News:

Ramadan Mubarak!

I pray that we get the full blessings of Ramadan and may Allah (SWT) grant us more blessings in the year to come.
Amin Summa Amin.

Ramadan Kareem,

Main Menu

Tatsuniya Online (GIZO DA GOGI)

Started by IBB, March 27, 2003, 10:28:08 AM

Previous topic - Next topic

0 Members and 22 Guests are viewing this topic.

gogannaka

kai amma fa mutane da rashin kirki suke
pls maama dont tell us the guy went away with it
Surely after suffering comes enjoyment

MaAMaa_LagOS

Mutumin nan ya kai tsuntsun gida ya sa shi a keji ya fita ya sayo kaza ;D a hada da tsuntsun ka ga an sami biyu kenan.
    Matar mutumin nan ta ga tsuntsun a keji yana ta kyarma. Sai ta tambaye shi mai ya hada shi da mallam har ya kamo shi ya sa a keji? Sai tsuntsun ya kwashe labarin yadda sukayi da mutumin duk ya gaya mata. Ita kuwa tausayin shi ya kamata ta bude keji ta ce "Fita ka tafi Allah ya saka ma". Fitowar tsuntsu ke da wuya sai ya yo kan baiwar Allahnan ya kwakwale mata ido daya ya tafi abinshi. :'(
   kurunkus kan dan bera.
aSY DoES iT

baby_gal_84

tau ina ruwan kuwa da nasa hali kenan.... a takaice dai matar mutumen ce kadar mai kirki .... amma ita ma wa ya sani maybe tana da nata mugun hali....
ond of love fills the life with sweet promises.

IBB

maama lagos this story has to have part three. the snake reloaded  ;D ;D
IHS

Guduma

Gata nan gata nan ku.

Anyi wani mutum a wani kauye wanda ke da sana'ar fatauci da jakunansa biyu. A kullum sati ya kan tafi da jakunansa cin kasuwoyi inda yake yin kwana biyu, ko uku watarana. To, shi wannan mutum Allah ya bashi kyakykyawar mace, wacce  kauyensu kaf, babu mace mai kyanta. Ita wannan mata kuwa fasikace ta kin kari, domin a kullum mijinta yayi tafiya, to fasikan garin maza sai suyi layi a kofar gidansa, wani ya shiga ya fito, wani kuma haka
Rannan wani yana cikin dakin matarsa ya dade sosai bai fito ba, har wanda ke jiransa ya gaji, abin ya dami shi wanda ke jiran har ya rasa abin da zai yi. Can yana zaune, ya kuntume don fushi wanda ke cikin dakin, sai dabara ta fado masa. Ya nemo tsumagiya mai kyau ya zo da ita kofar dakin ya dinga dukan kasa yana wani karaji da gunji kamar dai na jakuna dake tafe, wato domin matan nan da wanda suke tare su ji, su zaci cewa kila maigidanta ne ya dawo.
Mutuminnan dai ya ci gaba da kartar kasa har matan ta ji, sai tace wa kwartonnan, "wai! ai ga mijina ya dawo! yaya zanyi da kai, ni 'ya su?". Sai kwarton yace "ki bude mini kofa da sauri, sai na fita a guje, ta yadda ba zai ganni ba balle ya ganeni". Ta ce "to". A kofar daki kuwa wancan kwarto yana jinsu, sai ya make da tsumagiyarsa a hannu, yana jira na cikin dakin ya fito. Can sai ya ga an bude kofa da gaggawa, sai ya ga wanda ke ciki ya fito a guje, ya nufi kofar gida. Sai shima yayi wuf, ya bishi ya dinga tsala masa bulala har ya kaishi bayan gari. Wanda ake duka yana jin zafin duka, amma ba daman yayi ihu don gudun tonan asirinsa, sai kawai dai yana ta gudu, wannan ko sai shirga masa bulala yakeyi har ya kaishi nesa tukun ya dawo gun matannan.
To kasan kauye, baa rasa matattara inda mutanen gari ke haduwa ana hirar yau da kullum. To suma kwartayennan biyu washe gari sai suka fito gindin wata itaciya tareda sauran jamaa suka zauna. Sai kwarton da aka yiwa bulala sosai jiya da dare yace, " ashe malam mai jakai ya dawo?" Shi kuwa wanda ya tsuga masa duka ya ce, "aa, ai malam maijakai bai dawo ba, kila sai jibi". Da wanda aka dokannan yaji haka, sai yayi shiru yana mamaki cewa an cuceshi jiya da aka fasa masa jiki da bulala, yana tsammani mijin matar ne. Sai ya ce  " ;Din kuwa mai jaki bai dawo ba, to lalle kauyennan namu akwai azzalumai!!".
Kurungus kan bera, wanda yaji tsoro.................

kilishi

A story of a jealous man and what befell him
This is a story about a jealous man.

