Author Topic: Bambanci Tsakanin Mazhabar Ja’afariyya da Akidar Shi’a  (Read 11585 times)

0 Members and 1 Guest are viewing this topic.

Offline _Waziri_

 • Sr. Member
 • ****
 • Join Date: May 2004
 • Posts: 479
  • View Profile
Bambanci Tsakanin Mazhabar Ja’afariyya da Akidar Shi’a

Ga dukkan alamu akwai ‘yan Shi’a da yawa a dandalin_siyasa@yahoogroups.com wanda yasa al’amarin tattaunawa tsakanin ‘yan Shi’a da ‘yan Sunna ya ki wucewa duk da kiraye kiraye da aka rika yi da a bar tattaunar addini a dandalin. Bayan irin nawa karamin gudumuwar da na bada na shawarwari game da inda za’a iya yin tattaunawar da kuma yadda za’a yi ta, na cira na yi dan tsokaci game da bambancin da ke tsakanin akidar Shi’a da mazhabar Ja’afariyya. Har’ila yau na kuma yi nuni da cewa lalle tattaunawa da suka gudana baya tsakanin masu kiran kansu ‘yan Shi’a da masu kiran kansu ‘yan Sunna, a kasar Nijeriya, sun nuna cewa duka bangarorin biyu sun yi wa abin da suke kirarin karewa ko rusawa sanin shanu ne kawai ta fuskar mukabala. Kash! Amma na lura abin da na fada bai yiwa wasu dadi ba domin wasu ‘yan Sunna sun ce ban yi masu adalci ba kamar yadda ‘yan Shi’a suka jaddada matsayinsu - ba tare da kawo wani hujjaba -  na cewa lalle Shi’a daidai take da Ja’afariyya ta kowane fanni.

A abin da mai karatu zai gani gaba na yi yinkurin tabbatar da kuren dake cikin wannan furuci da ‘yan Shi’a suke yi kuma da yardar Ubangiji(swt) zai fahimci lalle cikin adalci ne nace ‘yan Sunna da ‘yan Shi’a da suka rika tattaunawa a baya kamar su marigayi Sheik Ja’afar Adam Mahmud da Sheik Auwal Tal’udiy basu da kyakkyawar fahimtar abin da suke kirarin karewa ko korewa. Kafinnan ina so mai karatu ya fahimci cewa wannan mas’ala ni ban dauke ta wata abar damuwa ba don addini kowa kansa yake wa, kuma wanda ya yi don Shi, wato Allah(swt) Shi zai biya shi. A sabili da haka tattauna wa irin wannan ina yin ta ne don nishadi da wasa kwakwalwa domin yinkurin yin adalci ga  mutanen duniya na jiya da na yau, akan abin da suke tsayawa akai. Ina kokarin amfani da ilimi da ma’aunin tace bayani na hankali da tsinkaya irin wanda addinin Musulunci ya tanadar.


Imamu Ja’afar Ibn Muhammad, As Sadiq da Mazhaba Ja’afariyya


Shi dai Imamu Ja’afaru Ibn Muhammad As Sadiq wanda ake kira Abu Abdalla, ya rayu a tsakankanin shekarun 83 Bayan Hijira zuwa 148 Bayan Hijira ne. Da ne ga Imamu Muhammad Ibn Aliyu Zainul Abidina. Zainul Abidina da ne ga Hussaini Ibn Aliyu Ibn Abi Talib (RA).  Imamu Ja’afar Jika ne na manzon Allah (SAW) ta wurin Fatima (RA) ta  bangaren mahaifinsa da kuma Sayyidina Abubakar (RA) ta bangaren mahaifiyansa don Muhammad Ibn Abubakar shi ya haifi kakansa.

Shahararren mallami ne mai ilimin fannoni da yawa wanda suka hada da Falsafa da Hisabi da Fassarar mafarki da Chemistry da Ilimin sanin halittan dan Adam da Ilimin Taurari da kuma Fiqhu. Fatawowinsa suka samar da mahangan tantance hukunce hukunce a addinin Musulunci wanda aka fi sani da Mazhaba Ja’afariyya,  kuma wasu ‘yan Shi’a zubin goma shabiyu ( Ithna ashariyya) su na ikirarin lalle wannan mazhaba daidai take da akidar su kuma shi Imamin shi ne Imamin su na shidda a cikin goma sha biyu. Ma’ana a hisabance: Shi’a (zubin goma sha biyu) = Ja’afariyya

Amma gaskiyar magana shine a ma’unin hujja za’a iya cewa sam Shi’a ba itace Ja’afariya ba kamar haka a hisabance: Shi’a (zubin goma sha biyu) <> Ja’afariyya

Dalili na farko kuwa shine Shi’a zubin goma sha biyu ( Ithna ashariyya) akida ce wadda, bayan wasu abubuwa, take jaddada addinin Musulunci ya tabbatar kuma ya kebance halifanci da shugabanci musulmi bayan wafatin manzon tsira ga Sayyidina Ali (RA) da jikokinsa guda goma sha biyu har zuwa ranar tashin kiyama.

