News:

Ramadan Mubarak!

I pray that we get the full blessings of Ramadan and may Allah (SWT) grant us more blessings in the year to come.
Amin Summa Amin.

Ramadan Kareem,

Main Menu

Amfanin icen zogale wanda ake kira Moringa a ilimin kimiyar tsirrai

Started by bamalli, May 18, 2013, 07:30:09 PM

Previous topic - Next topic

0 Members and 1 Guest are viewing this topic.

bamalli

ZOGALEJama'a masu saurare assalamu alaikum. Barkan mu da sake saduwa a shirin Noma Tushen Arziki. A makon da ya gabata mun fara magana kan shuke-shuke da masana ilimin kimiya su ka gano amfaninsu a wannan zamani. Mun yi bayani kan itacen Bita-da-zugu da muhimmancinsa wajen samar da makamashi wanda kuma hakan yana iya taka muhimmiyar rawa wajen rage talauci a kasashe masu tasowa. A yau kuma zamu yi magana kan itacen zogale wanda sananne ne a kusan ko ina a kasashen Afrika musamman ma a kauyuka. Masana ilimin kimiyar tsirrai suna kiran zogale Moringa kuma a kasashe da dama da hakan aka san shi.Hala mai saurare ya yi mamaki idan ya ji cewa icen zogale yana da matukar amfani wajen maganin cututtuka masu yawa. Alal hakika, wasu masu maganin gargajiya sun dade suna amfani da wannan itace wajen warkar da ciwuwwuka da kuma sarrafa shi a matsayin abinci mai gina jiki. A wannan zamani da nazarin ilimin kimiya ya bunkasa, masana sun gudanar da bincike-bincike da dama kan zogale inda suka gano kimarsa ta magani, abinci da kuma abin sarrafawa a masana'antu.Icen zogale dan asalin kasar Indiya, nahiyar Afrika da kuma yankin Gabas ta Tsakiya ne. A halin yanzu ana nomansa a nahiyoyin Afrika da Amurka ta Tsakiya da ta Kudu, da kuma kasashen Sri Lanka, Indiya, Mexico, Malaysiya da Filipin. Icen zogale yana da saurin girma ga kuma jure wa fari. Itacen zogale ya na yi a wurare masu yawan ruwan sama da ma wuraren masu karancisa, da yankuna masu zafi. Yana da saurin girma, yana jure wa fari da kasa maras kyau. Ana shuka shi sosai a nahiyar Afrika, Amurka ta Tsakiya da ta Kudu, da kuma kasashe kamar India, Malaysiya, Philliphines da dai sauransu. Zogale yana cikin itatuwa da aka sansu da yawan anfani a fadin duniya, kuma kusan komai a jikin itacen yana da amfani, wato babu abin yasarwa a cikinsa.Kasar India tafi ko wace kasa a duniya noman zogale, tana noman kadada 38,000 inda take samar da ton miliyan 1.1 zuwa miliyan 1.3 na danyen kwanson zogale a duk shekara. A kasar Taiwan akwai babbar cibiyar kasa da kasa mai gudanar da nazari kan kayan lambu, wanda makasudin ayyukan da take gudanarwa shi ne rage talauci da rashin abinci mai gina jiki a kasashe masu tasowa ta hanyar inganta hanyoyin samar da kayan lambu da kuma sahiyar hanyar anfani da su. Ayyukan wannan cibiya sun hada da bincike kan itacen zogale.Ana cin ganyen zogale da kwansonsa da ake cirewa tun yana da taushi. A kasar India ana hada kwanson da wasu kayan lambu ana yin salad da su. Ana cin danye kwanson ko bayan an dafa shi. A kasashe daban daban ana magani da zogale; bawo, saiwa, fure, ganye, da kuma ‘ya‘yansa duk suna da amfani wajen magani. Sai dai anfanin zogale bai tsaya ga ci da yin magani irin na gargajiya ba. Saboda muhimman sinadaran da ya kunsa ana sayar da shi a kasashen waje. Kwanson zogale ya kunshi sinadarai kamar penicillin masu kashe kwayoyin cuta wadanda ake kira antibiotics. Saboda haka ana bukatarsa sosai a kasashe kamar su Ingila, Japan, Canada, da wasu kasashen Gabas ta Tsakiya. Tun sama da shekara goma da suka gabata wani kamfanin kasar India mai suna DRUMSTICK INDIA yake safarar kayan da aka