A story, a Story. Let it go. Let it come.

There was a certain man who used to live in a town, but afterwards he rose up and went to the bush, lest people might go after his wives, until one day the chief of the town heard about him and he said, 'He who goes and seduces his wives, if he comes (to me) I will give him a horse, and a cloak, and one hundred thousand cowries.'

Then a certain man said he would be the one to go and lie with his wife before his eyes. Then he went off and sought some baobab seeds. He opened them, (and) cleaned out the inside well; he sought for some very small pieces of money and poured them inside. He went, reached (the place where the man was) (and) gave him a present of them.

When he broke (one) open he saw the small money inside. He broke another also, (and) in the same way broke open another. And he said, I My friend, will you not show me where this baobab tree is?' He replied, The place where this baobab tree is is far away.' (And) he said, Take me (to it).' And he said, 'It cannot be climbed except by a ladder, (and) no one knows where it is save me.'

And he continued to entreat him; and at last the seducer said, I Let us go, I will take you there, but if it was not for you, I would not show any one the place.' So they set out along with his wife. When they came to the baobab tree then the seducer lifted the ladder and placed it (against the tree), (and) told the woman's husband to climb up. So up he climbed.

When he had finished climbing, then he lifted away the ladder, (and) carried it somewhere else (and) set it down, (and) came back. He seized the wife and threw her down. He did what he intended, the woman's husband looking on (and) not able to descend; but he said, 'I shall spit on you, I shall spit on you,' until they had finished what they were doing.

The seducer went his way. He came, (and) told the chief what they had done. The chief gave him his reward, and added to his gifts. He said, 'That's the medicine he required.' As for the (jealous) man, his wife with difficulty lifted the ladder, (and) brought it to him, (and) he descended. On his return home he collected all his goods, (and) returned (to live) in the town. He said, 'My jealousy dragged me into this; if I remain here, people will destroy me.'

That is the story.

Off with the rat's head.
ilishi

IBB

a wani gari anyi wata mata wacca duk lokacin da mijin ta yai tafiya sai kwartaye su fara hallara 'a gidan.
wata rana mijin yayi tafia sai kwarto yazo, kwarton nan na cikin daki sai mai gida ya akayi ya akayi bai samu tafiya ba sai ya dawo, mai gida yazo yana buga kofa yana sallama sai matar tace wa kwarton muryar mai gidan ta take ji, suka fara tunanin yadda za suyi sai matar ta tuna tana da katuwar-tukunya (big pot) a karkashin (under) gado shiken kwarto sai ya shiga ciki ya buya. mata ta fito ta bude wa mai-gida gida ya shigo suna daki 'a zaune da kuma kwarto 'a tukunya, sai ga wani kwarton yazo kuma yana kwankwasa (knocking) kofa sai matar tai sauri tace wa mijin ai masu karbar tukunya ne suka zo. shike nan sai mai gida ya dauki tukunya ya bawa mai knockin da mai-knockin yai gaba sai yace kai allah yai mani gyadar dogo sai wanda yake cikin tukunya yace allah ya maka gyadar dogo ko allah yai min
IHS

kilishi

I B B ashe ka iya tatsuniya haka? lallai matar shu'umar gaske ce,wato dai ita ce da luck!!! Allah kyauta. ;D
ilishi

Anonymous

badan karya karya ce in fada rijiyar zuma a ciro ni da gugar nakiya da alkaki in tuntube da tuwon shinkafa in dauje baki da tsokar nama :o

gogannaka

Quotebadan karya karya ce in fada rijiyar zuma a ciro ni da gugar nakiya da alkaki in tuntube da tuwon shinkafa in dauje baki da tsokar nama :o


Wayyo dadi!!!!!!!!!
Surely after suffering comes enjoyment

zezezee

hmmmmmmmmmmmmmmm...su ihsan manya!
hajjaju akwai ki fa ;D
 just realised that nothing is what it seems.

IBB

Gatan gatan ku.

A wani gari mai suna Shangai a cikin kasas Sin anyi wani jarimin Sarki mai dukiya. Allah bai bashi haihuwa ba. bayyan anyi ta rokon allah da kuma tsubbace-tsubbace sai yar autar matar sa Allah ya bata ciki, da sarki yaji labarin matarshi tayi ciki sai sonta ya shiga zuciyar sa sosai. sarki yasa akai ta kula da matar nan da kyau har ta sauka, ta haifi da na miji, sarki ya sami magaji.
dan sarki ya kawo karfi aka koya masa sukuwa da doki da duk abun daya kamata ya iya.

