janar Buhari

Sai kumu tattaro mu zabeshi, don saboda ta baci sai janar ka gyarota, sai janar Buhari

Matsalolinmu sun zame luru
Sai Janar Buhari
Ga barna kamar Karen zuru
Sai Janar Buhari
Ga sata I dogarin burgu
Sai Janar Buhari
Ga wasu ma suna ta dan daru
Sai Janar Buhari
Kasarmu ta ishe cikin turu
Sai Janar Buhari
An tura mu mun ishe garu
Sai Janar Buhari

Sai kumu tattaro mu zabeshi, don saboda ta baci sai janar ka gyarota, sai janar Buhari

To dada sai muzo mu dau aniya
Sai Janar Buhari
Domin sabuwar dashen tafiya
Sai Janar Buhari
Don mun mantuwa gidan ajiya
Sai Janar Buhari
Ma jewa buhari ban gajiya
Sai Janar Buhari
Mu tuna mai yazo muna ta jira
Sai Janar Buhari
Bana kam bamu yin irin ta jiya
Sai Janar Buhari

Sai kumu tattaro mu zabeshi, don saboda ta baci sai janar ka gyarota, sai janar Buhari

Janaral sai ka zo ka cecemu
Sai Janar Buhari
Wahala ta saka mu mun dimu
Sai Janar Buhari
Bamu ganin abinda ke binmu
Sai Janar Buhari
Kokuwa wanda ma fa zai karmu
Sai Janar Buhari
Kowa na ta so ya cucemu
Sai Janar Buhari
Ba me son ya san bukatunmu
Sai Janar Buhari

Sai kumu tattaro mu zabeshi, don saboda ta baci sai janar ka gyarota, sai janar Buhari

Ina da zargin da akwai azama
Sai Janar Buhari
A kau da zaben badi kan niyya
Sai Janar Buhari
Ko kuma a kauce shirya zabenma
Sai Janar Buhari
Domin kar buhari yai nasara
Sai Janar Buhari
To wallahi bar batun wasa
Sai Janar Buhari
In ta kasance zan dau fansa
Sai Janar Buhari

Sai kumu tattaro mu zabeshi, don saboda ta baci sai janar ka gyarota, sai janar Buhari

Ya ahalin Najeriya dangi
Sai Janar Buhari
Dole muzan muna gudun kangi
Sai Janar Buhari
Ko da za mu zammuna bangi
Sai Janar Buhari
Koko muna rawar kidan gangi
Sai Janar Buhari
Tabbas yazzamo musa waigi
Sai Janar Buhari
Ko ma samu me jikin kirgi
Sai Janar Buhari

Sai kumu tattaro mu zabeshi, don saboda ta baci sai janar ka gyarota, sai janar Buhari

Ina kuke ku masu bidar suna
Sai Janar Buhari
Yadda kasan ana zuben zana
Sai Janar Buhari
To haka za mu tashi har kwana
Sai Janar Buhari
Kullum kan idonku sai yana
Sai Janar Buhari
Komai ko budewar rana
Sai Janar Buhari
Sai kun ja ciki kamar tana
Sai Janar Buhari

Sai kumu tattaro mu zabeshi, don saboda ta baci sai janar ka gyarota, sai janar Buhari

Ya dangi mu dauki butoci
Sai Janar Buhari
Mui sallah don maganin kunci
Sai Janar Buhari
Mun farka da zamanin barci
Sai Janar Buhari
Kuma mu kula mu kauce ganganci
Sai Janar Buhari
Nasara kam abarmu sai mun ci
Sai Janar Buhari
Tabbas sai mun daga tutoci
Sai Janar Buhari

Sai kumu tattaro mu zabeshi, don saboda ta baci sai janar ka gyarota, sai janar Buhari

Kasarmu ta zame cikin rami
Sai Janar Buhari
Dole mu sa kafa mu sa hannu
Sai Janar Buhari
Mu cicciba dai uwargidan tamu
Sai Janar Buhari
Mu kaita gaci da hannuwayenmu
Sai Janar Buhari
Mu fifitata don ta wayemu
Sai Janar Buhari
Ta hannun shugaba Buharinmu
Sai Janar Buhari

Sai kumu tattaro mu zabeshi, don saboda ta baci sai janar ka gyarota, sai janar Buhari

Ya Allah ka sanya alheri
Sai Janar Buhari
Zaben baba ya wuce jari
Sai Janar Buhari
Kuri’unmu bana babu mai sari
Sai Janar Buhari
Koko mutum yanzu ya sha mari
Sai Janar Buhari
Ko kuma ma ya je gidan yari
Sai Janar Buhari
Allah bbani wanga dan buri
Sai Janar Buhari