sarrafa daga zogale. Kamfanin yana hulda da kamfanoni na aikin gona, na kayan abinci, na magani, da kuma na kayan kwalliya. Masana sun baiyana cewa ko da yake sunan zogale bai shahara ba duk da cewa kundayen tarihi sun ambace shi tun shekaru dubu biyu da suka gabata, ana amfani da shi a wurare daban-daban. Alal misali, sama da shekaru arba'in Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi amfani da wannan ice wajen inganta lafiya a kasashe da talauci ya addabesu a duk fadin duniya. Masanan suka ce dalilin boye sunan wannan itace mai albarka shi ne dumbin ribar da ke tattare da harkar sarrafa magunguna da kayayyakin inganta lafiya dangin bitamin (vitamins) da gishirin ma'adinai mai kare lafiyar jiki wato mineral salts a Turance. Saboda haka manyan kamfanonin magani ba kasafai uke son baiyana sinadarin da suke yin magunguna da shi ba.Idan muka leka nahiyar Afrika kuma zamu ga cewa hukumomi da cibiyoyin nazari sun maid a hankali kan wannan ice zogale ko kuma Moringa. Bayanin da zamu bayar a kan haka, mun tsakuro shi daga wata makala da jaridar Daily Trust da ake bugawa a Tarayyar Nigeria ta wallafa. A kokarin gwamnatin kasar Nigeriya a karon farko na bunkasa albarkatun da icen zogale ya ke da su, cibiyar bincike da bunkasa kayan sarrafawa a masana'antu ko sinadarai (wato Raw Materials Research and Development Council RMRDC) wanda take aiki karkashin Ma'aikar Kimiya da Fasaha ta Tarayya, ta gudanar da taron karawa juna ilmi da baje koli, da zimmar farkar da jama'a kan alfanun da zogale yake da shi. Taron mai taken ‘Moringa: Itaciya Da Zata Taimaka Wajen Cimma Manufofin Bunkasa Kasa' ya sami halartar masana da dama, wadanda suka yi nazari kan anfanin zagale da hanyoyin kwadaitar da jama'a su fara nomansa saboda kasuwanci.Daya daga cikin maharta taron Dr. Nwora A. Ozumba mai nazari ne a Bangaren Nazari Kan Zogale na Sashen Nazari kan Kwayoyin Cuta na Jami'ar Nnamdi Azikiwe da ke garin Akwa. Ga abinda yake cewa:"Hakika, a kidayar baya-bayan nan da na yi na samu cewa zogale yana maganin cututtuka tamanin da daya (81), kai yana ma iya warkar da kusan komai. Mu masana kimiya na zamani mun sha sukar masu maganin gargajiya kan cewa da suke yi magani daya yana iya warkar da cututtuka ashirin (20), amma yanzu mun gane cewa ganyen zogale yana da iya warkar da ciwuwwuka masu yawa, wadda an tabbatar da hakan a ilmance. Ganyen zogale na maganin ciwon suga, zazzabin cizon sauro, rashin isasshen abinci, da dai sauransu. Yanzu kam mun gane madogarar ilimi ta wannan magana da masu maganin gargajiya suke fadi..."Dr. Ozumba wanda ya share shekaru goma sha daya yana bincike kan icen zogale ya sheda wa jaridar Daily Trust cewa tun da ya gane wannan itace bai sake amfani da maganin karin gishirin ma'adinai wanda jiki ke bukata (mineral salts) irin wadanda kamfanonin magunguna suke sarrafawa ba, saboda, kamar yadda ya ce, aikinsu bai kama kafar na zogale ba. Dr. Ozumba ya kara da cewa: "A matsayinmu na masana masu bincike, nauyin da ya hau kan mu shi ne mu bunkasa wannan itace domin sarrafawa a masa'antu kuma mu yi kokarin kara masa kima. Saboda haka ne cibiyar RMRDC ta hada kai da kamfanin Avuco domin fito da abubuwan da wannan itace ke kunshe da su."Da ya kwatanta zogale da man fetur, Dr. Ozumba sai ya ce zogale baya karewa kuma baya gurbata muhalli, alhali man fetur zai kare kuma yana haddasa gurbacewar muhalli. Wani masani daga Jami'ar Ahmadu Bello da take birnin Zaria wanda ya sami halartar taron na cibiyar RMRDC Dr. I.M.Bugaje ya ce amfanin