Mean While

a wani nan kauye mai suna Bankok akwai wata yarinya mai kyan-hali, iyayenta sun mutu tun tana yar-karama, uncle dinta ya dauke ta take mashi aiki a gidan sa. sai yan-gida they took advantage of that suke gana wa yarinyar nan azaba ta tashin hankali, itace debo ruwa, girki, wanki, shara, abu kadan duka.

Sarkin Sin dansa ya isa aure, sai yasa akayi shela; duk 'yan-matan garin dana kauye suyi kwalliya su zo, Yarima zai zabi matar sa, amma da sharadi. sharadin kuwa shine sai ta fadi sunan sa (shi dan sarkin).

mata aka shiga kwalliya. ranar aure tazo. 'Yan-mata kowa ta cancara kwalliya sun dau hanya zuwa fada. amma yar baiwar Allah babu kayan kalliya.

'Yan-matan nan na tafiya sai ga wata tsohuwa tazo, tace 'dan allah 'yan-mata wacece zata iya wanke min baya na hannu na ya tsufa bazan iya ba'. 'yan mata suka kalle ta 'a wulakance sukace munyi kwalliya zamu ga yarima san nan za mu tsaya miyi miki wanka Allah ya sauwake.

kowace yarinya idan tazo sai tsohuwar nan ta tare ta ko za tayi mata wanka amma su ki. sai ga wanna yarinyar da iyayenta suka mutu ta zo tsohuwa ta roke ta, ta wanke mata baya yarinya tace to baba. tana cikin wanke mata baya sai bayan ya rufta (broke) tsohuwa ashe ba mutum baceba, sai tace mata ya haka kowa zai tafi fada yayi kwalliya banda ke yarinya tace bani da kaya. sai tsohuwa tace 'ki dauki wannan dan-basket din dake cikin bayana ki bude'. da yarinya ta bude sai ga kaya masu dan-karen-kyau suna kamshi taba bawa yarinya, yarinya ta karba tace na gode ta kama hanya sai tsohuwa ta tsayar da ita.


srry got 2 rush do sumtin will be updated as soon as pos
IHS

Ihsan

Quotehmmmmmmmmmmmmmmm...su ihsan manya!
hajjaju akwai ki fa ;D
??? zezezee, me no get u woo

anywayzzz...now that I am back, insha Allah more tatsuniyas to come.
greetings from Ihsaneey

