2007 Election: Idan 'Yan Adawa da gaske sukeyi

Started by _Waziri_, April 24, 2007, 10:54:09 AM

Previous topic - Next topic

0 Members and 1 Guest are viewing this topic.

_Waziri_

 Ku yaya  kuke gani?

Shuwagabannin jam'iyyun adawa, da 'yan takaransu, janar Buhari, Atiku, Attahiru Bafarawa, Pat Utomi, da sauran wadanda muke kira ga talakawa, da su fito suyi zanga zanga, irin su Sanusi Lamido Sanusi. Mu mu fara fitowa da iyanlanmu da 'ya'yanmu, muyi tafiya a kasa, na kwanaki, daga Kano zuwa Abuja. A lokacin ne zamu tabbatar wa talakawan Nijeriya cewa da gaske muke yi mu kwato musu 'yancinsu kamar yadda zai tabbata idan gwamnatin Nijeriya zata iya fitowa ta harbe duk mutanen da zasu biyomu daga kauyuka da birane a kan hanyarmu ta kwato wa talaka 'yancinsa!

Ni dai naga kaman su Mahatma Ghandi na Indiya sun fimu gaskiya a kan kaunar da suke yima talakawan kasarsu!

HUSNAA

WAZIRI
ALLAH YA SHIMAKA ALBARKA.
Naji sharhim malaman da akayi a DW Hausa wanda SLS ya fito yayi zazzafar suka ga wa'yannan barayin da suke kiran kansu shugabanin mu, wato irin su Sani Uba da Kanti Bello da makaman tan su. Wai sai a ce a dake ka a hana ka kuka (wannan abin ma fyade a akayi wa 'yan nigeria ba ma dukan su a kayi ba). Wai dan Allah kada ayi tashin hankali, a hakura a karbi sakamako yadda aka same shi. Ni ina mamakin irin wa'yannan kalaman. Dama baza suso aiyi hayaniya ba mana; sun san basu da gaskiya. Kuma in har mutum baya son ayi hayaniya, ya aikata abinda zai sa a guje wa hayaniyar mana!!

Da Allah duk wanda yake da damar shiga wannan nuna rashin amince war yayi kokari ya shiga. In talaka bai tashi ya karbi yancin sa ba yanzu, to Wallahi bazai taba yi ba. Naji ma wani a rediyo yana cewa wai addua ya kamata ayi ba zanga zangar lumana ba. To wa muke so ya kwato mana 'yancin na mu, in bamu tashi munyiba? So muke Allah SWT Ya sakko da mala'iku su zo su yi mana gwagwarmayar? Muyi Addu'a Allah Ya saka mana, amma kuma mu tashi muga cewa mun kama hanyar yadda Allah Zai saka mana din, kuma haka ba za tayiwu ba in ba a tabuka komai ba.

Ina cewa da Allah Ya sakko da cewa mutane su bauta maSA, ba Annaba ne sukayi  ta gwagwarmaya ba? In Allah Ya so ai da Zai sakko da fahimtar addini   a zukatan kowa, yadda ba sai Allah Ya turo da annabawa sun zo sun fadakar da mutane ba. Saboda haka dole mu tashi muyi gwagwarmayar kwatar 'yancin mu.
Ghafurallahi lana wa lakum

Dave McEwan Hill

The rest of the world is holding its breath that Nigeria doesn't break down into anarchy after your very troublesome and doubtful elections.
I will offer no advice. Only Nigerians can sort Nigeria.

We are also having an election here in Scotland. It is the most important election in Scotland since we joined with England in 1707. If the SNP wins on Thursday Scotland will be on course to leave Britain and regain its independence.
The vast majority of Scotland's Moslem community are voting in favour of Scotland's independence and the SNP's Bashir Ahmed will probably be the first Moslem elected to the Scottish Parliament, though we have another Moslem candidate in Osama Said who is facing a more difficult task.
I have been campaigning hard for the last couple of months (and since I left school in 1959)and by next Thursday all the years may feel worthwhile.