Amma ita mazhaba Ja’afariyya mahanga ce ta tantance hukunce-hukunce na addinin musulunci wanda aka samu daga fatawowin Imamu Ja’afaru Sadiq kamar yadda Malikiyya da Hanafiyya da Shafi’iyya da Hanbaliyya suka kasance. Kuma ana iya samun mutum yayi ikirarin bin Sunna ba Shi’a ba amma kuma yana daukan fatawar Imamu Ja’afaru Sadiq ko kuma abin da mazhaba Ja’afariyya ta iya fitar wa.

Sannan har’ila yau za’a iya cewa ba tare da shakka ba cewa shi Imamu Ja’afaru Sadiq ba dan Shi’a bane zubin goma sha biyu ba. Domin babu wata hujja ko bincike bayahudiya ko banasariya ko musulma a cikin Sunna ko Shi’a da za’a iya samar wa cewa wai Imam ya kore halifanci Sayyidina Abubakar(RA) ko kuma Sayyidina Umar(RA). In kuwa akwai to zaka samu acikin bayani ne mai raunin asali sosai koda kuwa a cikin littafin Shi’a ne.

Sannan daliban Imamu Ja’afaru Sadiq ba ‘yan Shi’a bane. Hasali ma su ne mallaman Sunna kamar su, Imamu Malik wanda fatawowinsa suka samar da mazhaba Malikiyya da  Imamu Abu Hanifa wanda fatawowinsa suka samar da mazhaba Hanafiyya da kuma Sufyanussauri wanda ya kasance babban mallamin hadisi a wannan lokacin. Sa’annan kuma da Jabir Ibn Alhayyan wanda ya yi fice a fanni Chemistry , turawa na kiransa Geber.  

Mallaman Imamu Ja’afaru Sadiq sun hada da mahaifinsa Imamu Muhammadu Baqir da Imamu Aliyu Ibn Hussaini, wanda ake kira Zainul Abidina ko kuma Imamu Sajjad. Wannan laqabi na Sajjad abokinsa ne wato Azzuhri, wanda ya fara koyar da Imamu Malik Ilimin Hadisi ya sa masa wannan sunan. Babu wata hujja ta ko’ina da ta taba nuna cewa Imamu Sajjad ya kore shugabancin Sayyidina Abubakar (RA) da Umar (RA). Ma’ana hujja ko daga wurin abokansa irinsu Azzuhri ko kuma a kowace littafi irin ta Shi’a zubin goma sha biyu-biyu.

Da wadannan hujjoji zamu iya cewa Ja’afariyya ba itace Shi’a ba. Kuma Imamu Ja’afaru As Sadiq ba dan Shi’a zubin goma sha biyu–biyu bane. Ko da yake mai kokarin kare akidar Shi’a zai iya kawo hujjoji daga littafai kamar su al-Kafi da Man La Yahduruhu al-Faqih da Tahdhib al-Ahkam da al-Istibsar wadanda shike sune littafai na farko wanda wasu mutane da  aka sani koda ba sosai ba suka fara rubutawa a duniyar Shi’a. Ma’ana duk wasu littafai da suka gabaci wadannan ba’a da sanin hakikanin wanda suka rubuta su. Kuma ko su wadannan din an rubuta su ne bayan duk an gama rubuta manyan littafan Sunna na Hadisi da Usul-al Fiqhu.

A cikin wadannan littafai za’a samu cewa akwai wani mutum mai suna Zurara Ibn A’yun wanda ya kasance hadimi ne ga Imamu Muhammadu Baqir da Imamu Ja’afar Assadiq a lokacin rayuwansu wanda ruwayoyinsa sun kai 2094 a fadin babban malamin Shi’a,  Sayyid Abul Qasim al-Khu’i (al-Khu’i, Mu‘jam Rijal al-Hadith Mujalladi. 7 Shafi. 249)

Sannan kuma har’ila yau Al-Kashshi yace hakika bacin shi wannan Zurarah Ibn A’yun din da gaba daya hadisan da aka samu wurin Imamu Muhammadu Baqir sun bace (Ikhtiyar Ma‘rifat ar-Rijal Mujjaladi. 1 Shafi. 345).

To amma kuma wannan malamin ya ruwaito a wurare da dama cewa Imamu Baqir da Imamu Sadiq duk sun tsine wa wannan mutumi. Ga misali wani wuri da aka ce Imamu Sadiq ya tsine masa:

Wallahi ya yi mani karya! Wallahi ya yi mani karya! Allah Ya tsine wa Zurara! Allah Ya tsine wa Zurara! Allah Ya tsine wa Zurara! (Ikhtiyar Ma‘`rifat ar-Rijal, Mujalladi. 1 Shafi. 361)

Banda wannan Zurara din akwai sauran manyan masu ruwaito Hadisai a Shi’a zubin goma sha biyu, kamar su:  Muhammad ibn Muslim da Abu Basir al-Muradi da al-Mufaddal ibn ‘Umar wanda duk a wannan littafi an ruwaito cewa Imamu Ja’far Assadiq ya tsitsine musu.