kilishi

All right.  A tale for you.  There was a man, a famous malam and an emir s son.  He had his daughter; the other was an only son.  He said, he said ... he went to see the old woman to whom the em... the malam had entrusted his child.  He said to her, Hey, can you do that ... call the malam s daughter so we can talk to her?
She replied, Yes, I ll just go tell her. So they went off. When she got there she said, The emir s son says he d like to talk to you.
She answered, When you go back, tell him I ll set a mortar on the wall and we can talk.
That was that.  She went back and told him.
That was that.  They went to the wall at night and chatted.  Everyday that s what they did.  Everyday that s what they did.  They d talk by the wall.
That s how it was until one day he said ... he got up and said that he wanted to marry her.
That was that.  But the malam replied, Me, I refuse to give her up.   He continued, I m going to marry my daughter to a koranic student.
He said, No.
She insisted, Father, let me marry him.  I want to marry him.
 He said, All right.   That s what they did, and it was finished.  That s how it was.  The marriage was performed.
When it was finished ... when it was finished, time passed and then one day--but he already had one wife.  He took some stones and gave them to the malam s daughter.  And he took some rice and gave it to the other wife.  He told them to boil water.
She went to her parents home and complained, Oh Father, he gave me stones and told me to boil, no ... to boil stones.  And he gave her rice and told her to cook it. He replied, Go and find a single grain of rice.  Find a single grain of rice, put it in those stones, and heat some oil.
That was that.  She went and got her grain of rice and put in some oil.  That was that.  Hers all became rice and the other woman s became stones.
He came and said, Bring me what I gave you to cook. First he went to the head wife and saw that hers had all become stones. That was that.  Then when he went over to the malam s child he found rice.  That was that.
That was that.  Time passed, and he felt something wasn t quite right.  So he took his horse ... he told her ... he took a mare and said to her, You see this mare?  Before I come back she s to have a colt that looks like my horse.  As for me, before I return, you, you re to have a son that looks like me.
That was that.  She went crying to her father and said, Father, as he was getting ready to go off to another country he told me that before he gets back the mare is to have a son that looks like his horse, and I m to have a son that looks like him.  But I m not pregnant and his mare isn t pregnant
He replied, Go off and wait. He performed some work for her and said, Wherever he stays, wherever he sleeps, you ll sleep there.  Wherever he spends the afternoon, that s where you ll spend the afternoon.
She mounted her mare and off they went.  Where he spent the afternoon, she spent the afternoon; where he slept, she slept.  When he stopped, where he stopped, that was that, she too stopped there.  Drummers were sent out to announce that there was a newly arrived divorc?e for anyone who wanted her.  When he heard he got up and went, and when he arrived he demanded, Young lady, do you want me?
She replied, It s been a long time I ve wanted you. He said, But if you want me, she said, you ll have to mate your horse with my mare.
That was that.  He answered, It s as good as done. When morning dawned, his mare and her horse were mated.
As for her, he came to her rooms.  She said, You see, I don t want anything from you except your ring, your perfume jar, and your blanket.
He responded, It s done.   That was that.  He gave them to her.  Once he d given them to her, she got back on the road and headed home.  On and on and on she went.  By the time he returned she d come back pregnant with his child and the mare was pregnant with his horse s child.  That s how she returned.
By the time he got back she d had the child.  As he made his greetings someone said, Here s your husband come back.   That was that.  When she was told, Here s your husband come back, then she picked up the child and held him in her arms in front of him.  Then she brought out the ring and put it on; she brought out the blanket and placed it over his shoulders; she brought out the perfume jar and set it in front of him.  When he got down from his trip he didn t go anywhere until he d gone to see the mare.  When he arrived, he saw it was his horse s son.  And then as he drew close to the house he saw her sitting with the child.  He looked exactly like him and he had on all his things.  He asked her, Hey, where did you get these things?
She replied, Where did I get these things? She went on, You see, you see them here, period.
That was that.  He said to her, Yes indeed, your father has become a very famous man.  Let s live together as a married couple.
She replied, Me, I m not staying married to you. She said, If you want the two of us to stay married, I swear, you ll have to get rid of your other wife.  Me, we can live here together. That was that.  He got rid of the other wife, and stayed with her.
K ungurus!  Off with the mouse s head
ilishi

Ihsan

oh...haven't seen this tatsuniya before. Quite..err...interesting :)

Well it has almost been year since anything was posted here! I actually can't think of of any tatsuniya right now...even if i do maybe i have already posted it. But let me try...here we go...

Gata nan gata nan ku...

Da akwai wani mutum dake da mata biyu dukkansu kuma suna da 'ya ya. To sai watarana uwargidan ta mutu a bar danta mai suna Janiya. Amaryar dama bata san uwargudan da danta! Ay kuwa shikenan ta samu abunyi; tayi ta gallazawa yaron, ba abinci sai aiki. Yaranta kuwa kuda ma baya taba su. To shi wannan yaron ya gaji wata saniya daga wajen maman shi. Ita dai saniyar nan tana magana dan haka duk wani tuggu da amarya ke shiryawa Janiya, saniya tana gaya mashi. Amarya taga tayi duk wani abu gashi har Janiya bai mutu ba. Sai rannan Janiya ya je wajen saniyar shi sai saniyar ke ce mashi "amarya zata sa a yanka ni, ka ce kana son kayan ciki". Haka aka yi kuwa, amarya ta sa aka yanka saniya, Janiya ya karbi kayan ciki.

To yau ma dai uwargida ta hada wani tuggun...da Janiya yaje wajen kayan cikin saniya sai ta ke ce mashi " Janiya Jannati, kishirya uwa ba uwa ba ce, Janiya Jannati...yau zata saka wuta a daki...kada ka kwata a gaban gado."

Dare yayi aka zo kwanciya...to dama kan gadon da dan amarya da Janiya ne. Janiya ya tafi can bayan gado ya kwanta. Ay kuwa bacci yayi bacci dan amarya ya murgino sai cikin wuta. Ya fara ihu yana cewa "iya nine, iya ni ne!" Ita kuwa tana can kwance da jaririnta tana cewa dama kai ne mana dan ubanka!

Washegari amarya ta tashi wai taga Janiya ya mutu...amma ina sai gawar danta ga Janiya kuma da ranshi! Karshe dai amarya haukacewa tayi!

Kurunkus kan tan bera...da badan gizo ba da nayi karaya...dama dai ....hehe
greetings from Ihsaneey