RIKICIN NIGER DELTA ZAI IYA KAWO MULKIN SOJA

Started by Dan-Borno, August 23, 2007, 11:20:34 AM

Previous topic - Next topic

0 Members and 1 Guest are viewing this topic.

Dan-Borno

Yan'uwa, wannan rikice rikice da ke faruwa a makwabtanmu
Niger Delta idan har gwamnatin tarayya bata fiddo da wata
mafita ba, to abin ba a cewa komai, lalle ne nan ba da dade
waba sojoji zasu karbi mulki saboda "insecurity".

Wannan kuma bari na fada muku, ba wani abu bane illa
makirce makirce na America, domin mun samu reliable
hanyar sadarwa inda Amurka ke cewa su dai interest din
su a Nigeria shine Mai a Niger Delta, in kuma baza a samu
zaman lafiya a gun ba, to lalle ne su ingizo sojoji saboda
a samu zaman lafiya domin suma su samu diban mai yadda
suke so.

Rashin zaman lafiya abune muhimmi a kasancewar kasa,
muddin babu zaman lafiya, hakika gwamnati bazata samu
zama ba.  A kasar mu najeria, tatar mai itace take kawo
mana kashi 75% na kudaden shiga, kuma shine a ke raba
wa sauran jihohin suke samun gudanar da ayyuka da yau
da kullum.

Abin takaici de, shine, har yanzu arewacin najeriya ba dau
hanyar samun karfafa ayyukan noma ba, saboda haka,
muddin a kasamu matsala da gwamnatin tarayya, jihohin
da zasu fara tagayyara sune na nan arewa, saboda muddin
ba abamu kason mu ba, lallai, ko dan ci rani wanda ke sayar
da tumatur a bakin kasuwa sai ya san cewa gwamnati bata
biya albashi ba.

Abisa wannan la'akari nake kira ga yan'uwa abokan zaman
kanoonline, da su tofa albarkacin bakinsu game da wannan
rikici da ake ta samu a Niger Delta. 

Wacce hanya shugaban kasa zai bi domin ya kawo karshen
wannan rigima

Wacce hanyoyi Shugaban kasa zai bi domin ya bunkasa noman
damina da noman rani a arewacin najeria

Kuma wace hanya shugaban kasa zai bi domin ya karfafa binciken
mai a arewacin nigeria.

Nine Dan-Borno, kuma duk wanda zai tofa albarkacin bakinsa to
yayi rubutu da hausa.
"My mama always used to tell me: 'If you can't find somethin' to live for, you best find somethin' to die for" - Tupak

Muhsin

To dan-Barno, a ganina wannan 'thread' din da ka rubuta shi a General Board da yafi.

Allah ya kiyaye wancen irin mulkin na sojoji. Abunda zan iya cewa kenan.

Sai anjima
Get to know [and remember] Allah in prosperity & He will know  [and remember] you in adversity.

bamalli

To har in Mulkin Sojan shi ne mafi kyau a garemu za su tsare mana mutuncinmu da rayuwarmu da addininmu to fa muna maraba da shi

waduz

Wannan magana naka "jan borgo" ai babba ce! Ai kai ma ka san cewa da soja ne ke mulki da rikicin nija delta bai taso ba. Da an yi amfani da karfin soja an murkushesu tuni. Amma duk da haka ai bamu yin fatan cewa soja su dawo mulki saboda irin mulkinsu na kama karya ne. Wani lokaci ma har sukan karya inda ba gaba! Sai anjima Jan borgo, ah wai! ashe danborno ne!

Dan-Borno

Ikon Allah duniya juyiyi, ina aminina Alkanawi
gashi su Waduz dan karamin alhaki har suna
canza min suna wai jan borgo.  Don Allah wai
what is jan borgo ne tukuna before i sprang
into action  ;D  ;D  ;D  ;D

Malam Waduz, in ka lura da abin da na rubuta
na nemi shawarwarin jama'a ne game da
ta wani hanyoyi ne za a bi saboda ganin cewa
wannan fadace fadace na niger delta bai
fantsama zuwa ko ina ba.
"My mama always used to tell me: 'If you can't find somethin' to live for, you best find somethin' to die for" - Tupak

HUSNAA

Ghafurallahi lana wa lakum

Bajoga

Assalamau Alaikum!!!
Gaskiya wannan topic din yazu dai-dai lokacin da ya kamata ayi magana akai, badon komai ba, sai don ganin irin yadda kasarnan dake ciki da kuma yadda take kara tabarbarewa.

To! ni anan zan iya cewa zuwan soja wannan kasa, mu a tunaninmu ba alkairi bane, amma yakan iya kasancewa shine mafi alkairi a agaremu. Saboda haka mu muna rokon Allah idan zuwansu shine mafi alkairi to muna maraba dasu.

Sa'annan kuma game da shawari akan yadda gwamnati zata gyara/shawo kan matsalar Niger Delta, wannan abinda dukkan musulmi yasani ne, shawari kawai shine mu koma ga Allah (SWT) da Manzo (SAW) mugani Allah zai kawo mana saukin dukkan al'amuranmu.

Gaskiya da wuya muyi abinda muke so, kuma mu ga abinda mukeso, sai dai akasin hakan.

Shuwagabanni sun baci da cin haram, hakanan talakawa, kowa bai son gaskiya a rayuwarsa kuma mun san gaskiyar.

Wannan shine abinda zan iya fadi akan lamarin.
Allah ya taimakemu.
HASBUNALLAHI............

amira

Quote from: Bajoga on September 22, 2007, 08:14:06 AM
Gaskiya da wuya muyi abinda muke so, kuma mu ga abinda mukeso, sai dai akasin hakan.

Shuwagabanni sun baci da cin haram, hakanan talakawa, kowa bai son gaskiya a rayuwarsa kuma mun san gaskiyar.

Wannan shine abinda zan iya fadi akan lamarin.
Allah ya taimakemu.

Wa'alaikumus Salaam

Gaskiyar ka wannan maganar haka take, haramunan dai anci shi kuma ba'a gama cin sa ba.
Maganar gaskiya kuma dama wanda ya samu ta hanyar cutar da dan uwansa ko bai so ayi masa
wata maganar Allah Da Annabi.
Ni dai tsorona, kada yan amurka su zo sukuma su kara dagargaza mana kasa dama wacce Allah cika.
matsalolin ita delta din suna dayawa ga masu noma an dauke masu fillin nomansu,ga satar mai wanda ke jawo fitina a tsakanin mutane masu saidawa. Kai abin dayawa yake duk mai son karin bayani yaje dawodu a kwai wani shafi na wani mutumi dan jarida da ya mutu shekaru baya yana yakin ita wannan matsalar garin.
Amma dai Allah Dai ya taimaka kuma ya shirya wannan abin takaicin Ameen.
*Each day is definately defining me and finding me*

HUSNAA

Ghafurallahi lana wa lakum