Sai kumu tattaro mu zabeshi, don saboda ta baci sai janar ka gyarota, sai janar Buhari

Don mene ake bidar mulki
Sai Janar Buhari
Don sata koko don aiki
Sai Janar Buhari
Jama’a na ta shan uban aiki
Sai Janar Buhari
Shi ko yana ta kai kudin banki
Sai Janar Buhari
Ya dinga shiga yana fitar zaki
Sai Janar Buhari
Har wataran yazan kamar gunki
Sai Janar Buhari

Sai kumu tattaro mu zabeshi, don saboda ta baci sai janar ka gyarota, sai janar Buhari

Ajiyarsa tana ta shan uban ninki
Sai Janar Buhari
Kamar waken da yai ta shan taki
Sai Janar Buhari
Muko muna habo muna miki
Sai Janar Buhari
Mun bar jaki muna bugun taiki
Sai Janar Buhari
Hakika kasarmu na jiran wanki
Sai Janar Buhari
Ko da ya zame ta gun yaki
Sai Janar Buhari

Sai kumu tattaro mu zabeshi, don saboda ta baci sai janar ka gyarota, sai janar Buhari

Ya ku masu cin amanarmu
Sai Janar Buhari
Kusan da sani muna da ranarmu
Sai Janar Buhari
Ko kun kai dila fa kwa barmu
Sai Janar Buhari
Kuri’armu tana wurin janar dinmu
Sai Janar Buhari
Shine za mu bai amanarmu
Sai Janar Buhari
Don mun san fa baya cutarmu
Sai Janar Buhari

Sai kumu tattaro mu zabeshi, don saboda ta baci sai janar ka gyarota, sai janar Buhari

To janaral sai ka zo ka dau aniya
Sai Janar Buhari
Don mun bika sai shirin tafiya
Sai Janar Buhari
Garin nasara fa ba a jin gajiya
Sai Janar Buhari
Ko da ba tuwo fa babu miya
Sai Janar Buhari
Idan Allah ya kai mu can gidan ajiya
Sai Janar Buhari
Kowa zai sha amma fa ban da giya
Sai Janar Buhari

Sai kumu tattaro mu zabeshi, don saboda ta baci sai janar ka gyarota, sai janar Buhari

Sai mai gaskiya da adalci
Sai Janar Buhari
Sai mai son a ba maza ‘yanci
Sai Janar Buhari
Sai mai son a danne ha’inci
Sai Janar Buhari
Sai mai kau da masu zalunci
Sai Janar Buhari
Sai mai rushe ‘yan munafunchi
Sai Janar Buhari
Sai sojan da ba ya makirci
Sai Janar Buhari

Sai kumu tattaro mu zabeshi, don saboda ta baci sai janar ka gyarota, sai janar Buhari

Sai  janaral uban mazajenmu
Sai Janar Buhari
Gaka fari kamar takardunmu
Sai Janar Buhari
Ga ilmi kamar sukul dinmu
Sai Janar Buhari
Ga karfi kamar hukumarmu
Sai Janar Buhari
Ga haske kama da nerarmu
Sai Janar Buhari
Ga tausai irin na kakanmu
Sai Janar Buhari

Sai kumu tattaro mu zabeshi, don saboda ta baci sai janar ka gyarota, sai janar Buhari

Na gode ubangiji jalla
Sai Janar Buhari
Kai ka tsare Buhari ba shakka
Sai Janar Buhari
Ka sanya ubanmu yai shigar sa’a
Sai Janar Buhari
Ya mulki kasarmu babu tangarda
Sai Janar Buhari
Dukkan rayuwa ta inganta
Sai Janar Buhari
Har sai ya zame gaban kowa.
Sai Janar Buhari

Sai kumu tattaro mu zabeshi, don saboda ta baci sai janar ka gyarota, sai janar Buhari

Da Allah mu tattaro mu zabeshi, don saboda ta baci sai janar ka gyarota, sai janar Buhari

Gara mu tattaro mu zabeshi, don saboda ta baci sai janar ka gyarota, sai janar BuhariMarubuci - Suleiman Haruna sulaimanharuna@yahoo.com
08037866802
Abuja - Nigeria

Offline _Waziri_

 • Sr. Member
 • ****
 • Join Date: May 2004
 • Posts: 479
  • View Profile
Re: wakar janar buhari
« Reply #1 on: January 08, 2007, 10:00:56 AM »
Wannan waka taka ta bani sha'awa kwarai. Allah yashi albarka.

Offline suleimanharuna

 • Member
 • *
 • Join Date: Jan 2007
 • Posts: 2
  • View Profile
Re: wakar janar buhari
« Reply #2 on: November 02, 2010, 04:56:13 PM »
the audio version of wakar janar buhari is on my facebook page. pls taste it.

Powered by EzPortal