KATA NAN KATAN KU
GIZO DA BASAMUDE
AKWAI WANI BASAMUDE A BIRNIN KUDUS. BASHI DA KOWA
SAI KATON SAN SA (HIS BULL) WANDA YAKE SAWA A GASAR
TABA KANSHI. SABODA YANA DA SAWO BABU WANDA ZAI IYA
TABA KANSA (HEAD) IDAN MUTUN BAI TABA BA SAI YA CINYE
SHI. HAKA YAKE YI DUK SHEKARA WANNAN SHEKARAR SAI GA
SHI A GARIN SU GIZO YA NEMI WANDA ZAI TABA KANSHI YA
BASHI SA (BULL) DUK GARIN KOWA YAKI. GIZO NA JIN LABARI
SAI YAZO YACE AI SHI ZAIYI SHIKE NAN BASAMUDE YACE TO
AKA SA RANAR GASA, DA RANAR TAZO GIZO SAI YAKI
FITOWA DAGA DAKIN SHI, BASAMUDE YAZO BAKIN KOFA
YACE GIZO YA FITO GIZO YACE YANA ZUWA BASAMUDE YAI
TA JIRA DA YA GAJI YA KARA CEWA GIZO YA FITO SAI GIZO
YA CE YANA AIKI NE YA KUSA GAMAWA BASAMUDE YACE
WANI IRIN AIKI NE WANNAN SAI GIZO YACE AI YANA DINKE
BANGO BASAMUDE YACE DINKE BANGO? GIZO YACE E SAI
GIZO YACE MASA YA LEKO DAKIN YA GANI YADDA AKE DINKE
BANGO BASAMUDE CIKIN MAMAKI YA LEKA YANA ZURA
KANSHI CIKIN DAKI SAI GIZO YA TABA. GIZO YA FARA TSALLE
NA CABA (TABA) NA CABA JAMA'A SUKA SHEDA AI GIZO YA
TABA SHIKENAN GIZO YACI KATON SA
KURUNKUS KAN DAN BERE