Wannan thread din kam lallai azimun ne ya kamata muyi santi.Hmm su Baby gurl manya. To bari na baku labarin mallam Lamiri mai gani har hanji da abokinsa Usman. Mallam ya gaiyaci usman gida suyi sallar magriba a masallacin kofar gidan sa dake kofar na'isa. Bayan sallar magariba Lamiri yasa aka kawo musu abinci, towon Dawa da miyar Kuka, tasha man Shanu. Koda Usman ya yanka lomar farko sai ya kada baki yace: Shin Gafarta mallam, ni ina ga kunce ba wani abu da Allah baiyi bayaninsa a cikin littafinsa maigirma ba, wato kur'ani.Mallam ya dube shi yace TABBAS, gaskiya ne. Usman da man shanu ya buge shi sai yace shin alagafarta mallam ko Allah yayi bayanin
MIYAR KUKA acikin Kur'ani kuwa. Lamiri ya zaburo ya sunkuyar da kai yace: KWARAI da Gaske. Ga ayar nan ta kur'ani da Allah yake cewa:
WATARA KUKA KA'IMA.... Usman ya gyara zama yace lallai kam wannan gaskiya ne. LOL!!!