Assalamu alaikum yan-uwa da abokan Arziki na kano online,da wani dan karamin tunanine nayi naga kamar ya kamata mu dan wasa kwakwalwa,mu dan gwada kacici-kacici (hausa/english riddles)
Ga wasu nan dai kan na samo wasu,wanda ya sanni ya ba da ansa. in kana/kina da wani ku rubuto
- shanu na dubu amma madaurinsu daya.
-baba na daka, gemu na waje
-takanda ba kashi ba
-baba ya zaga iya ta zaga basu hadu ba
-yadda dillin yakanyi dillin haka ma dillin ya kanyi dillin
- tsimagiyar kan hanya make yaro make babba
Wanda ya san ansa ya bayar in kuma kun bada gari na fada maku ansar