Koda yake wai ‘yan Shi’a sunce domin saboda taqiyya ce ya tsine musu domin ya kare su daga hushin sarakunan wannan zamanin. To ko an samu ace mutane kaman su Al-Khatab wanda shima Imamu Sadiq ya tsine wa domin yace wai Imamu Sadiq Allah ne, don saboda taqiyya ne ya tsine masa? Shin mabiya akidar Shi’a zubin goma shabiyu na nufin shi Imam ya yadda cewa shi Allah dinne? In ko ba haka ba to lallai tsinuwar dake kan Al-Khatab ta gaskiya ce kamar yadda wadda take kan su Zurara Ibn A’yun da Mufaddal Ibn Umar da Abu Basir al-Muradi da Muhammad Ibn Muslim ita ma gaskiya ce.  

I ma na don daga wadannan mutane ne da ire irensu aka sami mafi yawan abin da yau aka san Shi’a dashi wanda suka kuma nisanta daga abin da aka san Imamu Ja’afaru Assadiq dashi. A cikin wadannan littafai hudu da muka lissafa da farko wanda sune turakun Shi’a zubin goma sha biyu, akan sami hadisai masu karyata cikan kur’ani da wadanda suke kore halifancin Sayyidina Abubakar(RA) da Umar (RA) da kuma wadanda ke koyarda abubuwa da yawa masu rikitarwa a cikin addini wanda har ya zuwa yau ‘yan Shi’a na riko dasu kamar su ma’asumancin Imamu Ja’afar da sauran imamansu. Wannan albarkacin yawancin hadisan wadanda Imaman Shi’a suka tsine wa a cikin littafan. A sabili da haka bamu da wani mafita in muna son mu samu madarar ilimin da Imamu Ja’afar Assadiq ya bar mana sai mu koma ga abin da aka iya tace wa na Imamu Malik da Imamu Hanafi da Sufyanussauri da sauran mutane wadanda su ka yi rayuwa mai tsarki mai inganci a waccan zamanin.

Ina fatan yanzu mai karatu zai gane makaman zancen da zaren zubinsa ya shude wa da yawa masu tattaunawa tsakanin masu kiran kansu ‘yan Shi’a da ‘yan Sunna a Nijeriya. Kuma daga randa ‘yan Sunna suka iya fahimtar abin da ke cikin littafan Shi’a to kuwa kashin ‘yan Shi’a zai bushe a Nijeriya ta fuskar hujja da mukabala irin ta ilimi.

RATAYE

Ga mai son cigaba da wannan tattaunawar zai iya zuwa shafin fallen gizo na www.nigeriavillagesquare.com/board ko www.kanoonline.com/smf  ya kafa take da ginin zance mai ma’ana da inganci. Nan take kuwa zai ganni na ciro domin wasa kwakwalwa ta tare da more wasan odiyo-diyo dake tattare da tsinkaya!

Na barku lafiya

Waziri

Offline Dan-Borno

 • Super Member
 • *****
 • Join Date: Jan 2007
 • Location: Maiduguri
 • Posts: 2389
 • Gender: Male
 • EVERYTHING HAPPENS FOR A REASON
  • View Profile
  • Dan-Borno
Re: Bambanci Tsakanin Mazhabar Ja’afariyya da Akidar Shi’a
« Reply #1 on: May 26, 2009, 11:37:01 AM »
waz?????
"My mama always used to tell me: 'If you can't find somethin' to live for, you best find somethin' to die for" - Tupak

Offline Muhsin

 • Super Member
 • *****
 • Join Date: Jul 2006
 • Location: kano
 • Posts: 3107
 • Gender: Male
 • Ikraa bismi Rabbikal lazii khalaq
  • View Profile
  • The Learner
Re: Bambanci Tsakanin Mazhabar Ja’afariyya da Akidar Shi’a
« Reply #2 on: May 27, 2009, 02:33:07 PM »
Gaskiya Waziri akwai "babban kai". You really are versatile, bros. I wish I could do much more than that. But inshaAllah with time...

Well regarding the thread's topical issue, Shiites are the most enigmatic people I ever had encounter with amongst all the followers of Islamic denominations. I have had just recently finished reading one book entitled The Islamic Revolution in Iran by Prof. Alga. There I really, really learnt a lot concerning these dogmatized sect of people, their Ayatoollah, Mandi, Imams and the likes. Allah ya raba mu da tabewa irin tasu, amin.
Get to know [and remember] Allah in prosperity & He will know  [and remember] you in adversity.

Offline Rais

 • Full Member
 • ***
 • Join Date: Jan 2007
 • Posts: 115
  • View Profile
Re: Bambanci Tsakanin Mazhabar Ja’afariyya da Akidar Shi’a
« Reply #3 on: June 11, 2009, 03:27:27 PM »
waz?????
Gaskiya kam DB wannan dogon sharhi!!!! Amma ya kamata musan  waye WAZIRI
Bayan Mutuwa akwai hisaby

 


Powered by EzPortal