zogale bai tsaya ga fannin abinci ba domino kuwa yana tace ruwa. Idan aka fitar da mai da sauran sinadaran da ake bukata, tunkuzar ‘ya‘yan zogale tana iya tace ruwan sha tare da kawar da kwayoyin halitta (bacteria) masu jawo cututtuka. Dr. Bugaje ya ce muna iya tace ruwa da ‘ya‘yan zogale a maimakon alum wanda Nigeriya ta ke kashe biliyoyin dala domin sayo shi daga kasashen waje. Bugu da kari, zogale ba shi da wata illa saboda yana nan bisa yanayinsa na dabi'a, alhali an sani cewa alum yana jawo cututtuka da dama, cikinsu kuwa har da gurbacewar jinni. Domin tabbatar wa duniya da ingancin wannan fasahar tace ruwa, Dr. Bugaje ya sheda wa taron cewa za'a gina tashar tace ruwa ta gwaji a wani kauye kusa da garin Zaria, kuma hakan zai bai wa kamfanoni masu zaman kansu damar shigowa su zuba jari. Wannan masani ya kara da cewa tuni an fara sarrafa zogale a kasashen Tanzania da Malawi kuma suna fitar da shi zuwa kasashen Turai. Babban darektan kamfanin Avuco Nigeria Limited Yohanna Dami Kadashi ya baiyana cewa shekaru biyar ke nan kamfaninsu yana gudanar da bincike kan itacen zogale, kuma ya ce babban manufarsu ita ce gano amfani da kuma albarkatun da suke cikinsa. Darektan ya ce zogale yana maganin hawan jini, zazzabin cizon sauro da ciwon suga, da kuma saukaka zazzabin da masu ciwon kanjamau sukan yi fama da shi. Su ma ‘ya‘yan zogale suna da mai mai daraja wanda ake sayarwa $10 ko wace lita daya a kasuwannin duniya. Babban darektan cibiyar RMRDC wanda ta gudanar da toron Farfesa Peter A.Onwualu ya fadi cewa itacen zogale zai taimaka wajen samar da man abinci tare da sauran tsirrai masu samar da mai, a lokaci guda kuma ba zai zama kishiya ga noman cimaka ba. Farfesa Onwualu ya kara da cewa: "Ba shakka noma da sarrafa itacen zogale zai kawo mafita ga matsalolin da suka danganci samar da aikin yi da kudin shiga, da kuma inganta lafiya ta hanyar samar da ruwan sha lafiyayye kuma wadatacce. Hakazalika, nomawa, sarrafawa da kuma amfani da icen zogali zai taimaka gaya wajen tabbatar da wadatar abinci a kasa."Wani masani Farfesa Charles Wambede wanda mamba ne na cibiyar ilimin kimiya ta Nigeriya (Nigerian Academy of Science) da kuma cibiyar kasa-da-kasa ta binciken magungun da ake samu daga halittu masu rai (International Biomedical Research in Africa) yana cewa: "Ina fatar masanan Nigeriya su yi nazari kan icen zogale tare da wallafa nazarin nasu a majallolin kimiya. A kasar Ghana an yi nisa a wannan aikin..."Ga wasu fa'idoji da suke tattare da itacen zogale:1-Ganyensa yana kara karfin garkuwar jiki, yana kara kuzari, yana taimaka wa zagayawar jini da bugawarsa, yana taimaka wa aikin koda da hanta, yana maganin gyambon ciki, da dai sauransu.2-Ganyen zogale ya kunshi: i-ninki 7 na vitamin C da ke cikin lemo,ii-ninki 4 na sinadarin calcium da ke cikin madara,iii-ninki 4 na vitamin A da ke cikin karas,iv-ninki 2 na protein (wato abin da yake gina jiki) da madara,v-ninki 3 na sinadarin potassium da ke cikin ayaba.3-‘Ya‘yan zogale suna da mai wanda yawansa ya kai kashi 38-40%. Wannan man yana da sifofi irin na man zaitun wanda ya shara wajen daraja.4-Zogale zai taimaka wajen magance karancin abinci mai gina jiki.5-Noman zogale zai samar da aikin yi.6-Noman zogale da sarrafa shi zasu taimaka gaya wajen bunkasa tattalin arziki da rage talauci a kasashe masu tasowa.To jama'a masu saurare a nan zasu dakata sai mako mai zuwa in Allah ya yarda zaku ji ci gaba da wannan shiri na Noma Tushen Arziki. Wassalamu alaikum wa rahmatullahi Taala wa barakatu. Â