Author Topic: Kwalara a Kano  (Read 1201 times)

0 Members and 1 Guest are viewing this topic.

Offline Yusuf_Adamu

  • Member
  • *
  • Join Date: Nov 2001
  • Location: Kano, Nigeria
  • Posts: 3
    • View Profile
Kwalara a Kano
« on: December 04, 2001, 07:37:17 PM »
Jama'a Assalamu Alaykum,

Ku san kowa ya ji yadda Kwalara ke ta kashe da nakasa mutane a Kano da Jigawa musamman. Abin ya kusan zama cewa duk shekara ko bayan shekaru uku sai mu yi kwalara ko sankarau.

Abin damuwa ne matuka ganin yadda al'amura da suka shafi kiwon lafiya suke tafiya a Kano, kuma wasu abubuwan, abubuwan da za a iya maganinsu matukar hukumomi na yin aikinsu tsakani da Allah. Yanzu a ce har yanzu ba mu da isasshe kum tsaftataccen ruwan sha a Kano. Ku tuna fa 'yan shekaru baya, ruwan fanfo kamr ma zai fasa famfo a Kano yake, saboda karfi, kuma ga tsafta, amma muna kara tsufa muna lalacewa? Haka za mu ci gaba da tafiya.

Ina ganin lokaci ya yi da za mu sauya rawa. Me zai hana duk mutanen Kano dake wajen Nijeriya su hada kai su zama tarnaki ga shugabanni da ba su da kishin Kano? Dukanku kuna ganin yadda kasashen da kuke suke ci-gaba. In mun dage ba sai mun jira Nijeriya ba, mu ciyar da Kano gaba ta duk yadda za mu yi.

Mu daure mu taimakawa wadanda ba su da karfi. Kuma Dr. Alasan sai ka maida himma ga abinda ka fara, kada ka yi kasa a gwiwa. Allah Ya ba mu sa'a
amin.

Danuwanku,
Yusuf Adamu
usuf Adamu

 


Powered by EzPortal